< 1 Samuel 3 >

1 Le jeune Samuel servait Yahweh en la présence d’Héli. La parole de Yahweh était rare en ces jours-là, et la vision n’était pas fréquente.
Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.
2 En ce même temps, comme Héli était couché à sa place, — or ses yeux avaient commencé à se troubler et il ne pouvait plus voir;
Wata rana da dare Eli da idanunsa sun kusa makancewa har ba ya iya gani sosai yana kwance a inda ya saba.
3 la lampe de Dieu ne s’était pas encore éteinte, et Samuel était couché dans le temple de Yahweh, où était l’arche de Dieu, —
Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah.
4 Yahweh appela Samuel; il répondit: « Me voici! »
Sai Ubangiji ya kira Sama’ila. Sama’ila ya amsa ya ce, “Ga ni.”
5 Et il courut auprès d’Héli, et lui dit: « Me voici, car tu m’as appelé. » Héli répondit: « Je n’ai pas appelé; retourne te coucher. » Et il alla se coucher.
Sai ya ruga wajen Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Eli ya ce, “Ɗana ban kira ba, je ka kwanta”. Saboda haka ya tafi ya kwanta.
6 Yahweh appela de nouveau Samuel; et Samuel se leva et, étant allé auprès d’Héli, il dit: « Me voici, car tu m’as appelé. » Héli répondit: « Je n’ai pas appelé, mon fils; retourne te coucher. »
Ubangiji ya sāke kiransa ya ce, “Sama’ila!” Sama’ila ya tashi kuma ya je wurin Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”
7 Samuel ne connaissait pas encore Yahweh, car la parole de Yahweh ne lui avait pas encore été révélée.
Sama’ila dai bai riga ya san Ubangiji ba tukuna. Ba a kuma taɓa bayyana maganar Ubangiji a gare shi ba tukuna ba.
8 Yahweh appela de nouveau Samuel pour la troisième fois. Il se leva et, étant allé auprès d’Héli, il dit: « Me voici, car tu m’as appelé. » Héli comprit alors que c’était Yahweh qui appelait l’enfant.
Ubangiji ya kira Sama’ila sau na uku, Sama’ila kuma ya tashi ya tafi wurin Eli, “Ga ni, gama ka kira ni.” Sai Eli ya gane cewa Ubangiji ne ke kira yaron.
9 Et Héli dit à Samuel: « Va, couche-toi, et si l’on t’appelle encore, tu diras: Parlez, Yahweh, car votre serviteur écoute. » Et Samuel s’en alla et se coucha à sa place.
Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa.
10 Yahweh vint et se tint là, et il appela comme les autres fois: « Samuel! Samuel! » Samuel répondit: « Parlez, car votre serviteur écoute. »
Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya. Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.”
11 Et Yahweh dit à Samuel: « Voici que je vais faire dans Israël une chose que personne n’entendra sans que les deux oreilles lui tintent.
Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Duba ina dab da yin wani abu a Isra’ila da zai sa kunne kowa da yake ji, yă ji tsoro.
12 En ce jour-là j’accomplirai sur Héli tout ce que j’ai prononcé touchant sa maison; je commencerai et j’achèverai.
A ranar zan cika dukan maganar da na yi game da Eli da iyalinsa, daga farko har ƙarshe.
13 Je lui ai déclaré que j’allais juger sa maison pour jamais, à cause du crime dont il avait connaissance, et par lequel ses fils se sont rendus indignes sans qu’il les ait réprimés.
Gama na gaya masa zan hukunta gidansa har abada saboda zunubin da yake sane da shi;’ya’yansa sun wulaƙantar da kansu, shi kuma bai tsawata musu ba.
14 C’est pourquoi j’ai juré à la maison d’Héli que jamais le crime de la maison d’Héli ne sera expié, ni par des sacrifices ni par des oblations. »
Saboda haka na rantse a kan gidan Eli, ‘Ba za a taɓa shafe laifin gidan Eli da hadaya ko baiko ba.’”
15 Samuel resta couché jusqu’au matin, puis il ouvrit les portes de la maison de Yahweh. Et Samuel craignait de raconter la vision à Héli.
Sama’ila kuwa ya kwanta har safe, sa’an nan ya buɗe ƙofofin gidan Ubangiji. Ya ji tsoro yă gaya wa Eli wahayin,
16 Mais Héli appela Samuel, en disant: « Samuel, mon fils! » Il répondit: « Me voici. »
amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.” Sama’ila ya ce, “Ga ni.”
17 Et Héli dit: « Quelle est la parole que Yahweh t’a dite? Je te prie, ne me cache rien. Que Yahweh te traite dans toute sa rigueur si tu me caches quelque chose de toute la parole qu’il t’a dite! »
Eli ya ce, mene ne ya ce maka? Kada ka ɓoye mini. Allah ya yi da kai har ma fiye in ka ɓoye mini kome da ya ce maka.
18 Samuel lui raconta toutes les paroles sans lui rien cacher. Et Héli dit: « C’est Yahweh; ce qui lui semblera bon, qu’il le fasse! »
Don haka sai Sama’ila ya gaya masa kome bai ɓoye masa kome ba. Sa’an nan Eli ya ce, “Shi ne Ubangiji bari yă yi abin da ya yi kyau a gare shi.”
19 Samuel devint grand; Yahweh était avec lui, et il ne laissa tomber à terre aucune de ses paroles.
Ubangiji kuwa yana tare da Sama’ila har girmansa bai kuma bar ko ɗaya daga maganarsa ta kāsa cika ba.
20 Tout Israël, depuis Dan jusqu’à Bersabée, reconnut que Samuel était un vrai prophète de Yahweh.
Dukan Isra’ila daga Dan har Beyersheba suka shaida amincin Sama’ila annabi ne na Ubangiji.
21 Et Yahweh continuait d’apparaître à Silo, car Yahweh se manifestait à Samuel, à Silo, par la parole de Yahweh.
Ubangiji kuwa ya dinga bayyana a Shilo, a nan ya bayyana kansa ga Sama’ila ta wurin maganarsa.

< 1 Samuel 3 >