< 1 Peter 2 >
1 Wherefore, laying aside all malice, and all guile, and hypocrisies, and envies, and all evil-speakings,
Saboda haka sai ku tube dukkan keta, rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance.
2 As new-born babes, desire the pure milk of the word, that ye may grow thereby:
Kammar jarirai, sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara mai ruhaniya wadda take sahihiya, domin ta wurinta kuyi girma zuwa ceto,
3 If indeed ye have tasted that the Lord [is] gracious.
idan kun dandana Ubangiji mai-alheri ne.
4 To whom coming [as to] a living stone, disallowed indeed by men, but chosen by God, [and] precious,
Kuzo gareshi rayayyen dutse wanda mutane suka ki, amma zababbe ne mai-daraja wurin Allah.
5 Ye also, as living stones, are built up a spiritual house, a holy priesthood, to offer up spiritual sacrifices, acceptable to God by Jesus Christ.
Ku kuma kamar rayayyun duwatsu ana gina ku gida mai ruhaniya, domin ku zama tsarka-kan fristoci, domin ku mika hadayu masu ruhaniya abin karba ga Allah ta wurin Yesu Almasihu.
6 Wherefore also it is contained in the scripture, Behold, I lay in Sion a chief corner-stone, elect, precious: and he that believeth on him shall not be confounded.
Gama nassi ya ce, “Ga shi na sanya dutse na kan kusurwa, zababe, mai daraja a cikin Sihiyona. Duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zaya kunyata ba.”
7 To you therefore who believe [he is] precious: but to them who are disobedient, the stone which the builders disallowed, the same is made the head of the corner,
Daraja a gareku take ku da kun bada gaskiya. Amma, ga wadanda suka ki bada gaskiya, “Dutsen da magina suka ki shine aka mai she shi kan kusurwa”.
8 And a stone of stumbling, and a rock of offense, [even to them] who stumble at the word, being disobedient: to which also they were appointed.
kuma, “Dutsen sa tuntube da fa na sa tuntube. “Sun yi tuntube, da shike sun ki biyayya da maganar, an kuwa kaddara su ga wannan.
9 But ye [are] a chosen generation, a royal priesthood, a holy nation, a peculiar people; that ye should show forth the praises of him who hath called you out of darkness into his marvelous light:
Amma ku zababben jinsi ne, kungiyar fristoci ba-sarauci, al'umma mai-tsarki, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wanda ya kiraye ku daga chikin duhu zuwa cikin haskensa mai'ban al'ajibi.
10 Who in time past [were] not a people, but [are] now the people of God: who had not obtained mercy, but now have obtained mercy.
Ku da ba jama'a ba ne a da, amma yanzu jama'ar Allah ne. Da baku sami jinkai ba, amma yanzu kun sami jinkai.
11 Dearly beloved, I beseech [you] as strangers and pilgrims, abstain from fleshly lusts, which war against the soul;
Kaunatattu, ina rokon ku misalin baki da masu-tafiya kuma, ku guje wa sha'awoyin jiki wadanda ke yaki da rai.
12 Having your manner of life honest among the Gentiles: that, whereas they speak against you as evil-doers, they may by [your] good works, which they shall behold, glorify God in the day of visitation.
Ku kasance da kyakkyawan hali a cikin al'ummai, domin, sa'adda suke kushen ku kamar masu aikata mugunta, sai su lura da nagargarun ayyukanku su kuma daukaka Allah a ranar zuwansa.
13 Submit yourselves to every ordinance of man for the Lord's sake: whether to the king, as supreme;
Kuyi biyayya ga kowacce hukuma ta mutane sabili da Ubangiji, ko ga sarki domin shi ne shugaba.
14 Or to governors, as to them that are sent by him for the punishment of evil-doers, and for the praise of them that do well.
Ko kuwa ga masu mulki aikakkunsa ne domin su hori masu aikata mugunta da yabawa masu aikata nagarta.
15 For so is the will of God, that with well-doing ye may put to silence the ignorance of foolish men:
Gama wannan nufin Allah ne, ta wurin aikin kirki ku, kwabi jahilcin mutane marassa hikima.
16 As free, and not using [your] liberty for a cloke of maliciousness, but as the servants of God.
Kamar 'yan'tattu kada ku mori 'yan'cinku kamar mayafin mugunta, amma ku zama kamar bayin Allah.
17 Honor all [men]. Love the brotherhood. Fear God. Honor the king.
Ku girmama dukkan mutane. Ku kaunaci 'yan'uwa, kuji tsoron Allah. Ku girmama sarki.
18 Servants, [be] subject to [your] masters with all fear; not only to the good and gentle, but also to the froward.
Ku barori, kuyi biyayya ga iyayen gidanku da dukkan bangirma, ba ga nagargaru da masu saukin kai ba, amma har ga miskilai.
19 For this [is] thank-worthy, if a man for conscience towards God endureth grief, suffering wrongfully.
Gama abin yaba wa ne idan sabili da lamiri zuwa ga Allah in wani ya jimre da shan zalunci.
20 For what glory [is it], if, when ye are buffeted for your faults, ye bear it patiently? but if, when ye do well, and suffer [for it], ye bear it patiently, this [is] acceptable with God.
Gama wacce riba ke nan idan kun yi zunubi ana horonku kuna jimrewa da hukuncin? amma idan kunyi aikin kirki kuka sha wuya a kansa kuka yi hakuri, wannan abin karba ne wurin Allah.
21 For even to this were ye called: because Christ also suffered for us, leaving us an example, that ye should follow his steps:
Gama akan haka aka kiraye ku, gama Almasihu ma yasha azaba saboda ku, ya bar maku gurbi kubi sawunsa.
22 Who committed no sin, neither was guile found in his mouth:
Bai taba yin zunubi ba, ba'a taba jin yaudara a bakinsa ba.
23 Who, when he was reviled, reviled not again; when he suffered, he threatened not; but committed [himself] to him that judgeth righteously:
Da'a ka zage shi bai mai da zagi ba. Da ya sha azaba, bai yi kashedi ba, amma ya mika kansa ga wanda yake yin shari'ar adalci.
24 Who himself bore our sins in his own body on the tree, that we, being dead to sins, should live to righteousness; by whose stripes ye were healed.
Shi da kansa ya dauki zunubanmu a cikin jiki nasa ya kai su bisa itace, domin kada a iske mu cikin zunubi, amma muyi rayuwa ga adalci. Ta wurin raunukansa ne kuka warke.
25 For ye were as sheep going astray; but are now returned to the Shepherd and Bishop of your souls.
Dukkanku da kun bata kuna yawo kamar batattun tumaki, amma yanzu kun dawo wurin makiyayi da mai tsaron rayukanku.