< Jeremiah 14 >
1 That which hath been the word of Jehovah unto Jeremiah concerning the matters of the dearths:
Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa,
2 Mourned hath Judah, and her gates have languished, They have mourned to the earth, And the cry of Jerusalem hath gone up.
“Yahuda tana makoki biranenta suna fama; suna kuka saboda ƙasar, kuka kuma tana tasowa daga Urushalima.
3 And their honourable ones have sent their little ones to the water, They have come unto ditches, They have not found water, They have turned back — their vessels empty! They have been ashamed, And have blushed and covered their head.
Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa a maɓulɓulai amma babu ruwa. Suka dawo da tulunansu haka nan; da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe.
4 Because the ground hath been broken, For there hath been no rain in the land, Ashamed have been husbandmen, They have covered their head.
Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu.
5 For even the hind in the field hath brought forth — to forsake [it!] For there hath been no grass.
Har barewa a kurmi ma ta gudu ta bar’ya’yan da ta haihu sababbi saboda babu ciyawa.
6 And wild asses have stood on high places, They have swallowed up wind like dragons, Consumed have been their eyes, for there is no herb.
Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai suna haki kamar diloli; idanunsu sun kāsa gani saboda rashin makiyaya.”
7 Surely our iniquities have testified against us, O Jehovah, work for Thy name's sake, For many have been our backslidings, Against Thee we have sinned.
Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu, Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka. Gama jan bayanmu ya yi yawa; mun yi maka zunubi.
8 O Hope of Israel — its saviour in time of trouble, Why art Thou as a sojourner in the land? And as a traveller turned aside to lodge?
Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila, Mai Cetonsa a lokutan wahala, me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar, kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce?
9 Why art Thou as one dumb? As a mighty one not able to save? And Thou [art] in our midst, O Jehovah, And Thy name over us is called, leave us not.
Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato, kamar jarumi marar ƙarfin ceto? Kana a cikinmu, ya Ubangiji, da sunanka ake kiranmu; kada ka yashe mu!
10 Thus said Jehovah concerning this people: Well they have loved to wander, Their feet they have not restrained, And Jehovah hath not accepted them, Now doth He remember their iniquity, And inspect their sin.
Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane, “Suna son yawace-yawace ƙwarai; ba sa hana ƙafafunsu yawo. Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba; yanzu zai tuna da muguntarsu zai kuma hukunta su saboda zunubansu.”
11 And Jehovah saith unto me: Thou dost not pray for this people for good,
Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan.
12 When they fast, I hearken not unto their cry, And when they cause to ascend burnt-offering and present, I accept them not, For by sword, and by famine, And by pestilence, I am consuming them.
Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.”
13 And I say, 'Ah, Lord Jehovah, Lo, the prophets are saying to them: Ye do not see a sword, yea, famine is not to you, For true peace I give to you in this place.'
Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’”
14 And Jehovah saith unto me: Falsehood the prophets are prophesying in My name, I did not send them, nor command them, Nor have I spoken unto them: A false vision, and divination, and vanity, And the deceit of their own heart, they are prophesying to you.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne.
15 Therefore, thus said Jehovah concerning the prophets who are prophesying in My name, and I have not sent them, and they are saying, Sword and famine is not in this land: By sword and by famine are these prophets consumed.
Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su.
16 And the people to whom they are prophesying, Are cast into out-places of Jerusalem, Because of the famine, and of the sword, And they have none burying them, Them, their wives, and their sons, and their daughters, And I have poured out upon them this evil.
Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su.
17 And thou hast said unto them this word: Tears come down mine eyes night and day, And they do not cease, For, [with] a great breach, Broken hath been the virgin daughter of my people, A very grievous stroke.
“Ka yi musu wannan magana, “‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa.
18 If I have gone forth to the field, Then, lo, the pierced of the sword! And if I have entered the city, Then, lo, the diseased of famine! For both prophet and priest have gone up and down Unto a land that they knew not.
In na shiga cikin ƙasar, na ga waɗanda takobi ya kashe; in na shiga cikin birni, na ga waɗanda suke fama da yunwa. Da Annabi da firist duk sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’”
19 Hast Thou utterly rejected Judah? Zion hath Thy soul loathed? Wherefore hast Thou smitten us, And there is no healing to us? Looking for peace, and there is no good, And for a time of healing, and lo, terror.
Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan? Kana ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu don kada mu warke? Mun sa zuciya ga salama babu abin alherin da ya zo, mun sa rai ga lokacin warkarwa amma sai ga razana.
20 We have known, O Jehovah, our wickedness, The iniquity of our fathers, For we have sinned against Thee.
Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu da kuma laifin kakanninmu; tabbatacce mun yi maka zunubi.
21 Do not despise, for Thy name's sake, Dishonour not the throne of Thine honour, Remember, break not Thy covenant with us.
Saboda sunanka kada ka ƙi mu; kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka. Ka tuna da alkawarinka da mu kada ka tā da shi.
22 Are there among the vanities of the nations any causing rain? And do the heavens give showers? Art not Thou He, O Jehovah our God? And we wait for thee, for Thou — Thou hast done all these!
Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama? Sararin sama kansu sukan yi yayyafi? A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu. Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka, gama kai ne kake yi wannan duka.