< Ézéchiel 6 >

1 Et la parole du Seigneur me vint, disant:
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 Fils de l'homme, tourne la face contre les monts d'Israël, et prophétise contre eux.
“Ɗan mutum, ka kafa idonka a kan duwatsun Isra’ila; ka yi annabci a kansu
3 Et dis-leur: Montagnes d'Israël, écoutez la parole du Seigneur. Ainsi dit le Seigneur aux montagnes, aux collines, aux vallons et aux forêts: Voilà que j'amène contre vous le glaive, et vos hauts lieux seront détruits.
ka ce, ‘Ya ku duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa duwatsu da tuddai, ga rafuffuka da kuma kwaruruka. Ina shirin kawo takobi a kanku, kuma zan hallaka masujadanku.
4 Et vos autels seront brisés, et vos enclos détruits; et je jetterai vos cadavres en face de vos idoles.
Za a ragargaza bagadanku a kuma farfasa bagadanku na ƙone turare; zan kuma kashe mutanenku a gaban gumakanku.
5 Et je disperserai vos ossements autour de vos autels,
Zan shimfiɗa gawawwakin Isra’ilawa a gaban gumakansu, in kuma watsar da ƙasusuwanku kewaye da bagadanku.
6 Et dans toutes vos demeures. Vos villes seront dépeuplées et vos hauts lieux abolis, afin que vos autels soient abattus, vos idoles brisées et vos enclos détruits.
Duk inda kuke zama, garuruwa za su zama kango, za a kuma ragargaza masujadai, saboda bagadanku su rurrushe su zama kango, a kuma farfasa gumakanku su lalace, za a rurrushe bagadan ƙone turarenku, a kuma shafe dukan abin da kuka yi.
7 Et les cadavres tomberont au milieu de vous, et vous saurez que je suis le Seigneur.
Za a kashe mutanenku a cikinku, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.
8 Quand ceux de vous qui auront échappé au glaive seront parmi les nations, pendant votre dispersion dans les royaumes,
“‘Amma zan bar waɗansu, gama waɗansunku za su tsere wa takobi sa’ad da aka watsar da ku a cikin ƙasashe da al’ummai.
9 Ceux de vous qui auront échappé et qui seront captifs parmi les nations se souviendront de moi. J'ai juré contre leur cœur, qui s'est prostitué loin de moi, contre leurs yeux, qui se sont prostitués à leurs désirs. Et ils se frapperont au visage en souvenir de toutes leurs abominations.
Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata.
10 Et ils reconnaîtront que moi, le Seigneur, j'ai parlé.
Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji; ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.
11 Voici ce que dit le Seigneur: Bats des mains, frappe du pied, et dis: Malheur, malheur sur toutes les abominations de la maison d'Israël! Ils périront par le glaive, par la peste et par la famine.
“‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ku tafa hannuwanku tare ku kuma taka ƙafafunku ku yi ihu ku ce, “Kaito!” Saboda dukan mugaye da kuma abubuwan banƙyama na gidan Isra’ila, gama za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba.
12 Celui qui est près tombera sous le glaive; celui qui est loin périra par la peste; et celui qui est assiégé mourra de faim. Et j'assouvirai sur eux ma colère.
Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.
13 Et vous saurez que je suis le Seigneur, quand vos cadavres seront au milieu de vos idoles, autour de vos autels sur toute haute colline, sous chaque arbre touffu, où ils offraient les odeurs de l'encens à toutes leurs idoles.
Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu.
14 Et j'étendrai la main sur eux, et je désolerai la terre, et je la ruinerai dans toutes ses demeures à partir du désert de Déblatha. Et vous saurez que je suis le Seigneur.
Zan kuma miƙa hannuna a kansu in mai da ƙasarsu kango daga hamadan Dibila, a duk inda suke zama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’”

< Ézéchiel 6 >