< Tite 2 >
1 Pour toi, dis les choses qui sont conformes à la saine doctrine.
Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa.
2 Dis que les vieillards doivent être sobres, honnêtes, modérés, sains dans la foi, dans la charité, dans la patience.
Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.
3 Dis que les femmes âgées doivent aussi avoir l’extérieur qui convient à la sainteté, n’être ni médisantes, ni adonnées au vin; qu’elles doivent donner de bonnes instructions,
Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari.
4 dans le but d’apprendre aux jeunes femmes à aimer leurs maris et leurs enfants,
Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da’ya’yansu,
5 à être retenues, chastes, occupées aux soins domestiques, bonnes, soumises à leurs maris, afin que la parole de Dieu ne soit pas blasphémée.
su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.
6 Exhorte de même les jeunes gens à être modérés,
Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai.
7 te montrant toi-même à tous égards un modèle de bonnes œuvres, et donnant un enseignement pur, digne,
Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo
8 une parole saine, irréprochable, afin que l’adversaire soit confus, n’ayant aucun mal à dire de nous.
da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.
9 Exhorte les serviteurs à être soumis à leurs maîtres, à leur plaire en toutes choses, à n’être point contredisants,
Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana,
10 à ne rien dérober, mais à montrer toujours une parfaite fidélité, afin de faire honorer en tout la doctrine de Dieu notre Sauveur.
kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.
11 Car la grâce de Dieu, source de salut pour tous les hommes, a été manifestée.
Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane.
12 Elle nous enseigne à renoncer à l’impiété et aux convoitises mondaines, et à vivre dans le siècle présent selon la sagesse, la justice et la piété, (aiōn )
Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, (aiōn )
13 en attendant la bienheureuse espérance, et la manifestation de la gloire du grand Dieu et de notre Sauveur Jésus-Christ,
yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,
14 qui s’est donné lui-même pour nous, afin de nous racheter de toute iniquité, et de se faire un peuple qui lui appartienne, purifié par lui et zélé pour les bonnes œuvres.
wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.
15 Dis ces choses, exhorte, et reprends, avec une pleine autorité. Que personne ne te méprise.
Waɗannan kam, su ne abubuwan da ya kamata ka koyar, ka ƙarfafa ka kuma tsawata da dukan iko. Kada ka yarda wani yă rena ka.