< Hebrews 4 >
1 Let’s fear therefore, lest perhaps anyone of you should seem to have come short of a promise of entering into his rest.
Saboda haka, sai muyi lura kwarai don kada wani ya kasa kai ga shiga hutun da aka alkawarta maku na Allah.
2 For indeed we have had good news preached to us, even as they also did, but the word they heard didn’t profit them, because it wasn’t mixed with faith by those who heard.
Don mun ji albishir game da hutun Allah kamar yadda aka fada masu. Amma wancan sakon bai anfana ga wadanda suka ji ba tare da sun bada gaskiya ga sakon ba.
3 For we who have believed do enter into that rest, even as he has said, “As I swore in my wrath, they will not enter into my rest;” although the works were finished from the foundation of the world.
Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, “Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba.” Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya.
4 For he has said this somewhere about the seventh day, “God rested on the seventh day from all his works;”
Domin yayi fadi a wani wuri game da rana ta bakwai, “Allah ya huta a rana ta bakwai daga dukkan ayyukansa.”
5 and in this place again, “They will not enter into my rest.”
Ya sake cewa, “Baza su taba shiga hutu na ba.”
6 Seeing therefore it remains that some should enter into it, and they to whom the good news was preached before failed to enter in because of disobedience,
Saboda haka, tun da hutun Allah na kebe domin masu su shiga, kuma tun da Isra'ilawa da yawa wadanda suka ji sakon nan mai kyau game da hutunsa ba su shiga ba saboda rashin biyayya,
7 he again defines a certain day, “today”, saying through David so long a time afterward (just as has been said), “Today if you will hear his voice, don’t harden your hearts.”
Allah ya sake shirya wata rana da ake kira, “Yau.” Ya sa wannan rana sa'adda yayi magana ta wurin Dauda, wanda ya ce tun da dadewa da aka fara fada, “Yau idan kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”
8 For if Joshua had given them rest, he would not have spoken afterward of another day.
Don idan Joshua ya ba su hutu, da Allah ba zai sake magana a kan wata rana ba.
9 There remains therefore a Sabbath rest for the people of God.
Saboda haka, akwai hutun asabar kebabbe ga mutanen Allah.
10 For he who has entered into his rest has himself also rested from his works, as God did from his.
Don shi wanda ya shiga hutun Allah shi kansa ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah yayi da nasa.
11 Let’s therefore give diligence to enter into that rest, lest anyone fall after the same example of disobedience.
Saboda haka muyi marmarin shiga wancan hutun, don kada kowa ya fadi ga irin rashin biyayyar da suka yi.
12 For the word of God is living and active, and sharper than any two-edged sword, piercing even to the dividing of soul and spirit, of both joints and marrow, and is able to discern the thoughts and intentions of the heart.
Maganar Allah kuwa rayayyiyace, kuma mai ci, fiye da takobi mai kaifi-biyu. Takan ratsa har tsakanin rai da ruhu, kuma tana kaiwa bargo. Takan iya bincika tunanin zuciya da manufarta.
13 There is no creature that is hidden from his sight, but all things are naked and laid open before the eyes of him to whom we must give an account.
Babu halittaccen abu da ke boye a idon Allah. Sai dai, kome a sarari yake, kuma a bayyane yake a idonsa wanda lallai ne zamu bada lissafin kanmu a gare shi.
14 Having then a great high priest who has passed through the heavens, Jesus, the Son of God, let’s hold tightly to our confession.
Da yake muna da babban firist wanda ya ratsa sammai, Yesu Dan Allah, sai mu riki bangaskiyarmu da karfi.
15 For we don’t have a high priest who can’t be touched with the feeling of our infirmities, but one who has been in all points tempted like we are, yet without sin.
Domin babban firist namu ba marar tausayi ga kasawarmu bane, amma wanda aka jarraba ne ta ko wanne hali irin yadda aka yi mana, sai dai ba'a same shi da zunubi ba.
16 Let’s therefore draw near with boldness to the throne of grace, that we may receive mercy and may find grace for help in time of need.
Sai mu zo wurin kursiyin alheri gabagadi, domin a yi mana jinkai mu kuwa sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.