< Hebrews 8 >

1 Now the sum of the things that have been said is this, that we have such an high-priest, who is sat down at the right hand of the throne of the majesty in the heavens;
Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama,
2 a minister of holy things, and of the true tabernacle, which the Lord hath raised, and not man.
wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.
3 For every high-priest is appointed to offer gifts and sacrifices; wherefore it was necessary that He also should have something to offer.
Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yă miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yă kasance da abin da zai miƙa.
4 For if He were on earth, He could not be a priest, seeing there are priests already that offer gifts according to the law:
Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye.
5 who worship under the representation and shadow of heavenly things; as Moses was ordered by God, when he was about to finish the tabernacle. For see, saith He, that thou make all according to the model shewn thee in the mount.
Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”
6 But now He hath obtained a more excellent ministry, inasmuch as He is also the mediator of a better covenant, which is established upon better promises.
Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
7 For if the first covenant had been unexceptionable, there had been no room for a second:
Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba.
8 as we see there was, for after complaining of them, He adds, "Behold the days come, saith the Lord, that I will make a new covenant with the house of Israel, and with the house of Judah:
Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.
9 not according to the covenant which I made with their fathers, in the day when I took them by the hand to lead them out of the land of Egypt; for they continued not in my covenant, and I regarded them not, saith the Lord.
Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji.
10 But this is the covenant that I will make with the house of Israel after those days, saith the Lord, I will put my laws into their mind, and I will inscribe them on their hearts; and I will be to them a God, and they shall be to me a people.
Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.
11 And they shall not teach every one his neighbour, and every one his brother, saying, Know the Lord: for they shall all know me, from the lest even to the greatest of them.
Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.
12 For I will forgive their crimes, and their sins and their iniquities I will remember no more."
Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”
13 Now by saying, a new covenant, He hath antiquated the first: and what is antiquated, and groweth old, is near it's exit.
Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.

< Hebrews 8 >