< Exodus 8 >

1 And Jehovah saith unto Moses, 'Go in unto Pharaoh: and thou hast said unto him, Thus said Jehovah, Send My people away, and they serve Me;
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.
2 and if thou art refusing to send away, lo, I am smiting all thy border with frogs;
In ka ƙi barinsu, zan hore ka da annoban kwaɗi a dukan ƙasarka.
3 and the River hath teemed [with] frogs, and they have gone up and gone into thy house, and into the inner-chamber of thy bed, and on thy couch, and into the house of thy servants, and among thy people, and into thine ovens, and into thy kneading-troughs;
Nilu zai cika da kwaɗi. Za su haura zuwa cikin fadanka da kan gadonka, cikin gidajen bayinka da kan mutanenka, cikin kwanonin toye-toyenka da na cin abincinka.
4 yea, on thee, and on thy people, and on all thy servants do the frogs go up.'
Kwaɗin nan za su yi ta tsalle a kanka, da kan mutanenka, da kuma kan dukan bayinka.’”
5 And Jehovah saith unto Moses, 'Say unto Aaron, Stretch out thy hand, with thy rod, against the streams, against the rivers, and against the ponds, and cause the frogs to come up against the land of Egypt.'
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandanka bisa koguna da rafuffuka da kuma kududdufai, ka sa kwaɗi su fito su mamaye ƙasar Masar.’”
6 And Aaron stretcheth out his hand against the waters of Egypt, and the frog cometh up, and covereth the land of Egypt;
Sai Haruna ya miƙa hannunsa bisa ruwan Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka mamaye ƙasar Masar.
7 and the scribes do so with their flashings, and cause the frogs to come up against the land of Egypt.
Amma bokaye ma suka yi abubuwan nan ta wurin sihirinsu; suka sa kwaɗi suka fito suka mamaye ƙasar Masar.
8 And Pharaoh calleth for Moses and for Aaron, and saith, 'Make supplication unto Jehovah, that he turn aside the frogs from me, and from my people, and I send the people away, and they sacrifice to Jehovah.'
Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Yi addu’a ga Ubangiji yă ɗauke kwaɗi daga gare ni da mutanena, zan kuwa bar mutanenku su tafi su yi hadaya ga Ubangiji.”
9 And Moses saith to Pharaoh, 'Beautify thyself over me; when do I make supplication for thee, and for thy servants, and for thy people, to cut off the frogs from thee and from thy houses — only in the River they do remain?'
Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.”
10 and he saith, 'To-morrow.' And he saith, According to thy word [it is], so that thou knowest that there is none like Jehovah our God,
Fir’auna ya ce, “Gobe.” Musa ya amsa, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani kamar Ubangiji, Allahnmu.
11 and the frogs have turned aside from thee, and from thy houses, and from thy servants, and from thy people; only in the River they do remain.'
Kwaɗin za su bar ka da gidajenka, bayinka da mutanenka; za su kasance a Nilu ne kaɗai.”
12 And Moses — Aaron also — goeth out from Pharaoh, and Moses crieth unto Jehovah, concerning the matter of the frogs which He hath set on Pharaoh;
Bayan Musa da Haruna sun bar Fir’auna, Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji saboda kwaɗin da ya kawo a bisa Fir’auna.
13 and Jehovah doth according to the word of Moses, and the frogs die out of the houses, out of the courts, and out of the fields,
Sai Ubangiji ya yi abin da Musa ya nema. Kwaɗin suka mutu a gidaje, da filaye, da kuma gonaki.
14 and they heap them up together, and the land stinketh.
Aka jibga su tsibi-tsibi, ƙasar ta yi ɗoyi saboda su.
15 And Pharaoh seeth that there hath been a respite, and he hath hardened his heart, and hath not hearkened unto them, as Jehovah hath spoken.
Amma da Fir’auna ya ga an sami sauƙi, sai ya taurare, ya ƙi yă saurari Musa da Haruna kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
16 And Jehovah saith unto Moses, 'Say unto Aaron, Stretch out thy rod, and smite the dust of the land, and it hath become gnats in all the land of Egypt.'
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Miƙa hannunka ka bugi ƙurar ƙasa,’ dukan ƙurar ƙasar Masar kuwa za tă zama ƙwari masu cizo.”
17 And they do so, and Aaron stretcheth out his hand with his rod, and smiteth the dust of the land, and the gnats are on man and on beast; all the dust of the land hath been gnats in all the land of Egypt.
Suka yi haka, da Haruna ya miƙa hannunsa da sandan, ya bugi ƙurar ƙasa, sai ƙwari masu cizo suka fito a kan mutane da dabbobi. Dukan ƙurar, ko’ina a ƙasar Masar ta zama cinnaku.
18 And the scribes do so with their flashings, to bring out the gnats, and they have not been able, and the gnats are on man and on beast;
Sa’ad da bokayen Fir’auna suka yi ƙoƙari yin sihiri iri na rufe ido domin su fito da kwari, sai suka kāsa. Ƙwari masu cizo kuwa suka rufe mutane da dabbobi.
19 and the scribes say unto Pharaoh, 'It [is] the finger of God;' and the heart of Pharaoh is strong, and he hath not hearkened unto them, as Jehovah hath spoken.
Sai bokaye suka ce wa Fir’auna, “Wannan fa da hannun Allah a ciki.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
20 And Jehovah saith unto Moses, 'Rise early in the morning, and station thyself before Pharaoh, lo, he is going out to the waters, and thou hast said unto him, Thus said Jehovah, Send My people away, and they serve Me;
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada.
21 for, if thou art not sending My people away, lo, I am sending against thee, and against thy servants, and against thy people, and against thy houses, the beetle, and the houses of the Egyptians have been full of the beetle, and also the ground on which they are.
In ba ka bar mutanena suka tafi ba, zan turo da tarin ƙuda a kanka da bayinka, a kan mutanenka da cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da ƙudaje, har ma da ƙasa inda za su taka.
22 'And I have separated in that day the land of Goshen, in which My people are staying, that the beetle is not there, so that thou knowest that I [am] Jehovah in the midst of the land,
“‘Amma zan keɓe yankin Goshen, inda mutanena suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, domin ka sani cewa Ni, Ubangiji, ina cikin wannan ƙasa.
23 and I have put a division between My people and thy people: to-morrow is this sign.'
Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za tă auku.’”
24 And Jehovah doth so, and the grievous beetle entereth the house of Pharaoh, and the house of his servants, and in all the land of Egypt the land is corrupted from the presence of the beetle.
Ubangiji kuwa ya yi haka. Tarin ƙuda suka zubo a fadar Fir’auna da cikin gidajen bayinsa, da ko’ina a Masar, ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.
25 And Pharaoh calleth unto Moses and to Aaron, and saith, 'Go, sacrifice to your God in the land;'
Sai Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku miƙa hadaya ga Allahnku, a nan a cikin ƙasar.”
26 and Moses saith, 'Not right to do so, for the abomination of the Egyptians we do sacrifice to Jehovah our God; lo, we sacrifice the abomination of the Egyptians before their eyes — and they do not stone us!
Amma Musa ya ce, “Wannan ba zai yiwu ba. Hadayun da mukan miƙa wa Ubangiji, Allahnmu haram ne ga Masarawa. In kuwa muka miƙa hadayun da suke haram a idanunsu, ba za su jajjefe mu ba?
27 A journey of three days we go into the wilderness, and have sacrificed to Jehovah our God, as He saith unto us.'
Dole mu yi tafiya kwana uku cikin hamada domin miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnmu, yadda ya umarce mu.”
28 And Pharaoh saith, 'I send you away, and ye have sacrificed to Jehovah your God in the wilderness, only go not very far off; make ye supplication for me;'
Fir’auna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, don ku miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnku, a cikin hamada, amma ba za ku tafi da nisa ba. Yanzu ku yi mini addu’a.”
29 and Moses saith, 'Lo, I am going out from thee, and have made supplication unto Jehovah, and the beetle hath turned aside from Pharaoh, from his servants, and from his people — to-morrow, only let not Pharaoh add to deceive — in not sending the people away to sacrifice to Jehovah.'
Musa ya amsa, “Da zarar na bar ka, zan yi addu’a ga Ubangiji, gobe kuwa ƙudaje za su bar Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa. Sai dai a tabbata Fir’auna bai sāke yin ruɗi ta wurin ƙin barin mutane su tafi su miƙa hadayu ga Ubangiji ba.”
30 And Moses goeth out from Pharaoh, and maketh supplication unto Jehovah,
Sa’an nan Musa ya rabu da Fir’auna, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,
31 and Jehovah doth according to the word of Moses, and turneth aside the beetle from Pharaoh, from his servants, and from his people — there hath not been left one;
Ubangiji kuwa ya yi abin da Musa ya roƙa. Ƙudaje suka rabu da Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa; ba ƙudan da ya rage.
32 and Pharaoh hardeneth his heart also at this time, and hath not sent the people away.
Amma a wannan lokaci ma, Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai kuma bar mutanen suka tafi ba.

< Exodus 8 >