< Genesis 37 >

1 Jacob lived in the land where his father was staying, in the land of Canaan.
Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana.
2 These were the events concerning Jacob. Joseph, who was a young man seventeen years old, was guarding the flock with his brothers. He was with the sons of Bilhah and with the sons of Zilpah, his father's wives. Joseph brought an unfavorable report about them to their father.
Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da’yan’uwansa, wato,’ya’yan Bilha maza da kuma’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da’yan’uwansa.
3 Now Israel loved Joseph more than all his sons because he was the son of his old age. He made him a beautiful garment.
Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.
4 His brothers saw that their father loved him more than all his brothers. They hated him and would not speak kindly to him.
Sa’ad da’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
5 Joseph dreamed a dream, and he told his brothers about it. They hated him even more.
Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
6 He said to them, “Please listen to this dream which I dreamed.
Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi.
7 Behold, we were tying bundles of grain in the field and behold, my bundle rose and stood upright, and behold, your bundles came around and bowed down to my bundle.”
Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
8 His brothers said to him, “Will you really reign over us? Will you actually rule over us?” They hated him even more for his dreams and for his words.
Sai’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
9 He dreamed another dream and told it to his brothers. He said, “Look, I have dreamed another dream: The sun and the moon and eleven stars bowed down to me.”
Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
10 He told it to his father just as to his brothers, and his father rebuked him. He said to him, “What is this dream that you have dreamed? Will your mother and I and your brothers actually come to bow down to the ground to you?”
Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?”
11 His brothers were jealous of him, but his father kept the matter in mind.
’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
12 His brothers went to tend their father's flock in Shechem.
To,’yan’uwansa suka tafi kiwon garkunan mahaifinsu kusa da Shekem.
13 Israel said to Joseph, “Are not your brothers tending the flock in Shechem? Come, and I will send you to them.” Joseph said to him, “I am ready.”
Sai Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Kamar yadda ka sani,’yan’uwanka suna kiwon garkuna kusa da Shekem. Zo, in aike ka gare su.” Ya ce, “To.”
14 He said to him, “Go now, see whether it is well with your brothers and well with the flock, and bring me word.” So Jacob sent him out of the Valley of Hebron, and Joseph went to Shechem.
Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron. Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem,
15 A certain man found Joseph. Behold, Joseph was wandering in a field. The man asked him, “What do you seek?”
sai wani mutum ya same shi yana yawo a cikin jeji, sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”
16 Joseph said, “I am seeking my brothers. Tell me, please, where they are tending the flock.”
Yusuf ya amsa ya ce, “Ina neman’yan’uwana ne. Za ka iya faɗa mini inda suke kiwon garkunansu?”
17 The man said, “They left this place, for I heard them say, 'Let us go to Dothan.'” Joseph went after his brothers and found them at Dothan.
Mutumin ya amsa, “Sun yi gaba daga nan. Na ji su suna cewa, ‘Bari mu je Dotan.’” Saboda haka Yusuf ya bi bayan’yan’uwansa, ya kuwa same su kusa da Dotan.
18 They saw him from a distance, and before he came near to them, they plotted against him to kill him.
Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi.
19 His brothers said to one another, “Look, this dreamer is approaching.
Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa!
20 Come now, therefore, let us kill him and cast him into one of the pits. We will say, 'A wild animal has devoured him.' We will see what will become of his dreams.”
Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.”
21 Reuben heard it and rescued him from their hand. He said, “Let us not take his life.”
Sa’ad da Ruben ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă cece shi daga hannuwansu. Ya ce, “Kada mu ɗauki ransa.
22 Reuben said to them, “Shed no blood. Throw him into this pit that is in the wilderness, but lay no hand upon him”—that he might rescue him out of their hand to bring him back to his father.
Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa.
23 It came about that when Joseph reached his brothers, they stripped him of his beautiful garment.
Saboda haka sa’ad da Yusuf ya zo wurin’yan’uwansa, sai suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai gwanin kyau da ya sa,
24 They took him and threw him into the pit. The pit was empty with no water in it.
suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki.
25 They sat down to eat bread. They lifted up their eyes and looked, and, behold, a caravan of Ishmaelites was coming from Gilead, with their camels bearing spices and balm and myrrh. They were traveling to carry them down to Egypt.
Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.
26 Judah said to his brothers, “What profit is it if we kill our brother and cover up his blood?
Yahuda ya ce wa’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa?
27 Come, and let us sell him to the Ishmaelites and not lay our hands upon him. For he is our brother, our flesh.” His brothers listened to him.
Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai’yan’uwansa suka yarda.
28 The Midianite merchants passed by. His brothers drew Joseph up and lifted him up out of the pit. They sold Joseph to the Ishmaelites for twenty pieces of silver. The Ishmaelites carried Joseph into Egypt.
Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
29 Reuben returned to the pit, and, behold, Joseph was not in the pit. He tore his clothes.
Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa.
30 He returned to his brothers and said, “The boy is not there! And I, where can I go?”
Ya koma wurin’yan’uwansa ya ce, “Yaron ba ya can! Ina zan bi yanzu?”
31 They slaughtered a goat and then took Joseph's garment and dipped it into the blood.
Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin.
32 Then they brought it to their father and said, “We found this. Please see whether it is your son's clothing or not.”
Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.”
33 Jacob recognized it and said, “It is my son's clothing. A wild animal has devoured him. Joseph has certainly been torn to pieces.”
Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”
34 Jacob tore his garments and put sackcloth upon his loins. He mourned for his son many days.
Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa.
35 All his sons and daughters rose up to comfort him, but he refused to be comforted. He said, “Indeed I will go down to Sheol mourning for my son.” His father wept for him. (Sheol h7585)
Dukan’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi. (Sheol h7585)
36 The Midianites sold him in Egypt to Potiphar, an officer of Pharaoh, the captain of the bodyguard.
Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin’yan gadin fadar Fir’auna.

< Genesis 37 >