< Acts 18 >
1 After these things Paul departed from Athens and came to Corinth.
Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korint.
2 And finding there a certain Jew, named Aquila, a native of Pontus, who was lately come from Italy, with his wife Priscilla, (because Claudius Cesar had ordered all the Jews to depart from Rome, ) he went to them;
A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su,
3 and as he was of the same trade, he staid and worked with them: for they were tent-makers.
da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamar su, sai ya zauna ya yi aiki tare da su.
4 And he discoursed in the synagogue every sabbath-day, and persuaded both Jews and Greeks.
Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majami’a, yana ƙoƙari yă rinjayi Yahudawa da Hellenawa.
5 And when Silas and Timothy came down from Macedonia, Paul was very urgent in spirit, testifying to the Jews that Jesus was the Messiah.
Sa’ad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin wa’azi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.
6 But as they opposed and blasphemed, he shook his garment, and said unto them, Your blood be upon your own heads; I am clear of it: from henceforth I will go to the Gentiles.
Amma sa’ad da Yahudawa suka yi hamayya da Bulus suka kuma shiga zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa a cikin rashin yarda, ya ce musu, “Alhakinku yana a kanku! Ba ni da wani laifi. Daga yanzu zan tafi wajen Al’ummai.”
7 And departing thence, he went to the house of one named Justus, who worshipped God, whose house was contiguous to the synagogue.
Sai Bulus ya bar majami’ar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titus Yustus, mai yi wa Allah sujada.
8 But Crispus the ruler of the synagogue believed on the Lord with all his house: and many of the Corinthians hearing the word believed, and were baptized.
Kirisbus, shugaban majami’a, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma.
9 And the Lord said to Paul by a vision in the night, "Fear not, but speak: and be not silent:
Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru.
10 for I am with thee, and no man shall lay hands on thee to hurt thee; for I have much people in this city."
Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”
11 And he staid a year and six months, teaching among them the word of God.
Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah.
12 But when Gallio was proconsul of Achaia, the Jews with one accord rose against Paul, and brought him to the seat of justice,
Yayinda Galliyo yake muƙaddas Akayya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kuwa kawo shi cikin kotu.
13 saying, this fellow persuadeth men to worship God contrary to the law.
Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”
14 And when Paul was going to speak, Gallio said to the Jews, If it were indeed an act of injustice, or some wicked crime, it would be reasonable that I should bear with you.
A daidai sa’ad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku.
15 But if it be a question about words, and names, and your law, settle it yourselves; for I will be no judge of these matters.
Amma da yake ya shafi gardama ce game da kalmomi da sunaye da kuma dokarku, sai ku ji da ita da kanku. Ni ba zan zama mai shari’a kan irin waɗannan abubuwa ba.”
16 And he ordered them away from the tribunal.
Saboda haka ya kore su.
17 Then all the Greeks took Sosthenes the ruler of the synagogue, and beat him even before the tribunal: but Gallio did not concern himself about the matter.
Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majami’a suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yă kula.
18 And after Paul had staid there yet a considerable time, he took leave of the brethren, and sailed from thence to Syria, and with him Priscilla and Aquila, after he had shaved his head at Cenchrea; for he had a vow.
Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.
19 And he came to Esphesus, and left them there: but before his departure he himself went into the synagogue, and reasoned with the Jews.
Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majami’a ya kuma yi muhawwara da Yahudawa.
20 Though when they desired him to stay longer with them, he did not consent: but took his leave of them,
Sa’ad da suka roƙe shi ya ƙara’yan kwanaki da su, bai yarda ba.
21 saying, I must by all means keep the approaching feast at Jerusalem; but I will return to you again, God willing. So he sailed from Ephesus;
Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.
22 and landing at Cesarea, went up to Jerusalem, and after he had saluted the church, he went down to Antioch.
Sa’ad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya sa’an nan ya gangara zuwa Antiyok.
23 And when he had spent some time there, he departed, and went in order through the country of Galatia and Phrygia strengthening all the disciples.
Bayan ya yi’yan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga ko’ina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.
24 Now there came to Ephesus a certain Jew named Apollos, an Alexandrian by birth, an eloquent man, and mighty in the scriptures.
Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.
25 Who had been instructed in the way of our Lord; and being fervent in spirit, he spake and taught clearly the things of the Lord, though he knew only the baptism of John.
An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani.
26 And as he began to speak openly in the synagogue, Aquila and Priscilla heard him and took him home, and expounded to him the way of God more perfectly.
Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.
27 And as he was inclined to go into Achaia, the brethren wrote to the disciples exhorting them to receive him: who when he arrived, was very helpful to those who had believed through grace.
Sa’ad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai’yan’uwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata.
28 For he disputed vehemently with the Jews in public, proving by the scriptures, that Jesus was the Christ.
Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.