< Proverbs 30 >
1 The words of Agur the son of Jakeh, [even] the prophecy: the man spoke to Ithiel, even to Ithiel and Ucal,
Maganganun Agur ɗan Yake, magana ce horarriya. Wannan mutum ya furta wa Itiyel da kuma ga Ukal,
2 Surely I [am] more brutish than [any] man, and have not the understanding of a man.
“Ni ne mafi jahilci a cikin mutane; ba ni da fahimi irin na mutum.
3 I neither learned wisdom, nor have the knowledge of the holy.
Ban koyi hikima ba, ba ni kuma da sani game da Mai Tsarkin nan,
4 Who hath ascended into heaven, or descended? who hath gathered the wind in his fists? who hath bound the waters in a garment? who hath established all the ends of the earth? what [is] his name, and what [is] his son's name, if thou canst tell?
Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani!
5 Every word of God [is] pure: he [is] a shield to them that put their trust in him.
“Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
6 Add thou not to his words, lest he reprove thee, and thou be found a liar.
Kada ka ƙara ga maganarsa, in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne.
7 Two [things] have I required of thee; deny [them] not to me before I die:
“Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji; kada ka hana ni kafin in mutu.
8 Remove far from me vanity and lies; give me neither poverty nor riches; feed me with food convenient for me:
Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.
9 Lest I be full, and deny [thee], and say, Who [is] the LORD? or lest I be poor, and steal, and take the name of my God [in vain].
In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.
10 Accuse not a servant to his master, lest he curse thee, and thou be found guilty.
“Kada ka baza ƙarairayi game da bawa ga maigidansa, in ba haka ba, zai la’ance ka, za ka kuwa sha wahala a kan haka.
11 [There is] a generation [that] curseth their father, and doth not bless their mother.
“Akwai waɗanda sukan zagi mahaifinsu ba sa kuma sa wa mahaifiyarsu albarka;
12 [There is] a generation [that are] pure in their own eyes, and [yet] are not washed from their filthiness.
waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su;
13 [There is] a generation, O how lofty are their eyes! and their eyelids are lifted up.
waɗanda kullum idanunsu masu kallon reni ne, waɗanda kallon da suke yi na daurin gira ne;
14 [There is] a generation, whose teeth [are as] swords, and their jaw-teeth [as] knives, to devour the poor from off the earth, and the needy from [among] men.
waɗanda haƙoransu takuba ne waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne don su cinye matalauta daga duniya da kuma mabukata daga cikin mutane.
15 The horse-leech hath two daughters, [crying], Give, give. There are three [things that] are never satisfied, [yes], four [things] say not, [It is] enough:
“Matsattsaku tana da’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’
16 The grave; and the barren womb; the earth [that] is not filled with water; and the fire [that] saith not, [It is] enough. (Sheol )
Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’ (Sheol )
17 The eye [that] mocketh at [its] father, and despiseth to obey [its] mother, the ravens of the valley shall pick it out, and the young eagles shall eat it.
“Idon da yake yi wa mahaifi ba’a, wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya, hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido, ungulai za su cinye su.
18 There are three [things which] are too wonderful for me, yes, four which I know not:
“Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,
19 The way of an eagle in the air; the way of a serpent upon a rock; the way of a ship in the midst of the sea; and the way of a man with a maid.
yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da’ya mace.
20 Such [is] the way of an adulterous woman; she eateth, and wipeth her mouth, and saith, I have done no wickedness.
“Ga yadda mazinaciya take yi. Takan ci ta share bakinta ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’
21 For three [things] the earth is disquieted, and for four [which] it cannot bear:
“Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki, abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa,
22 For a servant when he reigneth; and a fool when he is filled with food.
bawan da ya zama sarki, wawan da ya ƙoshi da abinci,
23 For an odious [woman] when she is married; and a handmaid that is heir to her mistress.
macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji, da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta.
24 There are four [things which are] little upon the earth, but they [are] very wise:
“Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana, duk da haka suna da hikima ƙwarai.
25 The ants [are] a people not strong, yet they prepare their food in the summer;
Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;
26 The conies [are but] a feeble people, yet they make their houses in the rocks;
remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;
27 The locusts have no king, yet go they forth all of them by bands;
fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;
28 The spider taketh hold with her hands, and is in king's palaces.
ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.
29 There are three [things] which go well, yes, four are comely in going:
“Akwai abubuwa uku da suke jan jiki da kuma taƙama a tafiyarsu abubuwa huɗu waɗanda suke kwarjini da taƙama a tafiyarsu,
30 A lion, [which is] strongest among beasts, and turneth not away for any;
zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa;
31 A greyhound; a he-goat also; and a king, against whom [there is] no rising up.
zakara mai taƙama, da bunsuru, da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi.
32 If thou hast done foolishly in lifting up thyself, or if thou hast thought evil, [lay] thy hand upon thy mouth.
“In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka, ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta, ka dāfa hannunka a bisa bakinka!
33 Surely the churning of milk bringeth forth butter, and the wringing of the nose bringeth forth blood: so the forcing of wrath bringeth forth strife.
Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.”