< Matthew 16 >
1 The Pharisees and Sadducees came, and testing him, asked him to show them a sign from heaven.
Sai Farisawa da Sadukiyawa suka zo su gwada shi suka roke shi ya nuna masu alama daga sama.
2 But he answered them, “When it is evening, you say, ‘It will be fair weather, for the sky is red.’
Amma ya amsa ya ce masu, “Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,'
3 In the morning, ‘It will be foul weather today, for the sky is red and threatening.’ Hypocrites! You know how to discern the appearance of the sky, but you can’t discern the signs of the times!
Kuma da safe ku ce, 'Zai zama yanayi mara kyau a yau, domin sama ta yi ja ta kuma gama gari, kun san yadda za ku bayyana kammanin sararin sama, amma ba ku iya bayyana alamun lokaci ba.
4 An evil and adulterous generation seeks after a sign, and there will be no sign given to it, except the sign of the prophet Jonah.” He left them and departed.
Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa.” Daga nan sai Yesu ya tafi.
5 The disciples came to the other side and had forgotten to take bread.
Almajiran suka zo daga wancan gefe, amma sun manta su dauki gurasa,
6 Jesus said to them, “Take heed and beware of the yeast of the Pharisees and Sadducees.”
Yesu ya ce masu, “Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.”
7 They reasoned amongst themselves, saying, “We brought no bread.”
Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, “Ko saboda bamu kawo gurasa bane.”
8 Jesus, perceiving it, said, “Why do you reason amongst yourselves, you of little faith, because you have brought no bread?
Yesu yana sane da wannan sai ya ce, “Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane?
9 Don’t you yet perceive or remember the five loaves for the five thousand, and how many baskets you took up,
Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba?
10 or the seven loaves for the four thousand, and how many baskets you took up?
Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba?
11 How is it that you don’t perceive that I didn’t speak to you concerning bread? But beware of the yeast of the Pharisees and Sadducees.”
Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.”
12 Then they understood that he didn’t tell them to beware of the yeast of bread, but of the teaching of the Pharisees and Sadducees.
Sa'annan suka fahimta cewa ba yana gaya masu su yi hankali da yistin da ke cikin gurasa ba ne, amma sai dai su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa.
13 Now when Jesus came into the parts of Caesarea Philippi, he asked his disciples, saying, “Who do men say that I, the Son of Man, am?”
A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake?
14 They said, “Some say John the Baptiser, some, Elijah, and others, Jeremiah or one of the prophets.”
Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.”
15 He said to them, “But who do you say that I am?”
Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?”
16 Simon Peter answered, “You are the Christ, the Son of the living God.”
Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.”
17 Jesus answered him, “Blessed are you, Simon Bar Jonah, for flesh and blood has not revealed this to you, but my Father who is in heaven.
Yesu ya amsa ya ce masa, “Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama.
18 I also tell you that you are Peter, and on this rock I will build my assembly, and the gates of Hades will not prevail against it. (Hadēs )
Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba. (Hadēs )
19 I will give to you the keys of the Kingdom of Heaven, and whatever you bind on earth will have been bound in heaven; and whatever you release on earth will have been released in heaven.”
Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama,”
20 Then he commanded the disciples that they should tell no one that he was Jesus the Christ.
Sai Yesu ya umarci almajiransa kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu.
21 From that time, Jesus began to show his disciples that he must go to Jerusalem and suffer many things from the elders, chief priests, and scribes, and be killed, and the third day be raised up.
Daga lokacin nan Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa a hannun dattawa, da manyan firistoci da malaman attaura, a kashe shi, a tashe shi zuwa rai a rana ta uku.
22 Peter took him aside and began to rebuke him, saying, “Far be it from you, Lord! This will never be done to you.”
Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.”
23 But he turned and said to Peter, “Get behind me, Satan! You are a stumbling block to me, for you are not setting your mind on the things of God, but on the things of men.”
Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.”
24 Then Jesus said to his disciples, “If anyone desires to come after me, let him deny himself, take up his cross, and follow me.
Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni.
25 For whoever desires to save his life will lose it, and whoever will lose his life for my sake will find it.
Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Duk wanda ya rasa ransa domina zai same shi.
26 For what will it profit a man if he gains the whole world and forfeits his life? Or what will a man give in exchange for his life?
Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa?
27 For the Son of Man will come in the glory of his Father with his angels, and then he will render to everyone according to his deeds.
Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa.
28 Most certainly I tell you, there are some standing here who will in no way taste of death until they see the Son of Man coming in his Kingdom.”
Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.”