< Numbers 35 >

1 And the Lord spak these thingis to Moises, in the feeldi places of Moab, aboue Jordan,
A filayen Mowab, wajen Urdun, ɗaura da Yeriko, Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,
2 ayens Jericho, Comaunde thou to the sones of Israel, that thei yyue to dekenes of her possessiouns,
“Ka umarci Isra’ilawa su ba wa Lawiyawa garuruwan da za su zauna a ciki daga cikin gādon da Isra’ilawa za su mallaka. A kuma ba su wurin kiwo kewaye da garuruwan.
3 citees to dwelle, and the suburbabis of tho bi cumpas, that thei dwelle in `the citees, and the suburbabis be to beestis, and `werk beestis;
Sa’an nan za su kasance da garuruwan da za su zauna, su sami fili, da kuma za su yi kiwon garkensu na shanu da tumaki da kuma sauran dabbobinsu.
4 whiche suburbabis schulen be strecchid forth fro the wallis of citees with outforth `bi cumpas, in the space of a thousynde paacis;
“Wuraren kiwo a kewayen garuruwan da za a ba wa Lawiyawa, girmansu zai zama mai fāɗin kamu dubu ɗaya daga katangar garin.
5 ayens the eest schulen be two thousynde cubitis, and ayens the south in lijk manere schulen be two thousynde cubitis, and at the see that biholdith to the west schal be the same mesure, and the north coost schal be endid bi euene terme. And the citees schulen be in the myddis, and the suburbabis with outforth.
A bayan garin, ka auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu wajen kudu, da kuma kamu dubu uku wajen arewa, a bar garin a tsakiya. Za su kasance da wannan a matsayin wurin kiwo na garuruwan.
6 Forsothe of tho citees whiche ye schulen yyue to dekenes, sixe schulen be departid in to helpis of fugityues, `ether of fleynge men, that he that schedde blood, fle to tho; and outakun these sixe, ye schulen yyue to dekenes othere two and fourti citees,
“A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida daga cikin garuruwan za su zama biranen mafaka, inda wanda ya kashe mutum zai gudu yă je. Ban da wannan, a ba su waɗansu garuruwa arba’in da biyu.
7 that is, togidere eiyte and fourti, with her surburbabis.
Duka-duka dai a ba Lawiyawa garuruwa arba’in da takwas, tare da wuraren kiwonsu.
8 And tho citees that schulen be youun of the possessiouns of sones of Israel, schulen be takun awey, mo fro hem that han more, and fewere `schulen be takun awey fro hem that han lesse, alle bi hem silf schulen yyue bi the mesure of her eritage, citees to dekenes.
Garuruwan da za ku ba wa Lawiyawa daga ƙasar da Isra’ilawa suka mallaka, za a ba da su bisa girman gādon kowace kabila. Ka karɓi garuruwa masu yawa daga kabilar da take da garuruwa masu yawa, amma kaɗan daga kabilar da ba ta da garuruwa masu yawa.”
9 The Lord seide to Moises,
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
10 Spek thou to the sones of Israel, and thou schalt seie to hem, Whanne ye han passid Jordan, in the lond of Canaan,
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana,
11 deme ye whiche citees owen to be in to the helpis of fugityues, whiche not wilfuli han sched blood.
ku zaɓi waɗansu garuruwan da za su zama biranen mafakarku, inda wanda ya kashe mutum cikin kuskure zai iya gudu zuwa.
12 In whiche whanne the fleere hath fled, the kynesman of hym that is slayn, schal not mow sle hym, til he stonde in the siyt of the multitude, and the cause of hym be demed.
Za su zama wuraren mafaka daga hannun mai bin hakki, don kada a kashe mai kisankai, tun ba a kai shi gaban shari’a, a gaban taron jama’a ba.
13 Forsothe of tho citees that ben departid to the helpis of fugityues,
Waɗannan garuruwa shida da aka bayar za su zama biranen mafakarku.
14 thre schulen be ouer Jordan, and thre in the lond of Canaan;
A ba da uku a wannan gefe na Urdun, a kuma ba da uku a Kan’ana, su zama biranen mafaka.
15 as wel to the sones of Israel as to comelyngis and pilgryms; that he fle to tho citees, that schedde blood not wilfuli.
Waɗannan garuruwa shida za su zama wurin mafaka wa Isra’ilawa, baƙi da duk sauran mutanen da suke zama a cikinsu, saboda duk wanda ya kashe mutum cikin kuskure yă iya gudu zuwa.
16 If ony man smytith a man with yrun, and he that is smytun is deed, `the smyter schal be gilti of mansleyng, and he schal die.
“‘In wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, to, shi mai kisankai ne; sai a kashe mai kisankan nan.
17 If he castith a stoon, and a man is deed bi the strook, he schal be punyschid in lijk maner.
Ko kuwa in wani yana riƙe da dutsen da ya isa yă kashe mutum a hannunsa, ya kuma harbi wani da dutsen har ya mutu, to, shi mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.
18 If a man smytun with a staf dieth, he schal be vengid bi `the blood of the smytere.
Ko kuwa wani yana da makami na itace a hannunsa da ya isa yă kashe mutum, ya kuma bugi wani da shi har ya mutu, shi ma mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.
19 The niy kynesman of hym that is slayn schal sle the mansleere; anoon as he takith hym, `that is, the manquellere, he schal sle hym.
Sai mai bin hakkin jinin yă kashe mai kisankan, sa’ad da ya sadu da mai kisankan, sai yă kashe shi.
20 If bi haterede a man hurtlith, `ethir schoufith, `a man, ethir castith ony thing in to hym bi aspiyngis,
In saboda ƙiyayya, mutum ya laɓe, ya soke wani, ko ya jefe shi da wani abu da gangan har ya mutu,
21 ether whanne he was enemy, smoot with hond, and he is deed, the smytere schal be gilti of mansleyng. The kynesman `of him that is slayn, anoon as he findith him, `that is, the sleere, schal sle hym.
ko kuwa saboda ƙiyayya ya naushe shi har ya mutu, sai a kashe wannan mutumin da ya yi haka; shi mai kisankai ne. Sai mai bin hakkin jini yă kashe mai kisankan in ya same shi.
22 That if bi sudeyn caas, and without hatrede and enemytees,
“‘Amma in cikin tsautsayi ne ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuma ya jefe shi, ba da gangan ba,
23 he doith ony thing of these;
ko kuwa bai gan shi ba, ya jefa dutsen da zai kashe shi a kansa, ya kuwa mutu, to, da yake shi ba abokin gābansa ba ne, bai kuma yi nufi yă ji masa ba,
24 and this is preued in heryng `of the puple, and the questioun of blood is discussid bitwixe the smytere and the kynesman,
dole taro su yi hukunci tsakanin mai laifin, da mai bin hakkin jini bisa waɗannan ƙa’idodi.
25 the innocent schal be delyuered fro the hond of the vengere, and bi sentence of iugis he schal be led ayen in to the citee, to which he fledde, and he schal dwelle there, til the grete preest die, which is anoyntid with oile.
Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki.
26 If the sleere is foundun with out the coostis `of the citees that ben asigned to exilid men,
“‘Amma in wanda ake zargin ya kuskura ya fita, ya kai iyakar birnin mafaka wadda ya gudu ya je,
27 and is slayn of him that is vengere, he that sleeth him, `that is, the exilid man, schal be with out gilt;
idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan gari, mai bin hakkin jinin zai iya kashe mai kisankai ɗin ba tare da wani laifi ba.
28 for the exilid man ouyte sitte in the citee `til to the `deth of the bischop; forsothe aftir that thilke bischop is deed, the mansleere schal turne ayen in to his lond.
Dole wanda ake zargin, yă kasance a birninsa na mafaka sai bayan mutuwa babban firist; sai bayan mutuwar babban firist ne kawai zai iya komo ga mallakarsa.
29 These schulen be euerlastynge and lawful thingis in alle youre dwellyngis.
“‘Waɗannan su ne za su zama ƙa’idodin da za ku kasance da su, a dukan tsararraki masu zuwa.
30 A mansleere schal be punyschid vndur witnessis; no man schal `be dampned at the witnessyng of o man.
“‘Kowa da ya kashe wani, za a kashe shi a matsayin mai kisankai, bisa ga shaidar shaidu. Amma kada a kashe wani bisa ga shaidar mutum ɗaya.
31 Ye schulen not take prijs of him which is gilti of blood, anoon and he schal die.
“‘Kada a karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, wanda ya cancanci mutuwa. Lalle ne a kashe shi.
32 Men exilid, and fugityues, schulen not mow turne ayen in ony maner in to her citees, bifore the deeth of the bischop, lest ye defoulen the lond of youre abitacioun,
“‘Kada a karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don yă koma yă zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba.
33 which is defoulid bi the blood of innocent men; and it may not be clensid in other maner, no but bi the blood of hym, that schedde the blood of anothir man.
“‘Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama a ciki. Zub da jini yakan ƙazantar da ƙasa, ba a kuma iya yin kafara saboda wannan ƙasa da aka zub da jini, sai dai ta wurin jinin mutumin da ya zub da jinin.
34 And so youre possessioun schal be clensid, for Y schal dwelle with you; for Y am the Lord, that dwelle among the sones of Israel.
Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama, wadda ni kuma nake zama a ciki, gama Ni Ubangiji, ina zama a cikin Isra’ilawa.’”

< Numbers 35 >