< 1 Thessalonians 4 >

1 Therfor, britheren, fro hennus forward we preien you, and bisechen in the Lord Jhesu, that as ye han resseyued of vs, hou it bihoueth you to go and to plese God, so walke ye, that ye abounde the more.
A karshe, 'yan'uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka.
2 For ye witen what comaundementis Y haue youun to you bi the Lord Jhesu.
Domin kun san umarnin da muka baku cikin Ubangiji Yesu.
3 For this is the wille of God, youre holynesse, that ye absteyne you fro fornycacioun.
Gama wannan ne nufin Allah: kebewar ku - cewa ku kauce wa zina da fasikanci,
4 That ech of you kunne welde his vessel in holynesse, and onour;
Cewa kowannenku ya san yadda zai rike mata tasa cikin tsarki da girmamawa.
5 not in passioun of lust, as hethene men that knowen not God.
Kada kayi mata cikin zautuwar sha'awa ( kamar al'ummai wadanda basu san Allah ba).
6 And that no man ouergo, nethir disseyue his brothir in chaffaring. For the Lord is venger of alle these thingis, as we biforseiden to you, and han witnessid.
Kada wani ya kuskura yaci amanar dan'uwansa akan wannan al'amari. Gama Ubangiji mai ramuwa ne akan dukkan wadannan al'amura, Kamar yadda a baya muka yi maku kashedi kuma muka shaida.
7 For God clepide not vs in to vnclennesse, but in to holynesse.
Gama Allah bai kira mu ga rashin tsarki ba, amma ga rayuwar tsarki.
8 Therfor he that dispisith these thingis, dispisith not man, but God, that also yaf his holi spirit in vs.
Domin haka, duk wanda yaki wannan ba mutane yaki ba, amma Allah, wanda ya bada Ruhunsa Mai Tsarki a gareku.
9 But of the charite of britherhed we hadden no nede to write to you; ye silf han lerud of God, that ye loue togidere;
Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa.
10 for ye don that in to alle britheren in al Macedonye. And, britheren, we preyen you, that ye abounde more; and taken kepe, that ye be quyet;
Ba shakka, kunayin haka ga dukkan 'yan'uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku 'yan'uwa, kuyi haka bugu da kari.
11 and that ye do youre nede, and `ye worche with youre hoondis, as we han comaundid to you;
Kuma muna gargadin ku 'yan'uwa kuyi kokari ku zauna a natse, ku kula da al'amuranku, kuyi aiki da hannuwanku, Yadda muka umarceku a baya.
12 and that ye wandre onestli to hem that ben with outforth, and that of no mannus ye desir ony thing.
Kuyi haka domin tafiyar ku ta zama dai dai a gaban wadanda basu bada gaskiya ba, kuma ya zama baku cikin bukatar komai.
13 For, britheren, we wolen not, that ye vnknowe of men that dien, that ye be not soreuful, as othere that han not hope.
Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, 'yan'uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba.
14 For if we bileuen, that Jhesu was deed, and roos ayen, so God schal lede with hym hem that ben deed bi Jhesu.
Domin idan mun bada gaskiya Yesu ya mutu kuma ya tashi, haka kuma tare da Yesu Allah zai maido da duk wadanda suka yi barci a cikinsa.
15 And we seien this thing to you in the word of the Lord, that we that lyuen, that ben left in the comyng of the Lord, schulen not come bifor hem that ben deed.
Gama muna fada maku wannan daga maganar Ubangiji, cewa mu da muke a raye, da aka bari har zuwan Ubangiji, babu shakka ba za mu riga wadanda suka yi barci ba.
16 For the Lord hym silf schal come doun fro heuene, in the comaundement, and in the vois of an archaungel, and in the trumpe of God; and the deed men that ben in Crist, schulen rise ayen first.
Gama Ubangiji da kan sa zai sauko daga sama. Zai zo da muryar babban mala'ika, da karar kahon Allah, sai matattu cikin Almasihu su fara tashi.
17 Afterward we that lyuen, that ben left, schulen be rauyschid togidere with hem in cloudis, metinge Crist `in to the eir; and so euere more we schulen be with the Lord.
Sai mu da muke a raye, wadanda aka bari, tare dasu za'a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu hadu da Ubangiji cikin sararin sama. Haka zamu cigaba da kasancewa da Ubangiji.
18 Therfor be ye coumfortid togidere in these wordis.
Domin haka ku ta'azantar da juna da wadannan maganganu.

< 1 Thessalonians 4 >