< Genèse 31 >
1 Or, il fut instruit des propos des fils de Laban, qui disaient: "Jacob s’est emparé de tout ce que possédait notre père; c’est des biens de notre père qu’il a créé toute cette opulence."
Yaƙub ya ji cewa’ya’ya Laban mazan suna cewa, “Yaƙub ya kwashe dukan abin da mahaifinmu yake da shi, ya kuma sami dukan wannan arziki daga abin da yake na mahaifinmu.”
2 Jacob remarqua que la face de Laban n’était plus à son égard comme précédemment.
Yaƙub kuma ya lura cewa halin Laban gare shi ya canja ba kamar yadda yake a dā ba.
3 Et l’Éternel dit à Jacob: "Retourne au pays de tes pères, dans ton lieu natal; je serai avec toi."
Sai Ubangiji ya ce wa Yaƙub, “Koma ƙasar kakanninka da kuma danginka, zan kuwa kasance tare da kai.”
4 Alors Jacob envoya quérir Rachel et Léa aux champs, près de son troupeau;
Saboda haka Yaƙub ya aika a ce wa Rahila da Liyatu su zo jeji inda garkunan suke.
5 et il leur dit: "Je vois, au visage de votre père, qu’il n’est plus pour moi comme hier ni avant hier; mais le Dieu de mon père a été avec moi.
Sai ya ce musu, “Na ga cewa halin mahaifinku gare ni ba kamar yadda dā yake ba, amma Allah na mahaifina yana tare da ni.
6 Pour vous, vous savez que j’ai servi votre père de toutes mes forces,
Kun san cewa na yi aiki wa mahaifinku da dukan ƙarfina,
7 tandis que votre père s’est joué de moi et dix fois a changé mon salaire; mais Dieu n’a pas permis qu’il me fit du tort.
duk da haka mahaifinku ya cuce ni ta wurin sauya albashina sau goma. Amma dai, Allah bai yardar masa yă yi mini lahani ba.
8 Lorsqu’il parlait ainsi: ‘Les bêtes pointillées seront ton salaire’, tout le bétail produisait des animaux pointillés; disait-il: ‘Les rayés seront ton salaire’, tout le bétail en produisait des rayés.
In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne.
9 C’Est Dieu qui a dégagé le bétail de votre père et me l’a donné.
Ta haka Allah ya kwashe dabbobin mahaifinku ya ba ni.
10 Or, à l’époque où les troupeaux s’accouplent, je levai les yeux et j’eus une vision et voici que les mâles qui fécondaient le bétail étaient rayés, pointillés et grivelés.
“A lokacin ɗaukar cikin garken, na taɓa yin mafarki inda na ga bunsuran da suke barbara da garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne.
11 Un envoyé du Seigneur me dit dans la vision: ‘Jacob!’ Je répondis: ‘Me voici.’
Sai mala’ikan Allah ya ce mini a mafarkin, ‘Yaƙub.’ Sai na amsa na ce, ‘Ga ni.’
12 II reprit: ‘Lève les yeux et regarde; tous les mâles qui fécondent le bétail sont rayés, pointillés et grivelés. C’Est que j’ai vu la conduite de Laban à ton égard.
Ya ce, ‘Ɗaga idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne, gama na ga dukan abin da Laban yake yin maka.
13 Je suis la Divinité de Béthel, où tu as consacré un monument, où tu as prononcé un vœu en mon honneur. Maintenant, dispose-toi à sortir de ce pays et retourne au pays de ta naissance.’"
Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’”
14 Pour réponse, Rachel et Léa lui dirent: "Est il encore pour nous une part et un héritage dans la maison de notre père?
Sai Rahila da Liyatu suka amsa suka ce, “Muna da wani rabo a gādon kayan mahaifinmu ne?
15 N’Avons nous pas été considérées par lui comme des étrangères, puisqu’il nous a vendues? Il a consommé, oui, consommé notre bien!
Ba kamar baƙi ne yake ɗaukarmu ba? Ba sayar da mu kaɗai ya yi ba, har ma ya yi amfani da abin da aka biya saboda mu.
16 Certes, toute la fortune que Dieu a retirée à notre père, elle est à nous et à nos enfants; et maintenant, tout ce que Dieu t’a dit, fais le."
Tabbatacce dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga mahaifinmu ya zama namu da’ya’yanmu. Saboda haka ka yi duk abin da Allah ya faɗa maka.”
17 Jacob s’y disposa. Il fit monter ses fils et ses femmes sur les chameaux;
Sa’an nan Yaƙub ya sa’ya’yansa da matansa a kan raƙuma,
18 il emmena tout son bétail avec tous les biens qu’il avait amassés, possessions à lui, qu’il avait acquises dans le territoire d’Aram et s’achemina vers son père Isaac au pays de Canaan.
ya kuma kora dukan dabbobinsa, suka ja gabansa, tare da dukan abubuwan da ya samu a Faddan Aram, don su tafi wurin mahaifinsa Ishaku a ƙasar Kan’ana.
19 Comme Laban était allé faire la tonte de ses brebis, Rachel déroba les pénates de son père.
Sa’ad da Laban ya tafi don askin tumakinsa, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.
20 Jacob trompa l’esprit de Laban l’Araméen, en s’enfuyant sans lui rien dire.
Yaƙub kuwa ya ruɗe Laban mutumin Aram da bai sanar da shi zai gudu ba.
21 II s’enfuit donc, lui et tout ce qui lui appartenait; il se mit en devoir de passer le fleuve, puis il se dirigea vers le mont Galaad.
Saboda haka ya gudu da dukan abin da ya mallaka, ya ƙetare Kogi, ya nufi yankin tuddan Gileyad.
22 Laban fut informé, le troisième jour, que Jacob s’était enfui.
A rana ta uku, sai aka faɗa wa Laban cewa Yaƙub ya gudu.
23 Il prit ses frères avec lui, le poursuivit l’espace de sept journées et le joignit au mont Galaad.
Sai Laban ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi bayan Yaƙub har kwana bakwai, ya kuma same shi a yankin tuddan Gileyad.
24 Mais Dieu visita Laban l’Araméen dans un songe nocturne et lui dit: "Garde toi d’interpeller Jacob, en bien ou en mal."
Sai Allah ya bayyana ga Laban mutumin Aram a mafarki da dare, ya ce masa, “Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu, ko mai kyau ko marar kyau.”
25 Laban arriva jusqu’à Jacob. Or, Jacob avait dressé sa tente sur la montagne et Laban posta ses frères sur la même montagne de Galaad.
Yaƙub ya riga ya kafa tentinsa a yankin tuddan Gileyad sa’ad da Laban ya same shi. Laban da danginsa suka kafa sansani a can su ma.
26 Laban dit à Jacob: "Qu’as-tu fait? Tu as abusé mon esprit et tu as emmené mes filles comme des prisonnières de guerre!
Sai Laban ya ce wa Yaƙub, “Me ke nan ka yi? Ka ruɗe ni, ka kuma ɗauki’ya’yana mata kamar kamammun yaƙi.
27 Pourquoi t’es tu enfui furtivement et m’as tu trompé et ne m’as tu rien dit? Mais je t’aurais reconduit avec allégresse, avec des chants, au son du tambourin et de la harpe!
Me ya sa ka gudu a ɓoye ka kuma ruɗe ni? Me ya sa ba ka faɗa mini don in sallame ka da farin ciki da waƙoƙi haɗe da kiɗin ganguna da garayu ba?
28 Et puis, tu ne m’as pas laissé embrasser mes fils et mes filles! Certes, tu as agi en insensé.
Ba ka ma bari in sumbaci jikokina da’ya’yana mata in yi musu bankwana ba. Ka yi wauta.
29 Il serait au pouvoir de ma main de vous faire du mal; mais le Dieu de votre père, cette nuit, m’a parlé ainsi: ‘Garde toi d’interpeller Jacob, soit en bien, soit en mal.’
Ina da iko in cuce ka; amma jiya da dare Allahn mahaifinka ya faɗa mini, ‘Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu ko mai kyau ko marar kyau.’
30 Et maintenant que tu t’en vas, parce que tu soupires après la maison de ton père, pourquoi as tu dérobé mes dieux?"
Yanzu ka gudu domin kana marmari komawa gidan mahaifinka. Amma don me ka sace mini gumakana?”
31 Jacob répondit en ces termes à Laban: "J’Ai craint, parce que je me disais que tu pourrais m’enlever de force tes filles.
Yaƙub ya amsa wa Laban, “Na ji tsoro ne, domin na yi tsammani za ka ƙwace’ya’yanka mata daga gare ni ƙarfi da yaji.
32 Quant à celui que tu trouverais en possession de tes dieux, qu’il cesse de vivre! En présence de nos frères, vérifie toi même ce qui est par devers moi et reprends ton bien." Or, Jacob ne savait pas que Rachel les avait dérobés.
Amma in ka sami wani wanda yake da gumakanka, ba zai rayu ba. Kai da kanka ka duba a gaban danginmu, ko akwai wani abin da yake naka a nan tare da ni; in ka gani, ka ɗauka.” Yaƙub dai bai san cewa Rahila ta sace gumakan ba.
33 Laban entra dans la tente de Jacob, dans celle de Léa, dans celle des deux servantes et ne les trouva point. Étant sorti de la tente de Léa, il entra dans celle de Rachel.
Saboda haka Laban ya shiga tentin Yaƙub, ya shiga tentin Liyatu da kuma tentuna matan nan biyu bayi, amma bai sami kome ba. Bayan ya fita daga tentin Liyatu, sai ya shiga tentin Rahila.
34 Mais Rachel avait pris les pénates, les avait cachés dans la selle du chameau et s’était assise dessus. Laban fouilla toute la tente et ne les trouva point.
Rahila fa ta kwashe gumakan gidan ta sa su cikin sirdin raƙumi, ta kuma zauna a kansu. Laban ya bincika cikin kowane abu a tentin amma bai sami kome ba.
35 Elle dit à son père: "Ne sois pas offensé, mon seigneur, si je ne puis me lever devant toi à cause de l’incommodité habituelle des femmes." II chercha encore et il ne trouva point les pénates.
Sai Rahila ta ce wa mahaifinta, “Kada ka yi fushi, ranka yă daɗe da ban tashi tsaye a gabanka ba; gama ina al’adar mata ne.” Saboda haka ya bincika amma bai sami gumakan gidan ba.
36 Jacob s’emporta en plaintes contre Laban; il se récria, disant à Laban: "Quel est mon crime, quelle est ma faute, pour que tu t’acharnes après moi?
Yaƙub ya fusata, ya kuma yi wa Laban faɗa. Ya tambayi Laban, “Mene ne laifina? Wanda zunubi na yi da kake farautata?
37 Après avoir fureté tout mon ménage, qu’as tu découvert qui appartienne à ta maison? Éxpose le ici, en présence de mes frères et des tiens et qu’ils se prononcent entre nous deux!
Yanzu da ka bincika dukan kayayyakina, me ka samu da yake na gidanka? Kawo shi nan a gaban danginka da kuma dangina, bari su zama alƙali tsakaninmu biyu.
38 Ces vingt ans que j’ai été chez toi, tes brebis, ni tes chèvres n’ont avorté et les béliers de ton troupeau, je n’en ai point mangé.
“Na kasance tare da kai shekaru ashirin. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuwa ci raguna daga garkunanka ba.
39 La bête mise en pièces, je ne te l’ai point rapportée; c’est moi qui en souffrais le dommage, tu me la faisais payer, qu’elle eût été prise le jour, qu’elle eût été ravie la nuit.
Ban kawo dabbobinka da namun jeji suka yayyaga; na kuma ɗauki hasarar ba? Ka nemi in biya dukan abin da aka sace da rana ko da dare.
40 J’Étais, le jour, en proie au hâle et aux frimas la nuit; et le sommeil fuyait de mes yeux.
Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci.
41 J’Ai passé ainsi vingt années dans ta maison! Je t’ai servi quatorze ans pour tes deux filles et six ans pour ton menu bétail et tu as changé dix fois mon salaire.
Haka ya kasance shekaru ashirin da na yi a gidanka. Na yi maka aiki shekaru goma sha huɗu domin’ya’yanka mata biyu, na kuma yi shekaru shida domin garkunanka, ka kuma canja albashina sau goma.
42 Si le Dieu de mon père, le Dieu d’Abraham et celui que révère Isaac ne m’était venu en aide, certes, actuellement tu m’aurais laissé partir les mains vides. Dieu a vu mon humiliation et le labeur de mes mains et il a prononcé hier."
Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.”
43 Laban répondit à Jacob: "Ces filles sont mes filles et ces fils sont mes fils et ce bétail est le mien; tout ce que tu vois m’appartient. Étant mes filles, comment agirais je contre elles, dès lors, ou contre les fils qu’elles ont enfantés?
Laban ya amsa wa Yaƙub, “Matan,’ya’yana ne,’ya’yansu,’ya’yana ne, garkunan kuma garkunana ne. Dukan abin da kake gani, nawa ne. Duk da haka me zan yi a rana ta yau ga waɗannan’ya’yana mata, ko kuma ga’ya’yan da suka haifa?
44 Maintenant, tiens, concluons une alliance, moi et toi, ce sera une alliance entre nous deux."
Zo, bari mu ƙulla yarjejjeniya, da kai da ni, bari kuma ta kasance shaida a tsakaninmu.”
45 Jacob prit une pierre et l’érigea en monument.
Saboda haka Yaƙub ya ɗauki dutse ya kafa yă zama al’amudi.
46 Et il dit à ses frères: "Ramassez des pierres." Ils prirent des pierres et en firent un monceau et l’on mangea là, sur le monceau.
Ya ce wa danginsa. “Ku tattara waɗansu duwatsu.” Sai suka kwashe duwatsu suka tsiba, suka kuwa ci abinci a can kusa da tsibin.
47 Laban l’appela Yegar Sahadouthâ et Jacob le nomma Galed.
Laban ya sa masa suna Yegar Sahaduta, Yaƙub kuwa ya kira shi Galeyed.
48 Laban avait dit: "Ce monceau est un témoin entre nous deux dès aujourd’hui." De là on énonça son nom Galed;
Laban ya ce, “Wannan tsibi, shi ne shaida tsakaninka da ni a yau.” Shi ya sa aka kira shi Galeyed.
49 et aussi Miçpa, parce qu’il dit: "L’Éternel sera présent entre nous deux, alors que nous serons cachés l’un à l’autre.
Aka kuma kira shi Mizfa, domin ya ce, “Ubangiji yă sa ido tsakanin ni da kai sa’ad da muka rabu da juna.
50 Si tu outrageais mes filles; si tu associais d’autres épouses à mes filles nul n’est avec nous; mais vois! Dieu est témoin entre moi et toi!"
Laban ya ce in ka wulaƙanta’ya’yana mata, ko ka auri waɗansu mata ban da’ya’yana mata, ko da yake babu wani da yake tare da mu, ka tuna cewa Allah shi ne shaida tsakaninka da ni.”
51 Laban dit à Jacob: "Tu vois ce monceau, tu vois ce monument que j’ai posé entre nous deux; soit témoin ce monceau,
Laban ya kuma ce wa Yaƙub, “Ga wannan tsibi, ga kuma wannan al’amudin da na kafa tsakaninka da ni.
52 soit témoin cette pierre, que je ne dépasserai point de ton côté ce monceau, que tu ne dépasseras point de mon côté ce monceau ni cette pierre, dans des vues mauvaises.
Wannan tsibin shi ne shaida, wannan al’amudi kuma shaida ne, cewa ba zan tsallake wannan tsibi zuwa gefenka don in cuce ka ba, kai kuma ba za ka tsallake wannan tsibi da al’amudi zuwa gefena don ka cuce ni ba.
53 Puissent nous juger le Dieu d’Abraham et le dieu de Nahor, les divinités de leur père!" Et Jacob jura par le Dieu révéré de son père Isaac.
Bari Allah na Ibrahim da Allah na Nahor, Allah na iyayensu, yă zama alƙali tsakaninmu.” Saboda haka Yaƙub ya yi rantsuwa da sunan Tsoron mahaifinsa Ishaku.
54 Jacob égorgea des animaux sur la montagne et invita ses parents au festin. Ils y prirent part et passèrent la nuit sur la montagne.
Ya miƙa hadaya a can a ƙasar tudu, ya kuma gayyaci danginsa zuwa wurin cin abinci. Bayan suka ci, sai suka kwana a can.
55 Laban se leva de bon matin, embrassa ses fils et ses filles et les bénit; puis il partit et s’en retourna chez lui.
Da sassafe kashegari sai Laban ya sumbaci jikokinsa da’ya’yansa mata, ya sa musu albarka. Sa’an nan ya yi bankwana da su, ya koma gida.