< 1 Peter 3 >

1 In the same way, wives, be in subjection to your own husbands, so that, even if any don’t obey the Word, they may be won by the behavior of their wives without a word,
Haka ku kuma da kuke matan aure, kuyi biyayya da na ku mazajen, domin in har wadansunsu basa biyayya da maganar Allah, halin matansu ya shawo kansu ba tare da magana ba,
2 seeing your pure behavior in fear.
Domin sun ga tsattsakan halinku da ladabinku.
3 Let your beauty come not from the outward adorning of braiding your hair, and of wearing gold ornaments or of putting on fine clothing,
Haka ma adonku kar ya zama na kwalliyar waje kitson kai, kayan zinariya ko tufafi masu kawa.
4 but from the hidden person of the heart, in the incorruptible adornment of a gentle and quiet spirit, which is very precious in God’s sight.
Amma bari adon ya zama na mutum na cikin zuciya, kuma adon ya zama kyan nan marar dushewa, na kamun kai da natsatsen ruhu, wanda yake da daraja a gaban Allah.
5 For this is how in the past the holy women who hoped in God also adorned themselves, being in subjection to their own husbands.
Haka tsarkakan mata su ka yi ado kamar haka. Suka dogara ga Allah suka yi biyayya ga mazajensu.
6 So Sarah obeyed Abraham, calling him lord, whose children you now are if you do well and are not put in fear by any terror.
Ta haka Saratu ta yi biyayya ga Ibrahim ta kira shi “ubangiji”. Yanzu ku 'ya'yantane in dai kun yi aiki nagari, idan kuma ba ku ji tsoron wahala ba.
7 You husbands, in the same way, live with your wives according to knowledge, giving honor to the woman as to the weaker vessel, as also being joint heirs of the grace of life, that your prayers may not be hindered.
Kamar yadda na fada wa matan aure haka ma mazaje, ku zauna da mata da sanin su raunana ne abokan tarayya ne na karbar baiwar rayuwa. Ku dinga yin haka domin a rika jin addu'oinku.
8 Finally, all of you be like-minded, compassionate, loving as brothers, tenderhearted, courteous,
Daga karshe, dukanku ku hada hankulanku, ku zama masu juyayi, masu kauna kamar 'yan'uwa, masu taushin zuciya, masu tawali'u.
9 not rendering evil for evil or insult for insult; but instead blessing, knowing that you were called to this, that you may inherit a blessing.
Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi. A maimakon haka ku cigaba da sa albarka, gama sabili da haka ne musamman aka kiraye ku, domin ku gaji albarka.
10 For, “He who would love life and see good days, let him keep his tongue from evil and his lips from speaking deceit.
“Wanda duk yake so ya more a rayuwarsa ya kuma ga kwanaki masu alheri, to fa, ya kame harshen sa daga mugunta da lebensa daga maganganun yaudara.
11 Let him turn away from evil and do good. Let him seek peace and pursue it.
Ya rabu da mugunta ya aikata abin da ke nagari. Bari ya nemi zaman salama ya kuma dimanceta.
12 For the eyes of the Lord are on the righteous, and his ears open to their prayer; but the face of the Lord is against those who do evil.”
Idanun Ubangiji suna duban adalai, kunnuwansa kuma suna sauraron roke rokensu. Amma fuskar Ubangiji tana gaba da masu aikata mugunta.”
13 Now who will harm you if you become imitators of that which is good?
Wanene ya isa ya cuce ku idan kun himmatu ga yin abin da ke nagari?
14 But even if you should suffer for righteousness’ sake, you are blessed. “Don’t fear what they fear, neither be troubled.”
Amma idan kuna shan wuya saboda adalci, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoron abin da su ke tsoro. Kada ku damu.
15 But sanctify the Lord God in your hearts. Always be ready to give an answer to everyone who asks you a reason concerning the hope that is in you, with humility and fear,
Maimakon haka, ku kebe Ubangiji a cikin zukatanku cewa shi mai tsarki ne. Kullum ku zauna da shiri domin ku amsa wa mai tambayar ku dalilin sa begenku ga Allah. Amma fa kuyi haka tare da tawali'u da bangirma.
16 having a good conscience. Thus, while you are spoken against as evildoers, they may be disappointed who curse your good way of life in Messiah.
Ku zama da tsatsakan lamiri domin mutanen da ke zargin rayuwarku mai kyau cikin Almasihu, su ji kunya domin suna maganar gaba da ku kamar ku mugaye ne.
17 For it is better, if it is God’s will, that you suffer for doing what is right than for doing evil.
Ya fi kyau, a sha wuya akan aiki nagari, idan nufin Allah ne, da a sha wuya sabili da mugun aiki.
18 Because Messiah also suffered for sins once, the righteous for the unrighteous, that he might bring you to God, being put to death in the flesh, but made alive in the Spirit,
Almasihu ya sha wahala sau daya tak sabili da zunubai. Shi da ya ke mai adalci ya sha wahala domin mu marasa adalci, domin ya kawo mu ga Allah. Aka kashe shi cikin jiki, amma aka rayar da shi cikin Ruhu.
19 in whom he also went and preached to the spirits in prison,
A Ruhu ne, ya je ya yi wa'azi ga ruhohin da ke a yanzu cikin kurkuku.
20 who before were disobedient when God waited patiently in the days of Noah while the ship was being built. In it, few, that is, eight souls, were saved through water.
Sun yi rashin biyayya ne sa'adda hakurin Allah yake jiransu a lokacin Nuhu a zamanin sassaka jirgin ruwa, sai Allah ya tsirar da mutane kalilan wato rayuka takwas daga cikin ruwa.
21 This is a symbol of immersion, which now saves you—not the putting away of the filth of the flesh, but the answer of a good conscience toward God—through the resurrection of Yeshua the Messiah,
Wannan kwatancin baftismar da take cetonmu yanzu ne, ba kamar ta wanke Dauda daga jiki ba, sai dai ta rokon Allah da lamiri mai kyau ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu.
22 who is at the right hand of God, having gone into heaven, angels and authorities and powers being made subject to him.
Ya hau sama. Yana dama ga Allah. Mala'iku, da mulkoki da masu iko dole su yi masa biyayya.

< 1 Peter 3 >