< Exodus 27 >

1 'And thou hast made the altar of shittim wood, five cubits the length, and five cubits the breadth — the altar is square — and three cubits its height.
“Ka gina bagade da itacen ƙirya, mai tsawo kamu uku, zai zama murabba’i, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kuma kamu biyar.
2 And thou hast made its horns on its four corners, its horns are of the same, and thou hast overlaid it [with] brass.
Ka yi masa ƙaho a kowace kusurwan nan huɗu, domin bagade da ƙahoni duk su zama ɗaya, ka dalaye bagade da tagulla.
3 And thou hast made its pots to remove its ashes, and its shovels, and its bowls, and its forks, and its fire-pans, even all its vessels thou dost make of brass.
Ka yi duk kayan aikinsa da tagulla, tukwanensa na ɗiban toka, da manyan cokula, da kwanonin yayyafawa, da cokula masu yatsotsi don nama da kuma farantai domin wuta.
4 'And thou hast made for it a grate of net-work of brass, and hast made on the net four rings of brass on its four extremities,
Ka yi raga na tagulla dominsa, ka kuma yi zoben tagulla a kowace kusurwan nan huɗu na bagaden.
5 and hast put it under the compass of the altar beneath, and the net hath been unto the middle of the altar.
Ka sa ragar a ƙarƙashin bagade domin tă kai tsakiyar bagade.
6 'And thou hast made staves for the altar, staves of shittim wood, and hast overlaid them [with] brass.
Ka yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da tagulla.
7 And the staves have been brought into the rings, and the staves have been on the two sides of the altar in bearing it.
Za a zura sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefe biyu na bagade a lokacin da ake ɗaukarsa.
8 Hollow with boards thou dost make it, as it hath been shewed thee in the mount, so do they make [it].
Ka yi bagaden da katakai, sa’an nan ka robe cikinsa. Ka yi shi bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.
9 'And thou hast made the court of the tabernacle: for the south side southward, hangings for the court of twined linen, a hundred by the cubit [is] the length for the one side,
“Ka yi fili domin tabanakul. Tsawon gefen kudu zai zama kamu ɗari da labulen da aka yi da zaren lili mai kyau,
10 and its twenty pillars and their twenty sockets [are] of brass, the pegs of the pillars and their fillets [are] of silver;
da katakai ashirin da rammukan tagulla ashirin da ƙugiyoyin azurfa da kuma rammuka a kan katakai.
11 and so for the north side in length, hangings of a hundred [cubits] in length, and its twenty pillars and their twenty sockets [are] of brass, the pegs of the pillars and their fillets [are] of silver.
A wajen arewa shi ma, tsawon yă zama ƙafa ɗari. Ka kama labulen da ƙugiyoyin da aka yi da azurfa waɗanda aka manna a kan ƙarfen da aka dalaye da azurfa.
12 'And [for] the breadth of the court at the west side [are] hangings of fifty cubits, their pillars ten, and their sockets ten.
“Faɗin ƙarshen filin a yamma zai zama kamu hamsin. A kuma sa labule tare da rammuka goma da kuma katakai goma.
13 And [for] the breadth of the court at the east side, eastward, [are] fifty cubits.
A wajen gabas can ƙarshe, wajen fitowar rana, fāɗin filin zai zama kamu hamsin.
14 And the hangings at the side [are] fifteen cubits, their pillars three, and their sockets three.
Tsayin labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku,
15 And at the second side [are] hangings fifteen [cubits], their pillars three, and their sockets three.
haka kuma tsayin labule na wancan gefen, zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku.
16 'And for the gate of the court a covering of twenty cubits, blue, and purple, and scarlet, and twined linen, work of an embroiderer; their pillars four, their sockets four.
“Domin ƙofar tentin, a saƙa labule mai tsayin kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai ruwan shuɗi, da shunayya, da jan zare, mai aikin gwani, da katakai huɗu tare da rammukansu huɗu.
17 All the pillars of the court round about [are] filleted [with] silver, their pegs [are] silver, and their sockets brass.
Duk katakan da suke kewaye da filin, za a yi musu maɗaurai na azurfa da kuma ƙugiyoyi, da rammukan tagulla.
18 'The length of the court [is] a hundred by the cubit, and the breadth fifty by fifty, and the height five cubits, of twined linen, and their sockets [are] brass,
Tsayin filin zai zama kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu hamsin, tsayin labulensa na lallausan zaren lilin zai zama kamu biyar, a kuma yi rammukansa da tagulla.
19 even all the vessels of the tabernacle, in all its service, and all its pins, and all the pins of the court, [are] brass.
Dukan sauran kayan da aka yi amfani da su a aikin wannan tabanakul, ko da wanda irin aiki ne za a yi da su, har da dukan dogayen turakunsa da na filin, za a yi su da tagulla ne.
20 'And thou — thou dost command the sons of Israel, and they bring unto thee pure beaten olive oil for the light, to cause the lamp to go up continually;
“Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai, tatacce daga zaitun domin fitilu, saboda fitilun su yi ta ci a koyaushe.
21 in the tent of meeting, at the outside of the vail, which [is] over the testimony, doth Aaron — his sons also — arrange it from evening till morning before Jehovah — a statute age-during to their generations, from the sons of Israel.
A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa.

< Exodus 27 >