< Deuteronomy 6 >
1 'And this [is] the command, the statutes and the judgments which Jehovah your God hath commanded to teach you, to do in the land which ye are passing over thither to possess it,
Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka,
2 so that thou dost fear Jehovah thy God, to keep all His statutes and His commands, which I am commanding thee, thou, and thy son, and thy son's son, all days of thy life, and so that thy days are prolonged.
saboda ku,’ya’yanku, da kuma’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai.
3 'And thou hast heard, O Israel, and observed to do, that it may be well with thee, and that thou mayest multiply exceedingly, as Jehovah, God of thy fathers, hath spoken to thee, [in] the land flowing with milk and honey.
Ku ji, ya Isra’ila, ku kuma kula, ku kiyaye su don yă zama muku da lafiya, ku kuma ƙaru sosai a ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji, Allahn kakanninku ya yi muku alkawari.
4 'Hear, O Israel, Jehovah our God [is] one Jehovah;
Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.
5 and thou hast loved Jehovah thy God with all thy heart, and with all thy soul, and with all thy might,
Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku.
6 and these words which I am commanding thee to-day have been on thine heart,
Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku.
7 and thou hast repeated them to thy sons, and spoken of them in thy sitting in thine house, and in thy walking in the way, and in thy lying down, and in thy rising up,
Ku koya wa’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
8 and hast bound them for a sign upon thy hand, and they have been for frontlets between thine eyes,
Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku.
9 and thou hast written them on door-posts of thy house, and on thy gates.
Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
10 'And it hath been, when Jehovah thy God doth bring thee in unto the land which He hath sworn to thy fathers, to Abraham, to Isaac, and to Jacob, to give to thee — cities great and good, which thou hast not built,
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya rantse ga kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, yă ba ku, ƙasa mai girma, mai manyan biranen da ba ku kuka gina ba,
11 and houses full of all good things which thou hast not filled, and wells digged which thou hast not digged, vineyards and olive-yards which thou hast not planted, and thou hast eaten, and been satisfied;
gidaje cike da kowane irin abubuwa masu kyau, da ba ku kuka tanadar ba, rijiyoyin da ba ku kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun da ba ku kuka shuka ba, sa’ad da kuwa kuka ci, kuka kuma ƙoshi,
12 'Take heed to thyself lest thou forget Jehovah who hath brought thee out of the land of Egypt, out of a house of servants;
ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar, da gidan bauta ba.
13 Jehovah thy God thou dost fear, and Him thou dost serve, and by His name thou dost swear;
Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa.
14 ye do not go after other gods, of the gods of the peoples who [are] round about you;
Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku;
15 for a zealous God [is] Jehovah thy God in thy midst — lest the anger of Jehovah thy God burn against thee, and He hath destroyed thee from off the face of the ground.
gama Ubangiji Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar.
16 'Ye do not try Jehovah your God as ye tried in Massah;
Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Massa.
17 ye do diligently keep the commands of Jehovah your God, and His testimonies, and His statutes which He hath commanded thee,
Ku tabbata kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa da kuma ƙa’idodinsa da ya ba ku.
18 and thou hast done that which is right and good in the eyes of Jehovah, so that it is well with thee, and thou hast gone in and possessed the good land which Jehovah hath sworn to thy fathers,
Ku aikata abin da yake daidai da kuma mai kyau a idon Ubangiji, don yă zama muka da lafiya, ku kuwa shiga ku mallaki ƙasa mai kyau da Ubangiji ya yi alkawari da rantsuwa ga kakanninku.
19 to drive away all thine enemies from thy presence, as Jehovah hath spoken.
Zai kuwa korin dukan abokan gābanku da suke gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa.
20 'When thy son asketh thee hereafter, saying, What [are] the testimonies, and the statutes, and the judgments, which Jehovah our God hath commanded you?
Nan gaba, sa’ad da’ya’yanku suka tambaye ku, “Mene ne ma’anar farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnmu ya umarce ku?”
21 then thou hast said to thy son, Servants we have been to Pharaoh in Egypt, and Jehovah bringeth us out of Egypt by a high hand;
Sai ku gaya musu, “Dā mu bayin Fir’auna ne a Masar, amma Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu masu ƙarfi.
22 and Jehovah giveth signs and wonders, great and sad, on Egypt, on Pharaoh, and on all his house, before our eyes;
A idanunmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da al’ajabai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da kuma dukan gidansa.
23 and us He hath brought out thence, in order to bring us in, to give to us the land which He had sworn to our fathers.
Amma ya fitar da mu daga can domin yă kawo mu cikin ƙasar da ya yi wa kakanninmu alkawari tare da rantsuwa zai ba mu.
24 And Jehovah commandeth us to do all these statutes, to fear Jehovah our God, for good to ourselves all the days, to keep us alive, as [at] this day;
Ubangiji ya umarce mu mu yi biyayya da dukan waɗannan ƙa’idodi, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu, saboda kullum mu ci gaba, a kuma bar mu da rai, kamar yadda yake a yau.
25 and righteousness it is for us, when we observe to do all this command before Jehovah our God, as He hath commanded us.
In kuma muka kula, muka kiyaye dukan dokokin nan a gaban Ubangiji Allahnmu, kamar yadda ya umarce mu, wannan zai zama adalci a gare mu.”