< 3 John 1 >

1 The elder to Gaius the beloved, whom I love in truth.
Dattijon nan, Zuwa ga ƙaunataccen abokina Gayus, wanda nake ƙauna ƙwarai da gaske.
2 Beloved, I pray that you may prosper in all things and be healthy, even as your soul prospers.
Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.
3 For I rejoiced greatly when brothers came and testified about your truth, even as you walk in truth.
Na yi farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗansu’yan’uwa suka zo suka yi zance game da yadda kake da aminci ga gaskiyan nan da kuma yadda kake cin gaba cikin gaskiyan nan.
4 I have no greater joy than this: to hear about my children walking in truth.
Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
5 Beloved, you do a faithful work in whatever you accomplish for those who are brothers and strangers.
Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa’yan’uwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka.
6 They have testified about your love before the assembly. You will do well to send them forward on their journey in a way worthy of God,
Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah.
7 because for the sake of the Name they went out, taking nothing from the Gentiles.
Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba.
8 We therefore ought to receive such, that we may be fellow workers for the truth.
Saboda haka ya kamata mu nuna halin karɓan baƙi ga irin mutanen nan domin mu yi aiki tare saboda gaskiyan nan.
9 I wrote to the assembly, but Diotrephes, who loves to be first among them, doesn’t accept what we say.
Na rubuta wa ikkilisiya, amma Diyotirefes, wanda yake son zama na farko, ya ƙi yă yi hulɗa da mu.
10 Therefore, if I come, I will call attention to his deeds which he does, unjustly accusing us with wicked words. Not content with this, he doesn’t receive the brothers himself, and those who would, he forbids and throws out of the assembly.
Saboda haka in na zo, zan tone abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har yana ƙin marabtar’yan’uwa. Yana hana waɗanda suke so yin haka, yana ma korinsu daga ikkilisiya.
11 Beloved, don’t imitate that which is evil, but that which is good. He who does good is of God. He who does evil hasn’t seen God.
Abokina ƙaunatacce, kada ka yi koyi da abin da yake mugu sai dai abin da yake nagari. Duk mai yin abin da yake nagari daga Allah yake. Duk mai yin abin da yake mugu bai taɓa sanin Allah ba.
12 Demetrius has the testimony of all, and of the truth itself; yes, we also testify, and you know that our testimony is true.
Demetiriyus yana da shaida mai kyau daga wurin kowa, har gaskiya kanta ma ta shaide shi. Mu ma muna ba da shaida mai kyau a kansa, ka kuma san cewa shaidarmu gaskiya ce.
13 I had many things to write to you, but I am unwilling to write to you with ink and pen;
Ina da abubuwa da dama da zan rubuta maka, sai dai ba na so in yi amfani da alƙalami da inki in rubuta su.
14 but I hope to see you soon. Then we will speak face to face. Peace be to you. The friends greet you. Greet the friends by name.
Ina fata in gan ka nan ba da daɗewa ba, za mu kuwa yi magana fuska da fuska. Salama gare ka. Abokai a nan suna gaishe ka. Ka gai da abokai a can da sunansu.

< 3 John 1 >