< Esther 6 >

1 Cette nuit-là, le roi ne pouvait pas dormir. Il ordonna qu'on apporte le livre des chroniques, et on les lut au roi.
A daren nan, sarki bai iya barci ba, saboda haka ya ba da umarni a kawo, a kuma karanta masa littafin tarihi na shekara-shekara, da rubutaccen labarin mulkinsa.
2 On y trouva écrit que Mardochée avait raconté que Bigthana et Teresh, deux des eunuques du roi, qui étaient portiers, avaient essayé de porter la main sur le roi Assuérus.
Aka tarar, a rubuce a ciki, cewa Mordekai ya tone ƙulle-ƙullen Bigtana da Teresh, biyu daga hafsoshin sarki, waɗanda suke tsaron mashigin ƙofa, waɗanda suka ƙulla su kashe Sarki Zerzes.
3 Le roi dit: « Quel honneur et quelle dignité a-t-on donné à Mardochée pour cela? » Les serviteurs du roi qui l'assistaient dirent: « On n'a rien fait pour lui. »
Sarki ya ce, “Wace girma da daraja ce aka ba wa Mordekai saboda wannan?” Masu hidimarsa suka ce, “Ba a yi masa wani abu ba.”
4 Le roi dit: « Qui est dans la cour? » Haman était entré dans la cour extérieure de la maison du roi, pour parler au roi de faire pendre Mardochée à la potence qu'il avait préparée pour lui.
Sarki ya ce, “Wa yake a haraba?” Daidai lokacin kuwa Haman ya shigo harabar waje na fada don yă yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a wurin rataye mai laifin da ya shirya.
5 Les serviteurs du roi lui dirent: « Voici Haman qui se tient dans la cour. » Le roi dit: « Qu'il entre. »
Masu yi wa sarki hidima, suka amsa, “Haman yana tsaye a haraba.” Sarki ya umarta, “A kawo shi ciki.”
6 Haman entra donc. Le roi lui dit: « Que fera-t-on à l'homme que le roi se plaît à honorer? » Haman disait en son for intérieur: « Qui le roi prendrait-il plaisir à honorer plus que moi? ».
Sa’an nan Haman ya shigo, sai sarki ya ce masa, “Me ya kamata a yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama?” Haman dai ya yi tunani a ransa ya ce, “Wane ne sarki zai girmama in ba ni ba?”
7 Haman dit au roi: « Pour l'homme que le roi veut honorer,
Sai ya amsa wa sarki cewa, “Saboda mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama,
8 que l'on apporte les vêtements royaux dont le roi se sert pour se vêtir, et le cheval que le roi monte et sur la tête duquel est posée une couronne royale.
bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai.
9 Que les vêtements et le cheval soient remis à l'un des princes les plus nobles du roi, afin qu'il en revête l'homme que le roi veut honorer, qu'il le fasse monter à cheval sur la place de la ville et qu'il proclame devant lui: « C'est ainsi qu'il sera fait à l'homme que le roi veut honorer ».
Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’”
10 Alors le roi dit à Haman: « Dépêche-toi de prendre les vêtements et le cheval, comme tu l'as dit, et fais-le pour Mardochée, le Juif, qui est assis à la porte du roi. Que rien ne manque à tout ce que tu as dit. »
Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”
11 Alors Haman prit les vêtements et le cheval, habilla Mardochée, le fit monter sur la place de la ville et proclama devant lui: « C'est ainsi qu'il sera fait à l'homme que le roi se plaît à honorer! »
Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!”
12 Mardochée revint à la porte du roi, mais Haman se précipita dans sa maison, en deuil et la tête couverte.
Daga baya, Mordekai ya dawo zuwa ƙofar sarki. Amma Haman ya ruga gida, kansa a rufe, saboda baƙin ciki.
13 Haman raconta à Zéresh, sa femme, et à tous ses amis tout ce qui lui était arrivé. Ses sages et Zéresh, sa femme, lui dirent alors: « Si Mardochée, devant lequel tu as commencé à tomber, est d'origine juive, tu ne prévaudras pas contre lui, mais tu tomberas certainement devant lui. »
Ya je ya faɗa wa matarsa Zeresh, da dukan abokansa, me ya same shi. Masu ba shi shawara, da matarsa Zeresh, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara fāɗuwa a gabansa, daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, tabbatacce za ka fāɗi a gabansa!”
14 Pendant qu'ils discutaient encore avec lui, les eunuques du roi arrivèrent et s'empressèrent d'amener Haman au banquet qu'Esther avait préparé.
Suna cikin magana da shi ke nan, sai ga bābānnin sarki, suka iso suka kuma hanzarta da Haman zuwa liyafar da Esta ta shirya.

< Esther 6 >