< John 6 >
1 After these things Jesus went over the sea of Galilee, which is [the sea] of Tiberias.
Bayan waddannan abubuwa, Yesu ya ketare tekun Galili, wanda a ke kira tekun Tibariya.
2 And a great multitude followed him, because they saw his miracles which he performed on them that were diseased.
Sai taro mai yawa suka bi shi domin suna ganin alamu da yake yi akan marasa lafiya.
3 And Jesus went upon a mountain, and there he sat with his disciples.
Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.
4 And the passover, a feast of the Jews, was nigh.
(Kuma da idin Ketarewa, wato idin Yahudawa, ya kusato.)
5 When Jesus then lifted up [his] eyes, and saw a great company come to him, he saith to Philip, Whence shall we buy bread that these may eat?
Da Yesu ya daga kai sai ya ga babban taro yana zuwa wurinsa, sai ya ce ma Filibus, “Ina za mu sayi gurasar da Mutanen nan za su ci?”
6 (And this he said to prove him: for he himself knew what he would do.)
( Ya fadi haka ne domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.)
7 Philip answered him, Two hundred penny-worth of bread is not sufficient for them, that every one of them make take a little:
Filibus ya amsa masa, “gurasar dinari biyu ma ba zata ishi kowannensu ya samu ko kadan ba.”
8 One of his disciples, Andrew, Simon Peter's brother, saith to him,
Daya daga cikin almajiransa, wato Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus, ya ce masa,
9 There is a lad here, who hath five barley-loaves, and two small fishes: but what are they among so many?
“Ga wani dan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu. Amma menene wadannan za su yi wa mutane masu yawa?”
10 And Jesus said, Make the men sit down. (Now there was much grass in the place.) So the men sat down in number about five thousand.
Yesu ya ce, “ku sa mutane su zauna.”( wurin kuwa akwai ciyawa.) Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar.
11 And Jesus took the loaves; and when he had given thanks, he distributed to the disciples, and the disciples to them that were set down; and likewise of the fishes, as much as they would.
Sai Yesu ya dauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa wadanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin gwargwadon abin da zai ishe su.
12 When they were satisfied, he said to his disciples, Gather the fragments that remain, that nothing may be lost.
Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara.”
13 Therefore they gathered [them], and filled twelve baskets with the fragments of the five barley-loaves, which remained over and above to them that had eaten.
Sai suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci.
14 Then those men, when they had seen the miracle that Jesus performed, said, This is truly that prophet that should come into the world.
Da jama'a suka ga alamar da ya yi, sai suka ce, “Hakika wannan shi ne annabin nan mai zuwa cikin duniya.
15 When Jesus therefore perceived that they would come and take him by force, to make him a king, he departed again to a mountain himself alone.
“Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su dauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen da kansa.
16 And when evening had [now] come, his disciples went down to the sea,
Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.
17 And entered into a boat, and went over the sea towards Capernaum. And it was now dark, and Jesus had not come to them.
Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.)
18 And the sea arose by reason of a great wind that blew.
Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa.
19 So when they had rowed about five and twenty or thirty furlongs, they see Jesus walking on the sea, and drawing nigh to the boat: and they were afraid.
Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita.
20 But he saith to them, It is I; be not afraid.
Amma ya ce masu, “Ni ne! kada ku firgita.”
21 Then they willingly received him into the boat: and immediately the boat was at the land whither they were going.
Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci.
22 The day following, when the people who stood on the other side of the sea saw that there was no other boat there, save that one into which his disciples had entered, and that Jesus went not with his disciples into the boat, but [that] his disciples had gone away alone;
Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai.
23 (Yet there came other boats from Tiberias nigh to the place where they ate bread, after the Lord had given thanks: )
Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya.
24 When the people therefore saw that Jesus was not there, neither his disciples, they also took boats, and came to Capernaum, seeking for Jesus.
Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
25 And when they had found him on the other side of the sea, they said to him, Rabbi, when camest thou hither?
Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Mallam, yaushe ka zo nan?”
26 Jesus answered them and said, Verily, verily, I say to you, Ye seek me, not because ye saw the miracles, but because ye ate of the loaves, and were satisfied.
Yesu ya amsa masu, da cewa, “hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi.
27 Labor not for the food which perisheth, but for that food which endureth to everlasting life, which the Son of man will give to you: for him hath God the Father sealed. (aiōnios )
Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa.” (aiōnios )
28 Then said they to him, What shall we do, that we may work the works of God?
Sai suka ce Masa, “Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah?
29 Jesus answered and said to them, This is the work of God, that ye believe on him whom he hath sent.
Yesu ya amsa, “Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko.”
30 They said therefore to him, What sign showest thou then, that we may see, and believe thee? what dost thou work?
Sai suka ce masa, “To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka?
31 Our fathers ate manna in the desert; as it is written, He gave them bread from heaven to eat.
Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, “Ya ba su gurasa daga sama su ci.”
32 Then Jesus said to them, Verily, verily, I say to you, Moses gave you not that bread from heaven; but my Father giveth you the true bread from heaven.
Sa'an nan Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama.
33 For the bread of God is he who cometh down from heaven, and giveth life to the world.
Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya,”
34 Then said they to him, Lord, evermore give us this bread.
Sai suka ce masa, “Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe.”
35 And Jesus said to them, I am the bread of life: he that cometh to me, shall never hunger; and he that believeth on me, shall never thirst.
Yesu ya ce masu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba.
36 But I said to you, That ye also have seen me, and believe not.
Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.
37 All that the Father giveth me, shall come to me; and him that cometh to me, I will in no wise reject.
Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan.
38 For I came down from heaven, not to do my own will, but the will of him that sent me.
Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
39 And this is the Father's will who hath sent me, that of all which he hath given me, I should lose nothing, but should raise it up again at the last day.
Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe.
40 And this is the will of him that sent me, that every one who seeth the Son, and believeth on him, may have everlasting life: and I will raise him up at the last day. (aiōnios )
Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe. (aiōnios )
41 The Jews then murmured at him, because he said, I am the bread which came down from heaven.
Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, “Nine Gurasar da ta sauko daga sama.”
42 And they said, Is not this Jesus the son of Joseph, whose father and mother we know? how is it then that he saith, I came down from heaven?
Suka ce, “Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'?
43 Jesus therefore answered and said to them, Murmur not among yourselves.
Yesu ya amsa, ya ce masu, “Kada ku yi gunaguni a junanku.
44 No man can come to me, except the Father who hath sent me draw him: and I will raise him up at the last day.
Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe.
45 It is written in the prophets, And they shall be all taught from God. Every man therefore that hath heard, and hath learned from the Father, cometh to me.
A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni.
46 Not that any man hath seen the Father, save he who is from God, he hath seen the Father.
Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban.
47 Verily, verily, I say to you, He that believeth on me hath everlasting life. (aiōnios )
Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami. (aiōnios )
48 I am that bread of life.
Ni ne Gurasa ta rai.
49 Your fathers ate manna in the wilderness, and are dead.
Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu.
50 This is the bread which cometh down from heaven, that a man may eat of it, and not die.
Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba.
51 I am the living bread which came down from heaven: if any man shall eat of this bread, he shall live for ever: and the bread that I will give is my flesh, which I will give for the life of the world. (aiōn )
Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya.” (aiōn )
52 The Jews therefore contended among themselves, saying, How can this man give us [his] flesh to eat?
Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, “Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci?
53 Then Jesus said to them, Verily, verily, I say to you, Except ye eat the flesh of the Son of man, and drink his blood, ye have no life in you.
Sai Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba.
54 Whoever eateth my flesh, and drinketh my blood, hath eternal life; and I will raise him up at the last day. (aiōnios )
Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe. (aiōnios )
55 For my flesh is food indeed, and my blood is drink indeed.
Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
56 He that eateth my flesh, and drinketh my blood, dwelleth in me, and I in him.
Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa.
57 As the living Father hath sent me, and I live by the Father: so he that eateth me, even he shall live by me.
Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni.
58 This is that bread which came down from heaven: not as your fathers ate manna, and are dead: he that eateth of this bread shall live for ever. (aiōn )
Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama, ba irin wadda Ubanninku suka ci suka mutu ba. Dukan wanda ya ci gurasar zai rayu har abada.” (aiōn )
59 These things he said in the synagogue, as he taught in Capernaum.
Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.
60 Many therefore of his disciples, when they had heard [this], said, This is a hard saying; who can hear it?
Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?”
61 When Jesus knew in himself that his disciples murmured at it, he said to them, Doth this offend you?
Yesu, kuwa da yake ya sani a ransa da cewa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce masu, “Wannan ya zamar maku laifi?
62 [What] if ye shall see the Son of man ascend up where he was before?
Yaya Ke nan in kun ga Dan Mutum yana hawa inda yake a da?
63 It is the spirit that reviveth; the flesh profiteth nothing: the words that I speak to you, [they] are spirit, and [they] are life.
Ruhu shine mai bayar da rai; Jiki ba ya amfana komai. Kalmomin da na fada maku ruhu ne, da kuma rai.
64 But there are some of you that believe not. For Jesus knew from the beginning who they were that believed not, and who he was that would betray him.
Amma fa akwai wadansun ku da ba su ba da gaskiya ba. Domin tun farko Yesu ya san wadanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi.
65 And he said, Therefore I said to you, that no man can come to me, except it were given to him by my Father.
Ya fada cewa, “shiyasa na gaya maku, ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban.”
66 From that [time] many of his disciples went back, and walked no more with him.
Bayan haka, da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su kara tafiya tare da shi ba.
67 Then said Jesus to the twelve, Will ye also go away?
Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “ku ba kwa so ku tafi, ko ba haka ba?
68 Then Simon Peter answered him, Lord, to whom shall we go? thou hast the words of eternal life. (aiōnios )
Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? kai kake da maganar rai madawwami. (aiōnios )
69 And we believe, and are sure that thou art that Christ, the Son of the living God.
Mu kwa mun gaskata mun kuma sani kai ne mai tsarkin nan na Allah.”
70 Jesus answered them, Have not I chosen you twelve, and one of you is a devil?
Yesu ya ce masu, “Ba ni na zabe ku, goma sha biyu ba, amma dayanku Iblis ne?”
71 He spoke of Judas Iscariot [the son] of Simon: for it was he that was to betray him, being one of the twelve.
Wato yana magana akan Yahuda dan Siman Iskariyoti, shi kuwa daya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu.