< Lévitique 9 >
1 Le huitième jour, Moïse appela Aaron et ses fils, et les anciens d'Israël;
A rana ta takwas, Musa ya kira Haruna da’ya’yansa maza da kuma dattawan Isra’ila.
2 Et il dit à Aaron: Prends un jeune veau pour le sacrifice pour le péché, et un bélier pour l'holocauste, l'un et l'autre sans défaut, et offre-les devant l'Éternel.
Ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki ɗan maraƙi domin hadayarka don zunubi da kuma ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, dukan biyu su kasance marar lahani, ka miƙa su a gaban Ubangiji.
3 Et tu parleras aux enfants d'Israël, en disant: Prenez un bouc pour le sacrifice pour le péché; un veau et un agneau sans défaut, âgés d'un an, pour l'holocauste;
Sa’an nan ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ku ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa,
4 Un taureau et un bélier pour le sacrifice de prospérités, pour sacrifier devant l'Éternel, et une offrande arrosée d'huile; car aujourd'hui l'Éternel vous apparaîtra.
da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.’”
5 Ils amenèrent donc devant le tabernacle d'assignation ce que Moïse avait commandé; et toute l'assemblée s'approcha, et se tint devant l'Éternel.
Suka ɗauki abubuwan da Musa ya umarta zuwa gaban Tentin Sujada, sai dukan jama’a suka zo kusa suka tsaya a gaban Ubangiji.
6 Et Moïse dit: Voici ce que l'Éternel a commandé, faites-le, et la gloire de l'Éternel vous apparaîtra.
Sa’an nan Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarce ku ku yi, domin ɗaukakar Ubangiji za tă bayyana gare ku.”
7 Puis Moïse dit à Aaron: Approche-toi de l'autel; fais ton sacrifice pour le péché et ton holocauste, et fais l'expiation pour toi et pour le peuple; présente aussi l'offrande du peuple, et fais l'expiation pour lui, comme l'Éternel l'a commandé.
Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama’a. Ka kuma kawo hadayar jama’a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
8 Alors Aaron s'approcha de l'autel, et égorgea le veau de son sacrifice pour le péché.
Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa.
9 Et les fils d'Aaron lui présentèrent le sang; il trempa son doigt dans le sang, en mit sur les cornes de l'autel, et répandit le sang au pied de l'autel.
’Ya’yan Haruna maza suka kawo masa jinin, ya kuma tsoma yatsarsa a cikin jinin ya zuba cikin ƙahonin bagade; sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden.
10 Et il fit fumer sur l'autel la graisse, les rognons, et la membrane qui recouvre le foie de la victime pour le péché, comme l'Éternel l'avait commandé à Moïse.
A kan bagaden, ya ƙone kitsen, ƙodojin, da abin da ya rufe hanta, daga hadaya don zunubi, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
11 Mais il brûla au feu, hors du camp, la chair et la peau.
Naman da fatar kuwa ya ƙone waje da sansanin.
12 Ensuite il égorgea l'holocauste. Les fils d'Aaron lui présentèrent le sang, et il le répandit sur l'autel tout autour.
Sa’an nan ya yanka hadaya ta ƙonawa.’Ya’yan Haruna maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagaden.
13 Ils lui présentèrent aussi l'holocauste, coupé par morceaux, et la tête, et il les fit fumer sur l'autel.
Suka miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa-gunduwa, haɗe da kan, ya kuwa ƙone su a bisa bagaden.
14 Puis il lava les entrailles et les jambes, et il les fit fumer sur l'holocauste à l'autel.
Sai ya wanke kayan ciki da ƙafafun, ya kuwa ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a kan bagade.
15 Il offrit aussi l'offrande du peuple. Il prit le bouc du sacrifice pour le péché qui était pour le peuple; il l'égorgea, et l'offrit pour le péché, comme le premier sacrifice;
Sa’an nan Haruna ya kawo hadayar da take domin mutane. Ya ɗauki akuya ta hadaya don zunubin mutane, ya yanka shi, ya miƙa shi domin hadaya don zunubi kamar yadda ya yi da na farko.
16 Et il offrit l'holocauste, et le fit selon l'ordonnance.
Ya kawo hadaya ta ƙonawa ya kuma miƙa ta yadda aka tsara.
17 Ensuite il présenta l'offrande; il en remplit la paume de sa main, et la fit fumer sur l'autel, outre l'holocauste du matin.
Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗiba a tafi hannu ya ƙone a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa ta safe.
18 Il égorgea aussi le taureau et le bélier en sacrifice de prospérités pour le peuple. Les fils d'Aaron lui présentèrent le sang, et il le répandit sur l'autel tout autour.
Haruna ya yanka maraƙin da ragon a matsayin hadaya ta salama domin mutane.’Ya’yansa maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagade.
19 Ils lui présentèrent aussi la graisse du taureau et du bélier, la queue, ce qui couvre les entrailles, les rognons, et la membrane qui recouvre le foie;
Amma sashen kitsen maraƙin da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji da kuma kitsen da ya rufe hanta,
20 Et ils mirent les graisses sur les poitrines, et il fit fumer les graisses sur l'autel;
suka shimfiɗa waɗannan a kan ƙirjin, sa’an nan Haruna ya ƙone kitsen a kan bagade.
21 Puis Aaron agita devant l'Éternel, en offrande, les poitrines et la jambe droite, comme Moïse l'avait commandé.
Sai Haruna ya kaɗa ƙirjin da kuma cinyar dama a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa, kamar yadda Musa ya umarta.
22 Et Aaron éleva ses mains vers le peuple, et le bénit; et il descendit, après avoir offert le sacrifice pour le péché, l'holocauste et le sacrifice de prospérités.
Sa’an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa wajen mutane ya sa musu albarka. Da yake ya miƙa hadaya don zunubi, hadaya ta ƙonawa da kuma hadaya ta salama, sai ya sauka.
23 Alors Moïse et Aaron entrèrent dans le tabernacle d'assignation, puis ils sortirent et bénirent le peuple; et la gloire de l'Éternel apparut à tout le peuple:
Sai Musa da Haruna suka shiga cikin Tentin Sujada. Da suka fita, sai suka sa wa mutane albarka; sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutane.
24 Un feu sortit de devant l'Éternel, et consuma sur l'autel l'holocauste et les graisses; et tout le peuple le vit, et ils poussèrent des cris de joie, et se jetèrent sur leurs faces.
Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada.