< 2 Chroniques 7 >

1 Aussitôt que Salomon eut achevé sa prière, le feu du ciel descendit et dévora les holocaustes, et la gloire du Seigneur remplit le temple.
Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.
2 Et, à ce moment-là, les prêtres ne purent entrer dans le temple, parce qu'il était rempli de la gloire du Seigneur.
Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi.
3 Et tous les fils d'Israël virent le feu descendre; et la gloire du Seigneur remplir l'édifice, et ils tombèrent la face sur le pavé du temple, et ils adorèrent le Seigneur, et ils le louèrent, à cause de sa bonté et de sa miséricorde infinies.
Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
4 Ensuite, le roi et tout le peuple immolèrent des victimes devant le Seigneur.
Sai sarki da dukan mutanen suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji.
5 Et le roi Salomon offrit en sacrifice vingt-deux mille bœufs, et cent vingt mille têtes de menu bétail; le roi et tout le peuple firent ainsi la dédicace du temple de Dieu.
Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah.
6 Et les prêtres; chacun à son poste, et les lévites, avec les instruments et les chants du roi David, rendaient gloire au Seigneur et à sa miséricorde éternelle; devant eux, des prêtres sonnaient de la trompette, et tout le peuple se tenait debout.
Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.
7 Et Salomon consacra le milieu du parvis du temple, car c'est là qu'il offrit les holocaustes et qu'il brûla la graisse des hosties pacifiques; car l'autel d'airain, qu'avait fait Salomon, ne suffisait pas à contenir les holocaustes, les oblations et la graisse.
Solomon ya tsarkake sashen tsakiya na filin da yake gaban haikalin Ubangiji, a can ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayun salama domin bagaden tagullar da ya yi ba zai iya ɗaukan hadayun ƙonawa, hadayun hatsi da kuma ɓangarori na kitsen ba.
8 Et le roi Salomon, en ce même temps-là, fit une fête de sept jours; avec lui était Israël, grande assemblée venue depuis l'entrée d'Emath jusqu'au fleuve d'Égypte.
Ta haka Solomon ya kiyaye bikin a wannan lokaci har kwana bakwai, dukan Isra’ila kuwa tare da shi, babban taro, mutane daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar.
9 Et le huitième jour il sanctifia la fin de la fête, parce que la fête de la Dédicace de l'autel avait duré sept jours.
A rana ta takwas sai suka yi taro, gama sun yi bikin keɓewar bagade na kwana bakwai da kuma biki na ƙarin kwana bakwai.
10 Et le vingt-troisième jour du septième mois, il renvoya le peuple, chacun en sa demeure, la joie dans le cœur, pénétré des biens que le Seigneur avait accordés à David, à Salomon et à Israël, son peuple.
A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila.
11 Or, Salomon avait achevé le temple du Seigneur, et son propre palais; et tout ce qu'en son âme il avait désiré faire dans le temple et dans le palais, il l'avait heureusement accompli.
Sa’ad da Solomon ya gama haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki ya kuma yi nasara a yin dukan abin da yake a zuciyarsa da zai yi a haikalin Ubangiji da kuma a fadarsa,
12 Et le Seigneur lui apparut pendant la nuit, et il dit: J'ai entendu ta prière; je me suis choisi ce lieu pour qu'il y eût un temple où l'on me sacrifiât.
sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.
13 Si je ferme le ciel et qu'il n'y ait point de pluie; si je commande aux sauterelles de dévorer vos arbres; si j'envoie la peste à mon peuple;
“Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena,
14 Et si mon peuple, pour qui mon nom est invoqué, rentre en soi-même, s'il prie, s'il désire ma présence, s'il se détourne de la mauvaise voie, je l'entendrai du haut du ciel; je serai miséricordieux pour ses péchés, et je guérirai sa terre.
in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.
15 Et mes yeux seront ouverts, et mes oreilles seront attentives à la prière qui sera faite eu ce temple.
Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri.
16 Car j'ai choisi et sanctifié cette demeure pour que mon nom y réside éternellement, et mes yeux et mon cœur y seront dans tous les siècles.
Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.
17 Et, si tu marches devant moi comme ton père, si tu fais ce que je t'ai prescrit, si tu observes mes commandements et mes préceptes,
“Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina,
18 Je maintiendrai ton trône royal, selon l'alliance que j'ai faite avec David, disant: Jamais, en Israël, il ne manquera de chef issu de toi.
zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’
19 Mais si vous vous pervertissez, si vous abandonnez les commandements et les préceptes que j'ai mis devant vous, si vous suivez, si vous servez d'autres dieux, si vous les adorez,
“Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada,
20 Je vous enlèverai de la terre que j'ai donnée à vos pères, je rejetterai loin de ma vue ce temple que j'ai consacré à mon nom; j'en ferai la fable et le jouet des gentils.
zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane.
21 Et cette demeure superbe, le passant, à son aspect, sera frappé de stupeur, et il s'écriera: Quel sujet a donc eu le Seigneur pour traiter ainsi leur terre et ce temple?
Ko da yake wannan haikali yanzu mai girma ne, dukan wanda ya wuce zai kaɗa kai yă ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi irin wannan abu ga wannan ƙasa da kuma ga wannan haikali?’
22 Et l'on répondra: C'est qu'ils ont abandonné le Seigneur Dieu de leurs pères, qui les avait ramenés de l'Égypte, et qu'ils ont pris d'autres dieux, qu'ils les ont adorés, qu'ils les ont servis; à cause de cela, il a fait fondre sur eux tous ces maux.
Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’”

< 2 Chroniques 7 >