< Romans 7 >

1 Or don’t you know, brothers (for I speak to men who know the law), that the law has dominion over a man for as long as he lives?
'Yan'uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari'a), cewar shari'a na mulkin mutum muddin ransa?
2 For the woman that has a husband is bound by law to the husband while he lives, but if the husband dies, she is discharged from the law of the husband.
Domin ta wurin shari'a matar aure a daure take muddin mijinta nada rai, amma idan mijinta ya mutu, ta kubuta daga shari'ar aure.
3 So then if, while the husband lives, she is joined to another man, she would be called an adulteress. But if the husband dies, she is free from the law, so that she is no adulteress, though she is joined to another man.
To don haka idan, mijinta na da rai, sai ta tafi ta zauna da wani mutumin, za'a kirata mazinaciya. Amma idan mijin ya mutu, ''yantarciya ce daga shari'a, domin kada ta kasance mazinaciya idan ta auri wani mutum.
4 Therefore, my brothers, you also were made dead to the law through the body of Messiah, that you would be joined to another, to him who was raised from the dead, that we might produce fruit to God.
Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya.
5 For when we were in the flesh, the sinful passions which were through the law worked in our members to bring out fruit to death.
Domin sa'adda muke cikin jiki, ana motsa dabi'armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari'a domin mu haifi 'ya'ya zuwa mutuwa.
6 But now we have been discharged from the law, having died to that in which we were held; so that we serve in newness of the spirit, and not in oldness of the letter.
Amma yanzu an kubutar damu daga shari'a, mun mutu daga abin da ya daure mu, domin mu yi bauta cikin sabuntuwar Ruhu, ba cikin tsohon rubutun shari'a ba.
7 What shall we say then? Is the law sin? May it never be! However, I wouldn’t have known sin except through the law. For I wouldn’t have known coveting unless the law had said, “You shall not covet.”
To me zamu ce kenan? ita shari'ar kanta zunubi ce? ba zai taba faruwa ba. Duk da haka. Idan ba ta wurin shari'a ba, ba zan taba sanin zunubi ba, in ba ta wurin shari'a ba. Ba zan taba kyashin abin wani ba, har sai da shari'a tace, “Kada kayi kyashi.”
8 But sin, finding occasion through the commandment, produced in me all kinds of coveting. For apart from the law, sin is dead.
Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha'awa dake cikina. Domin in da babu shari'a, zunubi matacce ne.
9 I was alive apart from the law once, but when the commandment came, sin revived and I died.
Ada na rayu sau daya ba tare da shari'a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu.
10 The commandment which was for life, this I found to be for death;
Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya.
11 for sin, finding occasion through the commandment, deceived me, and through it killed me.
Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni.
12 Therefore the law indeed is holy, and the commandment holy, righteous, and good.
Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau.
13 Did then that which is good become death to me? May it never be! But sin, that it might be shown to be sin, was producing death in me through that which is good; that through the commandment sin might become exceedingly sinful.
To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi.
14 For we know that the law is spiritual, but I am fleshly, sold under sin.
Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi.
15 For I don’t understand what I am doing. For I don’t practice what I desire to do; but what I hate, that I do.
Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa.
16 But if what I don’t desire, that I do, I consent to the law that it is good.
Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau.
17 So now it is no more I that do it, but sin which dwells in me.
Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina.
18 For I know that in me, that is, in my flesh, dwells no good thing. For desire is present with me, but I don’t find it doing that which is good.
Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa.
19 For the good which I desire, I don’t do; but the evil which I don’t desire, that I practice.
Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa.
20 But if what I don’t desire, that I do, it is no more I that do it, but sin which dwells in me.
To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina.
21 I find then the law that, while I desire to do good, evil is present.
Don haka, sai na iske, akwai ka'ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani.
22 For I delight in God’s Torah after the inward person,
Domin a cikina ina murna da shari'ar Allah.
23 but I see a different law in my members, warring against the law of my mind, and bringing me into captivity under the law of sin which is in my members.
Amma ina ganin wasu ka'idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka'idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka'idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina.
24 What a wretched man I am! Who will deliver me out of the body of this death?
Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa?
25 I thank God through Yeshua the Messiah, our Lord! So then with the mind, I myself serve God’s Torah, but with the flesh, sin’s law.
Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari'ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka'idar zunubi da ke tare da jikina.

< Romans 7 >