< Psalms 136 >

1 Alleluya. Knouleche ye to the Lord, for he is good, for his merci is withouten ende.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.
2 Knouleche ye to the God of goddis.
Ku yi godiya ga Allahn alloli.
3 Knouleche ye to the Lord of lordis.
Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji.
4 Which aloone makith grete merueils.
Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki,
5 Which made heuenes bi vndurstondyng.
Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai,
6 Which made stidefast erthe on watris.
Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye,
7 Which made grete liytis.
Wanda ya yi manyan haskoki,
8 The sunne in to the power of the dai.
Rana don tă yi mulkin yini,
9 The moone and sterris in to the power of the niyt.
Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare;
10 Which smoot Egipt with the firste gendrid thingis of hem.
Gare shi wanda ya kashe’ya’yan fari Masar
11 Which ledde out Israel fro the myddil of hem.
Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu
12 In a miyti hond and in an hiy arm.
Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko;
13 Whiche departide the reed see in to departyngis.
Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu
14 And ledde out Israel thoruy the myddil therof.
Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa,
15 And he `caste a down Farao and his pouer in the reed see.
Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku;
16 Which ledde ouer his puple thoruy desert.
Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada,
17 Which smoot grete kingis.
Wanda ya buge manyan sarakuna,
18 And killide strong kingis.
Ya karkashe manyan sarakuna,
19 Seon, the king of Amorreis.
Sihon sarkin Amoriyawa
20 And Og, the king of Baasan.
Da kuma Og sarkin Bashan,
21 And he yaf the lond of hem eritage.
Ya kuma ba da ƙasarsu gādo,
22 Eritage to Israel, his seruaunt.
Gādo ga bawansa Isra’ila;
23 For in oure lownesse he hadde mynde on vs.
Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu
24 And he ayenbouyte vs fro oure enemyes.
Ya kuma’yantar da mu daga abokan gābanmu,
25 Which yyueth mete to ech fleisch. Knouleche ye to God of heuene.
Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta.
26 Knouleche ye to the Lord of lordis; for his merci is with outen ende.
Ku yi godiya ga Allah na sama.

< Psalms 136 >