< 2 Corinthians 13 >
1 This [is] the third [time] I am coming to you: By the mouth of two or three witnesses shall every word be established.
Wannan ne karo na uku da nake zuwa gare ku, ''Ana tabbatar da kowanne zargi ta bakin shaidu biyu ko uku.''
2 I told you before, and foretell you, as if I were present, the second time; and being absent now I write to them who heretofore have sinned, and to all others, that, if I come again, I will not spare;
Na riga na yi magana a baya da wadanda suka yi zunubi da kuma sauran a lokacin da ina tare da ku karo na biyu, kuma ina sake fadi: Idan na sake zuwa, ba zan raga masu ba.
3 Since ye seek a proof of Christ speaking in me, who toward you is not weak, but is mighty in you.
Ina fadi maku wannan ne domin kuna neman shaida ko Almasihu na magana ta bakina. Shi ba kasashshe bane zuwa gare ku. Maimakon haka, Shi mai iko ne a cikin ku.
4 For though he was crucified through weakness, yet he liveth by the power of God. For we also are weak in him, but we shall live with him by the power of God towards you.
Domin an gicciye shi cikin kasawa, amma yana da rai ta ikon Allah. Don mu ma kasassu ne a cikin shi, amma za mu rayu tare da shi cikin ikon Allah dake cikinku.
5 Examine yourselves, whether ye are in the faith; prove your own selves. Know ye not your own selves, that Jesus Christ is in you, except ye are reprobates?
Ku auna kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya. Ku yi wa kanku gwaji. Ba ku lura da cewa Yesu Almasihu yana cikin ku ba? Yana cikin ku, sai dai in ba a amince da ku ba.
6 But I trust that ye will know that we are not reprobates.
Gama ina da gabagadin cewa za ku iske an amince da mu.
7 Now I pray to God that ye do no evil; not that we should appear approved, but that ye should do that which is honest, though we should be as reprobates.
Ina addu'a ga Allah cewa ba za a same ku da laifi ba. Ba wai ina rokon mu bayyana kamar mun ci gwadawar ba. Maimakon haka, ina addu'a ku yi abinda ke dai dai, ko dayake mun yi kamar mun fadi gwadawar.
8 For we can do nothing against the truth, but for the truth.
Domin bamu iya yin wani abu na tsayayya da gaskiya ba, sai dai mu yi domin gaskiya.
9 For we are glad, when we are weak, and ye are strong: and this also we wish, [even] your perfection.
Muna farin ciki idan mun kasa ku kuma kun yi karfi. Muna addu'a kuma domin ku kammalu.
10 Therefore I write these things being absent, lest being present I should use sharpness, according to the power which the Lord hath given me to edification, and not to destruction.
Na rubuta wadannan abubuwa yayinda ba ni tare da ku, saboda yayin da zan kasance da ku ba zan zamar maku mai fada ba. Ba na so inyi amfani da ikon da Ubangiji ya bani in tsattsaga ku, sai dai in gina ku.
11 Finally, brethren, farewell. Be perfect, be of good comfort, be of one mind, live in peace; and the God of love and peace will be with you.
A karshe, 'yan'uwa, ku yi farinciki, ku yi aiki don sabuntuwa, ku karfafa, ku yarda da juna, ku zauna cikin salama. Kuma Allahn kauna da salama zai kasance tare da ku.
12 Greet one another with a holy kiss.
Ku gai da juna da tsattsarkar sumba.
13 All the saints salute you.
Masu bi duka suna gaishe ku.
14 The grace of the Lord Jesus Christ, and the love of God, and the communion of the Holy Spirit, [be] with you all. Amen.
Bari alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.