< Genèse 29 >
1 Jacob reprit sa marche et s’en alla au pays des fils de l’Orient.
Sa’an nan Yaƙub ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai ƙasar mutanen gabashi.
2 Il regarda, et voici, il y avait un puits dans la campagne, et voici, il y avait à côté trois troupeaux de brebis qui étaient couchés, car c’était à ce puits qu’on abreuvait les troupeaux, et la pierre qui était sur l’ouverture du puits était grande.
A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne.
3 Là se réunissaient tous les troupeaux; on roulait la pierre de dessus l’ouverture du puits, on faisait boire les troupeaux, et l’on remettait la pierre à sa place sur l’ouverture du puits.
Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya.
4 Jacob dit aux bergers: « Mes frères, d’où êtes-vous? » ils répondirent: « Nous sommes de Haran. »
Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?” Suka amsa, “Mu daga Haran ne.”
5 Il leur dit: « Connaissez-vous Laban, fils de Nachor? » Ils répondirent: « Nous le connaissons. »
Sai ya ce musu, “Kun san Laban, jikan Nahor?” Suka amsa, “I, mun san shi.”
6 Il leur dit: « Est-il en bonne santé? » Ils répondirent: « Il est en bonne santé, et voici Rachel, sa fille, qui vient avec les brebis. »
Sa’an nan Yaƙub ya tambaye su, “Yana nan lafiya?” Suka ce, “I, yana lafiya, ga ma’yarsa Rahila tafe da tumaki.”
7 Il dit: « Voici, il est encore grand jour, et ce n’est pas le moment de rassembler les troupeaux; abreuvez les brebis et retournez les faire paître. »
Ya ce, “Duba har yanzu da sauran rana da yawa, lokaci bai kai na tara garkuna ba. Ku shayar da tumaki ku mai da su wurin kiwo.”
8 Ils répondirent: « Nous ne le pouvons pas jusqu’à ce que tous les troupeaux soient rassemblés et qu’on roule la pierre de dessus l’ouverture du puits; alors nous abreuverons les brebis. »
Suka amsa suka ce, “Ba za mu iya ba, sai dukan garkunan sun taru, aka kuma gungurar da dutsen daga bakin rijiyar. Sa’an nan za mu shayar da tumakin.”
9 Il s’entretenait encore avec eux, lorsque Rachel arriva avec les brebis de son père; car elle était bergère.
Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce.
10 Dès que Jacob vit Rachel, fille de Laban, frère de sa mère, et les brebis de Laban, frère de sa mère, il s’approcha, roula la pierre de dessus l’ouverture du puits, et abreuva les brebis de Laban, frère de sa mère.
Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.
11 Et Jacob baisa Rachel, et il éleva la voix et pleura.
Sa’an nan Yaƙub ya sumbaci Rahila, ya kuma ɗaga murya ya yi kuka.
12 Jacob apprit à Rachel qu’il était frère de son père, qu’il était fils de Rebecca; et elle courut l’annoncer à son père.
Ya riga ya faɗa wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne kuma ɗan Rebeka. Saboda haka ta ruga da gudu ta faɗa wa mahaifinta.
13 Quand Laban eut entendu parler de Jacob, fils de sa sœur, il courut au-devant de lui, et l’ayant pris dans ses bras, il lui donna des baisers et l’amena dans sa maison. Jacob raconta à Laban toutes ces choses,
Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa.
14 et Laban lui dit: « Oui, tu es mes os et ma chair. » Et Jacob demeura avec lui un mois entier.
Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.” Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif,
15 Alors Laban dit à Jacob: « Est-ce que, parce que tu es mon frère, tu me serviras pour rien? Dis-moi quel sera ton salaire. »
sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.”
16 Or Laban avait deux filles; l’aînée se nommait Lia, et la cadette Rachel.
Laban dai yana da’ya’ya mata biyu; sunan babbar Liyatu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.
17 Lia avait les yeux malades; mais Rachel était belle de taille et belle de visage.
Liyatu tana da raunannun idanu, amma Rahila dai tsarinta yana da kyau kuma kyakkyawa ce.
18 Comme Jacob aimait Rachel, il dit: « Je te servirai sept ans pour Rachel, ta fille cadette. »
Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar’yarka Rahila.”
19 Et Laban dit: « Mieux vaut te la donner que la donner à un autre; reste avec moi. »
Laban ya ce, “Ya fi kyau in ba ka ita, da in ba wani mutum dabam. Zauna tare da ni.”
20 Et Jacob servit pour Rachel sept années, et elles furent à ses yeux comme quelques jours, parce qu’il l’aimait.
Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata.
21 Jacob dit à Laban: « Donne-moi ma femme, car mon temps est accompli, et j’irai vers elle. »
Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”
22 Laban réunit tous les gens du lieu et fit un festin;
Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki.
23 et le soir, prenant Lia, sa fille, il l’amena à Jacob, qui alla vers elle.
Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita.
24 Et Laban donna sa servante Zelpha pour servante à Lia, sa fille.
Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa’yarsa tă zama mai hidimarta.
25 Le matin venu, voilà que c’était Lia. Et Jacob dit à Laban: « Que m’as-tu fait? N’est-ce pas pour Rachel que j’ai servi chez toi? Pourquoi m’as-tu trompé? »
Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”
26 Laban répondit: « Ce n’est pas l’usage dans notre pays de donner la cadette avant l’aînée.
Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da’ya ƙarama aure kafin’yar fari.
27 Achève la semaine de celle-ci, et nous te donnerons aussi l’autre pour le service que tu feras encore chez moi pendant sept autres années. »
Ka gama makon amaryanci na’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.”
28 Jacob fit ainsi, et il acheva la semaine de Lia; puis Laban lui donna pour femme Rachel, sa fille.
Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi’yarsa Rahila tă zama matarsa.
29 Et Laban donna sa servante Bala pour servante à Rachel, sa fille.
Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta.
30 Jacob alla aussi vers Rachel et il l’aima aussi plus que Lia; il servit encore chez Laban sept autres années.
Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai.
31 Yahweh vit que Lia était haïe, et il la rendit féconde, tandis que Rachel était stérile.
Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya.
32 Lia conçut et enfanta un fils, et elle le nomma Ruben, car elle dit: « Yahweh a regardé mon affliction; maintenant mon mari m’aimera. »
Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.”
33 Elle conçut encore et enfanta un fils, et elle dit: « Yahweh a entendu que j’étais haïe, et il m’a encore donné celui-là ». Et elle le nomma Siméon.
Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.
34 Elle conçut encore et enfanta un fils, et elle dit: « Cette fois mon mari s’attachera à moi car je lui ai enfanté trois fils. » C’est pourquoi on le nomma Lévi.
Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi.
35 Elle conçut encore et enfanta un fils, et elle dit: « Cette fois je louerai Yahweh. » C’est pourquoi elle le nomma Juda. Et elle cessa d’avoir des enfants.
Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa.