< Hebrews 6 >
1 Therfor we bringinge in a word of the bigynnyng of Crist, be we borun to the perfeccioun of hym, not eftsoone leggynge the foundement of penaunce fro deed werkis, and of the feith to God,
Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sake koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah,
2 and of teching of baptimys, and of leiynge on of hondis, and of risyng ayen of deed men, and of the euerlastinge doom. (aiōnios )
da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da dora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukuci. (aiōnios )
3 And this thing we schulen do, if God schal suffre.
Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda.
4 But it is impossible, that thei that ben onys liytned, and `han tastid also an heuenly yifte, and ben maad parceneris of the Hooli Goost,
Domin wadanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka dandana baiwar nan Basamaniya, suka kuma sami rabo na Ruhu Mai Tsarki,
5 and netheles han tastid the good word of God, and the vertues of the world to comynge, (aiōn )
har su ka dandana dadin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa, (aiōn )
6 and ben slidun fer awei, that thei be renewid eftsoone to penaunce. Whiche eftsones crucifien to hem silf the sone of God, and han to scorn.
sa'an nan kuma suka ridda—ba mai yiwuwa ba ne a sake jawo su ga tuba, tun da yake sake gicciye Dan Allah suke yi su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari.
7 For the erthe that drinkith reyn ofte comynge on it, and bringith forth couenable erbe to hem of whiche it is tilid, takith blessing of God.
Kasa ma da take shanye ruwan da ake yi a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga wadanda ake nomanta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.
8 But that that is bringinge forth thornes and breris, is repreuable, and next to curs, whos endyng schal be in to brennyng.
Amma idan tsire-tsirenta kaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, karshenta dai konewa ne.
9 But, ye moost dereworthe, we tristen of you betere thingis, and neer to helthe, thouy we speken so.
Ko da yake mun fadi haka, a game da ku kam, ya kaunatattu mun tabbata kuna abubuwa mafiya kyau na zancen ceto.
10 For God is not vniust, that he foryete youre werk and loue, whiche ye han schewid in his name; for ye han mynystrid to seyntis, `and mynistren.
Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ki kula da aikinku, da kuma kaunar sunansa da kuke yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.
11 And we coueiten that ech of you schewe the same bisynesse to the fillyng of hope in to the ende;
Muna dai bukata kwarai kowannanku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa karshe.
12 that ye be not maad slowe, but also sueris of hem, whiche bi feith and pacience schulen enherite the biheestis.
Don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da wadanda suka karbi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da hakurinsu.
13 For God bihetinge to Abraham, for he hadde noon grettere, bi whom he schulde swere, swoor bi hym silf,
Sa'adda Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa,
14 and seide, Y blessinge schal blesse thee, and Y multipliynge schal multiplie thee;
Ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma ribambamya zuriyarka.”
15 and so he long abidinge hadde the biheeste.
Ta haka, Ibrahim bayan da ya jure da hakuri, ya karbi cikar alkawarin.
16 For men sweren bi a grettere than hem silf, and the ende of al her ple is an ooth to confirmacioun.
Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su. Rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa da kowacce magana.
17 In which thing God willynge to schewe plenteuouslier to the eiris of his biheest the sadnesse of his counsel,
Don haka, sa'adda Allah yake son kara tabbatar wa magadan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sakewa ba ne sam, sai ya hada da rantsuwa,
18 puttide bitwixe an ooth, that bi twey thingis vnmeuable, bi whiche it is impossible that God lie, we han a strengeste solace, `we that fleen togidere to holde the hope that is put forth to vs.
Domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sakewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi karya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu karfafa kwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai.
19 Which hope as an ankir we han sikir to the soule, and sad, and goynge in to the ynnere thingis of hiding;
Muna da bege, kamar yadda yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen.
20 where the bifore goere, Jhesus, that is maad bischop with outen ende bi the ordre of Melchisedech, entride for vs. (aiōn )
Inda saboda mu ne Yasu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin Malkisadak. (aiōn )