< Amos 7 >

1 Ainsi m'a montré le Seigneur Yahvé: voici, il a formé des sauterelles au commencement de la germination de l'arrière-cour; et voici, c'était l'arrière-cour après la moisson du roi.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa.
2 Quand elles eurent fini de manger l'herbe du pays, je dis: « Seigneur Yahvé, pardonne, je t'en supplie! Comment Jacob pourrait-il tenir debout? Car il est petit. »
Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
3 Yahvé s'est incliné à ce sujet. « Cela n'arrivera pas », dit Yahvé.
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji.
4 Ainsi m'a montré le Seigneur Yahvé: voici, le Seigneur Yahvé a appelé le jugement par le feu, et il a asséché le grand abîme, et il aurait dévoré le pays.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa.
5 Alors je dis: « Seigneur Yahvé, arrête, je t'en supplie! Comment Jacob pourrait-il tenir debout? Car il est petit. »
Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
6 Yahvé s'est incliné à ce sujet. « Cela non plus n'arrivera pas », dit le Seigneur Yahvé.
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
7 Il me montra ainsi: voici, l'Éternel se tenait près d'un mur tracé au fil à plomb, un fil à plomb à la main.
Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa.
8 Yahvé me dit: « Amos, que vois-tu? » J'ai dit: « Un fil à plomb. » L'Éternel dit alors: « Voici que je vais placer un fil à plomb au milieu de mon peuple d'Israël. Je ne passerai plus devant eux.
Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?” Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba.
9 Les hauts lieux d'Isaac seront désolés, les sanctuaires d'Israël seront dévastés, et je me lèverai par l'épée contre la maison de Jéroboam. »
“Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango; da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.”
10 Alors Amatsia, prêtre de Béthel, envoya à Jéroboam, roi d'Israël, pour lui dire: « Amos a conspiré contre toi au milieu de la maison d'Israël. Le pays n'est pas capable de supporter toutes ses paroles.
Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba.
11 Car Amos dit: « Jéroboam mourra par l'épée, et Israël sera emmené captif hors de son pays ».
Gama ga abin da Amos yake cewa, “‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi, kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’”
12 Amatsia dit aussi à Amos: « Voyant, va, fuis dans le pays de Juda, et là, mange du pain, et prophétise là,
Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can.
13 mais ne prophétise plus à Béthel, car c'est le sanctuaire du roi, et c'est une maison royale! ».
Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”
14 Amos répondit à Amatsia: Je n'étais pas prophète, et je n'étais pas fils de prophète, mais j'étais berger et cultivateur de figues de Barbarie.
Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul.
15 L'Éternel m'a enlevé de la suite du troupeau, et l'Éternel m'a dit: Va, prophétise à mon peuple d'Israël.
Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’
16 Maintenant, écoute la parole de l'Éternel: « Tu dis: Ne prophétise pas contre Israël, et ne prêche pas contre la maison d'Isaac ».
Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce, “‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila, kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
17 C'est pourquoi Yahvé dit: 'Ta femme se prostituera dans la ville, tes fils et tes filles tomberont par l'épée, ton pays sera divisé au cordeau, tu mourras toi-même dans un pays impur, et Israël sera emmené captif hors de son pays.'"
“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’”

< Amos 7 >