< Genèse 30 >
1 Rachel voyant qu’elle n’enfantait pas d’enfant à Jacob, fut jalouse de sa sœur, et elle dit à Jacob: « Donne-moi des enfants, ou je meurs! »
Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub’ya’ya ba, sai ta fara kishin’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni’ya’ya, ko kuwa in mutu!”
2 La colère de Jacob s’enflamma contre Rachel, et il dit: « Suis-je à la place de Dieu, qui t’a refusé la fécondité? »
Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun’ya’ya?”
3 Elle dit: « Voici ma servante Bala; va vers elle; qu’elle enfante sur mes genoux, et par elle j’aurai, moi aussi, une famille. »
Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.”
4 Et elle lui donna Bala, sa servante, pour femme, et Jacob alla vers elle.
Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita,
5 Bala conçut et enfanta un fils à Jacob.
ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa.
6 Et Rachel dit: « Dieu m’a rendu justice, et même il a entendu ma voix et m’a donné un fils. » C’est pourquoi elle le nomma Dan.
Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan.
7 Bala, servante de Rachel, conçut encore et enfanta un second fils à Jacob.
Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu.
8 Et Rachel dit: « J’ai lutté auprès de Dieu à l’encontre de ma sœur, et je l’ai emporté. » Et elle le nomma Nephthali.
Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali.
9 Lorsque Lia vit qu’elle avait cessé d’avoir des enfants, elle prit Zelpha, sa servante, et la donna pour femme à Jacob.
Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa.
10 Zelpha, servante de Lia, enfanta un fils à Jacob;
Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa.
11 et Lia dit: « Quelle bonne fortune! » et elle le nomma Gad.
Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad.
12 Zelpha, servante de Lia, enfanta un second fils à Jacob;
Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu.
13 et Lia dit: « Pour mon bonheur! car les filles me diront bienheureuse. » Et elle le nomma Aser.
Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.
14 Ruben sortit au temps de la moisson des blés et, ayant trouvé des mandragores dans les champs, il les apporta à Lia, sa mère. Alors Rachel dit à Lia: « Donne-moi, je te prie, des mandragores de ton fils. »
A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.”
15 Elle lui répondit: « Est-ce peu que tu aies pris mon mari, pour que tu prennes encore les mandragores de mon fils? » Et Rachel dit: « Eh bien, qu’il couche avec toi cette nuit pour les mandragores de ton fils. »
Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.”
16 Le soir, comme Jacob revenait des champs, Lia sortit à sa rencontre et lui dit: « C’est vers moi que tu viendras, car je t’ai loué pour les mandragores de mon fils. » Et il coucha avec elle cette nuit-là.
Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.
17 Dieu exauça Lia; elle conçut et enfanta à Jacob un cinquième fils;
Allah ya saurari Liyatu, ta kuwa yi ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na biyar.
18 et Lia dit: « Dieu m’a donné mon salaire, parce que j’ai donné ma servante à mon mari. » Et elle le nomma Issachar.
Sai Liyatu ta ce, “Allah ya sāka mini saboda na ba da mai hidimata ga mijina.” Saboda haka ta ba shi suna Issakar.
19 Lia conçut encore et enfanta un sixième fils à Jacob;
Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida.
20 et elle dit: « Dieu m’a fait un beau don; cette fois mon mari habitera avec moi, puisque je lui ai enfanté six fils. » Et elle le nomma Zabulon.
Sai Liyatu ta ce, “Allah ya ba ni kyauta mai daraja. A wannan lokaci mijina zai darajarta ni, domin na haifa masa’ya’ya maza shida.” Saboda haka ta ba shi suna Zebulun.
21 Elle enfanta ensuite une fille, qu’elle appela Dina.
Daga baya ta haifi’ya ta kuwa ba ta suna Dina.
22 Dieu se souvint de Rachel; il l’exauça et la rendit féconde.
Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta.
23 Elle conçut et enfanta un fils, et elle dit: « Dieu a ôté mon opprobre. »
Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.”
24 Et elle le nomma Joseph, en disant: « Que Yahweh m’ajoute encore un autre fils! »
Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”
25 Lorsque Rachel eut enfanté Joseph, Jacob dit à Laban: « Laisse-moi partir, et que je retourne chez moi, dans mon pays.
Bayan Rahila ta haifi Yusuf, sai Yaƙub ya ce wa Laban, “Ka sallame ni don in koma ƙasata.
26 Donne-moi mes femmes, ainsi que mes enfants, pour lesquels je t’ai servi, et je m’en irai, car tu sais quel service j’ai fait pour toi. »
Ba ni matana da’ya’yana, waɗanda na bauta maka dominsu, zan kuwa tafi. Ka dai san yadda na bauta maka.”
27 Laban lui dit: « Si j’ai trouvé grâce à tes yeux... J’ai observé que Yahweh m’a béni à cause de toi;
Amma Laban ya ce masa, “In na sami tagomashi daga gare ka, ina roƙonka ka zauna. Na gane ta wurin duba cewaUbangiji ya albarkace ni saboda kai.”
28 fixe-moi ton salaire, et je te le donnerai. »
Ya ƙara da cewa, “Faɗa albashinka, zan kuwa biya shi.”
29 Jacob lui dit: « Tu sais toi-même comment je t’ai servi et ce qu’est devenu ton bétail avec moi.
Yaƙub ya ce masa, “Ka dai san yadda na yi maka aiki da kuma yadda dabbobinka suka yi yawa a hannuna.
30 Car c’était peu de chose que ton bien avant moi; mais il s’est extrêmement accru, et Yahweh t’a béni sur mes pas. Maintenant quand travaillerai-je aussi pour ma maison? »
Kaɗan da kake da shi kafin zuwata ya ƙaru sosai, kuma Ubangiji ya albarkace ka a duk inda na tafi. Amma yanzu, yaushe zan yi wani abu domin gidana ni ma?”
31 Laban dit: « Que te donnerai-je? » Et Jacob dit: « Tu ne me donneras rien. Si tu m’accordes ce que je vais dire, je recommencerai à paître ton troupeau et à le garder.
Sai Laban ya yi tambaya, “Me zan ba ka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Kada ka ba ni wani abu. Amma in za ka yi mini abu guda ɗaya, zan ci gaba da kiwon garkunanka, ina kuma lura da su.
32 Je passerai aujourd’hui à travers tout ton troupeau, en mettant à part parmi les agneaux toute bête tachetée et marquetée et toute bête noire, et parmi les chèvres tout ce qui est marqueté et tacheté: ce sera mon salaire.
Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana.
33 Ma droiture témoignera pour moi demain, quand tu viendras reconnaître mon salaire. Tout ce qui ne sera pas tacheté et marqueté parmi les chèvres, et noir parmi les agneaux sera chez moi un vol.
Gaskiyata kuwa za tă zama mini shaida nan gaba, duk sa’ad da ka bincika a kan albashin da ka biya ni. Duk akuyar da take tawa da ba dabbare-dabbare ko babare-babare, ko ɗan ragon da ba baƙi ba, zai kasance sata na yi.”
34 Laban dit: « Eh bien, qu’il en soit selon ta parole. »
Sai Laban ya ce, “Na yarda. Bari yă zama yadda ka faɗa.”
35 Et le jour même, il mit à part les boucs rayés et marquetés, toutes les chèvres tachetées et marquetées, toutes celles qui avaient du blanc, et tout ce qui était noir parmi les agneaux; et il les mit entre les mains de ses fils.
A wannan rana ya ware dukan bunsurai da suke dabbare-dabbare da masu zāne-zāne, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare (duka da suke da fari-fari a jikinsu), da dukan baƙaƙen tumaki, ya sa su a hannun’ya’yansa maza.
36 Puis il mit l’espace de trois journées de chemin entre lui et Jacob. Et Jacob faisait paître le reste du troupeau de Laban.
Sa’an nan ya sa nisan tafiya kwana uku tsakaninsa da Yaƙub, yayinda Yaƙub ya ci gaba da lura da sauran garkunan Laban Yaƙub.
37 Jacob prit des baguettes vertes de peuplier, d’amandier et de platane; il y pela des bandes blanches, mettant à nu le blanc qui était sur les baguettes.
Yaƙub ya samo ɗanyen reshen itatuwan aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bar fararen cikin katakon rassan.
38 Puis il plaça les baguettes qu’il avait pelées en regard des brebis dans les rigoles, dans les abreuvoirs où les brebis venaient boire; et elles entraient en chaleur quand elles venaient boire.
Sa’an nan ya zuba ɓararre rassan cikin dukan kwamame na banruwa saboda su kasance a gaban garkunan sa’ad da suka zo shan ruwa. A sa’ad da garkunan suke barbara suka kuma zo shan ruwa,
39 Et les brebis, entrant en chaleur devant les baguettes, faisaient des petits rayés, tachetés et marquetés.
sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne.
40 Jacob mettait à part les agneaux, et il tournait la face du troupeau vers ce qui était rayé et tout ce qui était noir dans le troupeau de Laban. Il se fit ainsi des troupeaux à lui, qu’il ne joignit pas au troupeau de Laban.
Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba.
41 En outre, c’était quand les brebis vigoureuses entraient en chaleur que Jacob mettait sous les yeux des brebis les baguettes dans les abreuvoirs, afin qu’elles entrassent en chaleur près des baguettes.
A duk sa’ad da ƙarfafa dabbobi mata suke barbara, Yaƙub yakan zuba rassan a kwamame a gaban dabbobin saboda su yi barbara kusa da rassan,
42 Quand les brebis étaient chétives, il ne les mettait point, en sorte que les agneaux chétifs étaient pour Laban, et les vigoureux pour Jacob.
amma in dabbobin raunana ne, ba ya sa su a can. Saboda haka raunanan dabbobi suka zama na Laban, ƙarfafan kuma suka zama na Yaƙub.
43 Cet homme devint ainsi extrêmement riche; il eut de nombreux troupeaux, des servantes et des serviteurs, des chameaux et des ânes
Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna.