< Nombres 18 >

1 Yahweh dit à Aaron: « Toi et tes fils, et la maison de ton père avec toi, vous porterez l’iniquité du sanctuaire; toi et tes fils avec toi, vous porterez l’iniquité de votre sacerdoce.
Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da’ya’yanka, da kuma iyalin mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi Tentin Sujada, kai da’ya’yanka kaɗai za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci.
2 Fais aussi approcher avec toi du sanctuaire tes autres frères, la tribu de Lévi, la tribu de ton père, afin qu’ils te soient adjoints et qu’ils te servent, lorsque toi, et tes fils avec toi, vous serez devant la tente du témoignage.
Ka kawo’yan’uwanka Lawiyawa daga kabilar kakanka tare da kai, don su taimake ka sa’ad da kai da’ya’yanka kuke hidima a gaban Tentin Sujada.
3 Ils rempliront ton service et le service de toute la tente; mais ils ne s’approcheront ni des ustensiles du sanctuaire, ni de l’autel, de peur que vous ne mouriez, eux et vous.
Za su kasance a ƙarƙashinka, su ne kuma za su yi dukan hidima ta Tenti, amma kada su je kusa da kayayyakin wuri mai tsarki, ko bagade, in ba haka ba, da kai da su, za ku mutu.
4 Ils te seront adjoints, et ils rempliront le service de la tente de réunion, pour tout le travail de la tente. Aucun étranger n’approchera de vous.
Za su haɗa hannu tare da kai su ɗauki nauyin lura da Tentin Sujada, dukan ayyuka a Tenti, ba kuma wanda zai zo kusa da inda kake.
5 Vous remplirez le service du sanctuaire et le service de l’autel, afin qu’il n’y ait plus de colère contre les enfants d’Israël.
“Kai ne za ka ɗauki nauyin lura da wuri mai tsarki da bagade, domin kada fushi yă sāke fāɗa a kan Isra’ilawa.
6 Voici, j’ai pris vos frères les lévites du milieu des enfants d’Israël; donnés à Yahweh, ils vous sont remis en don pour faire le travail de la tente de réunion.
Ni da kaina na zaɓo’yan’uwanka Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a matsayin kyauta a gare ku, keɓaɓɓu don Ubangiji, domin su yi hidima a Tentin Sujada.
7 Toi et tes fils avec toi, vous remplirez votre sacerdoce pour tout ce qui concerne l’autel et pour ce qui est en dedans du voile: vous ferez ce travail. Comme une fonction en pur don, je vous confère votre sacerdoce. L’étranger qui approchera sera mis à mort. »
Amma kai ne kaɗai da’ya’yanka za ku yi aiki a matsayin firistoci game da kowane abu a Tentin Sujada da kuma bayan labule. Ina ba ka aikin firist, yă zama naka. Duk wani kuma da ya zo kusa da wuri mai tsarki, dole a kashe shi.”
8 Yahweh dit à Aaron: « Voici, je te donne le service de ce qui est prélevé pour moi, de toutes les choses consacrées des enfants d’Israël; je te les donne, à raison de l’onction que tu as reçue, à toi et à tes fils, par une loi perpétuelle.
Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayun da za a miƙa mini, dukan tsarkakan hadayun da Isra’ilawa suka ba ni, na ba ka su su zama rabonka da na’ya’yanka har abada.
9 Voici ce qui te reviendra des choses très saintes, sauf ce que le feu doit consumer: toutes leurs offrandes, savoir toutes leurs oblations, tous leurs sacrifices pour le péché et tous leurs sacrifices de réparation qu’ils me rendront: tout cela, comme choses très saintes, sera pour toi et pour tes fils.
Kai za ka riƙe sashe mafi tsarki na hadayun da suka ragu daga wuta. Daga dukan kyautai mafi tsarki na hadayun da suka miƙa mini, ko ta gari, ko don zunubi, ko kuma don laifi, wannan kashi naka ne da’ya’yanka.
10 Tu les mangeras dans un lieu très saint; tout mâle en mangera; elles seront saintes pour toi.
Ku ci shi a matsayin abu mafi tsarki; kowane namiji zai ci. Dole ku ɗauke shi da tsarki.
11 Ceci encore t’appartient: ce qui est prélevé sur leurs dons, sur toute offrande balancée des enfants d’Israël; je te le donne à toi, à tes fils et à tes filles avec toi, par une loi perpétuelle; quiconque est pur dans ta maison en mangera.
“Har yanzu kuma duk abin da aka keɓe daga kyautai na dukan hadayun kaɗawa na Isra’ilawa naka ne. Na ba da wannan gare ka da’ya’yanka maza da mata, a kowane lokaci. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
12 Tout le meilleur de l’huile, tout le meilleur du vin nouveau et du blé, leurs prémices qu’ils offrent à Yahweh, je te les donne.
“Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji.
13 Les premiers produits de leur terre qu’ils apporteront à Yahweh seront pour toi. Quiconque est pur dans ta maison en mangera.
Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
14 Tout ce qui sera dévoué par anathème en Israël sera pour toi.
“Kome a Isra’ila da aka keɓe wa Ubangiji, zai zama naka.
15 Tout premier-né de toute chair, des hommes comme des animaux, qu’ils offrent à Yahweh, sera pour toi. Seulement tu feras racheter le premier-né de l’homme, et tu feras racheter le premier-né d’un animal impur.
Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.
16 Quant à son rachat, tu le feras racheter dès l’âge d’un mois, selon ton estimation, contre cinq sicles d’argent, selon le sicle du sanctuaire, qui est de vingt guéras.
Sa’ad da suke wata ɗaya da haihuwa, dole a fanshe su a bakin shekel biyar-biyar, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri da ake amfani da shi, wanda nauyinsa ya kai gera ashirin.
17 Mais tu ne feras pas racheter le premier-né du bœuf, ni le premier-né de la brebis, ni le premier-né de la chèvre: ils sont saints. Tu répandras leur sang sur l’autel et tu feras fumer leur graisse: c’est un sacrifice fait par le feu, d’une agréable odeur à Yahweh.
“Amma kada ka fanshe ɗan fari na saniya, tunkiya, ko akuya; gama suna da tsarki. Ka yayyafa jininsu a bisan bagade, ka kuma ƙone kitsensu kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
18 Leur chair sera pour toi, comme la poitrine qu’on balance et comme la cuisse droite.
Namansu zai zama naka, haka ma ƙirji na kaɗawa da cinyar dama za su zama naka.
19 Tout ce qui est prélevé sur les choses saintes, ce que les enfants d’Israël prélèvent pour Yahweh, je te le donne à toi, à tes fils et à tes filles avec toi, par une loi perpétuelle; c’est une alliance de sel, perpétuelle, devant Yahweh, pour toi et pour ta postérité avec toi. »
Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.”
20 Yahweh dit à Aaron: « Tu n’auras pas d’héritage dans leur pays, et il n’y aura pas de part pour toi au milieu d’eux; c’est moi qui suis ta part et ton héritage au milieu des enfants d’Israël.
Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa.
21 Voici que je donne comme héritage aux fils de Lévi toute dîme en Israël, pour le travail qu’ils font, le travail de la tente de réunion.
“Na ba wa Lawiyawa dukan zakka na Isra’ilawa a matsayin gādonsu, saboda aikin da suke yi yayinda suke hidima a Tentin Sujada.
22 Les enfants d’Israël n’approcheront plus de la tente de réunion, de peur qu’ils ne portent leur péché et qu’ils meurent.
Daga yanzu zuwa gaba, kada Isra’ilawa su yi kusa da Tentin Sujada, in ba haka ba kuwa su sha hukuncin zunubinsu, su kuma mutu.
23 Les Lévites feront le travail de la tente de réunion, et ils porteront leur iniquité. En vertu d’une loi perpétuelle parmi vos descendants, ils n’auront pas d’héritage au milieu des enfants d’Israël.
Lawiyawa ne za su yi aikin Tentin Sujada, su kuma ɗauki nauyin kowane laifin da aka aikata a wurin. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce daga yanzu har tsararraki masu zuwa. Ba za su sami gādo a cikin Isra’ilawa ba.
24 Car je donne aux Lévites comme héritage les dîmes que les enfants d’Israël prélèveront pour Yahweh; c’est pourquoi je leur dis: Ils n’auront pas d’héritage au milieu des enfants d’Israël. »
A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’”
25 Yahweh parla à Moïse, en disant:
Ubangiji ya ce wa Musa,
26 « Tu parleras aux Lévites et tu leur diras: “Lorsque vous recevrez des enfants d’Israël la dîme que je vous donne de leurs biens pour votre héritage, vous en prélèverez une offrande pour Yahweh, une dîme de la dîme;
“Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji.
27 et ce prélèvement que vous ferez vous sera compté comme le blé qu’on prélève de l’aire, et comme le vin nouveau qu’on prélève de la cuve.
Za a lissafta hadayarku kamar hatsin da aka sussuka daga masussuka, ko ruwan inabi daga wurin matsewar inabi.
28 C’est ainsi que vous prélèverez, vous aussi, une offrande pour Yahweh, sur toutes les dîmes que vous recevrez des enfants d’Israël, et cette offrande que vous en aurez prélevée pour Yahweh, vous la donnerez au prêtre Aaron.
Ta haka za ku miƙa hadaya ga Ubangiji daga cikin dukan zakkar da kuka karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga waɗannan zakka kuwa dole ku ba Haruna firist rabon Ubangiji.
29 Sur tous les dons que vous recevrez, vous prélèverez toute l’offrande de Yahweh; sur tout le meilleur, la sainte portion qui en est tirée.
Dole ku miƙa wa Ubangiji rabo mafi kyau da kuma sashi mafi tsarki na kowane abin da aka ba ku.’
30 Tu leur diras: Quand vous en aurez prélevé le meilleur, la dîme sera comptée aux lévites comme le produit de l’aire et comme le produit du pressoir.
“Ka faɗa wa Lawiyawa cewa, ‘Sa’ad da kuka miƙa sashi mafi kyau, za a lissafta shi a matsayin abin da ya fito daga masussuka, ko wurin matsewar ruwan inabi ne.
31 Vous la mangerez en tout lieu, vous et votre famille; car c’est votre salaire pour le travail que vous faites dans la tente de réunion.
Da kai da gidanka, za ku iya cin abin da ya rage a ko’ina, gama ladan aikinku ne a Tentin Sujada.
32 Vous ne porterez pour cela aucun péché, quand vous en aurez prélevé le meilleur, vous ne profanerez pas les saintes offrandes des enfants d’Israël, et vous ne mourrez point.” »
Ta wurin miƙa masa sashi mafi kyau, ba za ku zama masu laifi a wannan batu ba; ta haka ba za ku ƙazantar da tsarkakakkun hadayu na Isra’ilawa ba, ba kuwa za ku mutu ba.’”

< Nombres 18 >