< Ezra 6 >
1 So King Darius ordered an investigation in the house of archives in Babylon.
Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon.
2 In the fortified city of Ecbatana in Media a scroll was found; this was its record:
Sai aka sami takarda a Ekbatana a yankin Mediya, ga kuma abin da yake rubuce a ciki. Abin tunawa.
3 “In the first year of King Cyrus, Cyrus issued a decree about the house of God in Jerusalem: 'Let the house be rebuilt as a place for sacrifice, let its foundations be laid, let its height be sixty cubits, and its width sixty cubits,
A shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus, sarki ya ba da umarni game da haikalin Allah a Urushalima, ya ce, Bari a sāke gina haikalin yă zama wurin miƙa hadayu, a kuma aza harsashin ginin haikalin. Tsayinsa zai zama ƙafa tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tasa’in.
4 with three rows of large stones and a row of new timber, and let the cost be paid by the king's house.
Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako. Daga asusun sarki kuma za a biya kuɗin aikin.
5 Now bring back the gold and silver objects belonging to the house of God, which Nebuchadnezzar brought to Babylon from the temple in Jerusalem and send them back to the temple in Jerusalem. You are to put them in the house of God.'
Kwanonin zinariya da na azurfan gidan Allah waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga haikali a Urushalima ya kawo Babilon, a mayar da su wurinsu a haikali a Urushalima; a sa su cikin gidan Allah.
6 Now Tattenai, the governor of the Province Beyond the River, Shethar-Bozenai, and associates who are in the Province Beyond the River, keep away!
Saboda haka Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai, da ku masu muƙami na yankin, ku bar wurin.
7 Leave the work of this house of God alone. The governor and Jewish elders will build this house of God at that place.
Kada ku hana wannan aiki na haikalin Allah. Bari gwamnan Yahudawa, da dattawan Yahudawa su sāke gina wannan gidan Allah a wurin da yake a dā.
8 I am ordering that you must do this for these Jewish elders who build this house of God: Funds from the king's tribute beyond the River will be used to pay these men so they do not have to stop their work.
Na kuma ba da umarni game da abin da za ku yi wa dattawan Yahudawa cikin aikin ginin wannan gidan Allah. Daga asusun sarki a kuɗin da yake shigo wa Kewayen Kogin Yuferites za a biya mutanen nan duka, domin kada aikin yă tsaya.
9 Whatever is needed—young bulls, rams, or lambs for the burnt offerings to the God of Heaven, grain, salt, wine, or oil according to the command of the priests in Jerusalem—give these things to them every day without fail.
A tanada musu duk abin da suke bukata. A ba su’yan bijimai, da raguna, da’yan tumaki domin miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na sama, haka kuma dole a tanada wa firistoci alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da mai, kullum ba fasawa yadda firistoci suke yi a Urushalima
10 Do this so they will bring the offering in to the God of Heaven and pray for me, the king, and my sons.
domin su miƙa hadayu masu daɗi ga Allah na Sama, su kuma yi addu’a domin lafiyar sarki da’ya’yansa.
11 I am ordering that if anyone violates this decree, a beam must be pulled from his house and he must be impaled on it. His house must then be turned into a rubbish heap because of this.
Na kuma yi umarni cewa duk wanda ya karya wannan doka sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa’an nan a mai da gidansa juji.
12 May the God who has caused his name to dwell there overthrow any king or people who lifts a hand to change this decree, or to destroy this house of God in Jerusalem. I, Darius, am ordering this. Let it be done with diligence!”
Bari Allah yă sa sunansa yă kasance, yă hamɓarar da duka wani sarki ko mutanen da za su sa hannu don a sāke wannan doka, ko kuma don su rushe haikalin nan a Urushalima. Ni Dariyus na ba da wannan umarni, bari a yi biyayya babu wasa.
13 Then because of the decree sent by Darius the king, Tattenai, the governor of the Province Beyond the River, and Shethar-Bozenai and his associates, did everything that King Darius had ordered.
Saboda umarnin da sarki Dariyus ya aika, sai Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites da Shetar-Bozenai da abokansu suka yi biyayya da umarnin babu wasa.
14 So the Jewish elders built and prospered under the teaching of Haggaithe prophet and Zechariah son of Iddo. They completed their buildings according to the decree of the God of Israel and by the decree of Cyrus, Darius, and Artaxerxes the king of Persia.
Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.
15 The house was completed on the third day of the month of Adar, in the sixth year of King Darius' reign.
An gama ginin haikalin a rana ta uku na watan Adar a shekara ta shida ta mulkin Sarki Dariyus.
16 The Israelite people, priests, Levites, and the rest of the captives celebrated the dedication of this house of God with joy.
Sai mutanen Isra’ila, firistoci, Lawiyawa da kuma sauran waɗanda suka dawo daga bauta suka yi bikin keɓe gidan Allah, cike da farin ciki.
17 They offered one hundred bulls, one hundred rams, and four hundred lambs for the dedication of God's house. Twelve male goats were also offered as a sin offering for all Israel, one for each tribe in Israel.
Suka miƙa bijimai guda ɗari, da raguna ɗari biyu, da’yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, suka kuma miƙa bunsurai guda goma sha biyu don hadaya ta zunubi, kowane bunsuru ɗaya don kowace kabila ta Isra’ila.
18 They also assigned the priests and Levites to work divisions for the service of God in Jerusalem, as it was written in the Book of Moses.
Suka kuma naɗa firistoci a gundumominsu da kuma Lawiyawa a ƙungiyoyinsu don hidimar Allah a Urushalima, bisa ga abin da aka rubuta a Littafin Musa.
19 So those who had been in exile celebrated the Passover on the fourteenth day of the first month.
A rana ta goma sha huɗu ga watan farko, sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi Bikin Ƙetarewa.
20 The priests and Levites all purified themselves and slaughtered the Passover sacrifices for all those who had been in exile, including themselves.
Firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka zama da tsabta. Lawiyawa suka yanka ragon Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda suka dawo daga bauta, da kuma domin’yan’uwansu firistoci, da kuma domin kansu.
21 The Israelite people who ate some of the Passover meat were those who had returned from exile and had separated themselves from the uncleanness of the people of the land and sought Yahweh, the God of Israel.
Sai Isra’ilawa waɗanda suka dawo daga bauta suka ci tare da duk waɗanda suka keɓe kansu daga halin ƙazanta na Al’ummai maƙwabtansu, don su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
22 They joyfully celebrated the Festival of Unleavened Bread for seven days, for Yahweh had brought them joy and turned the heart of Assyria's king to strengthen their hands in the work of his house, the house of the God of Israel.
Suka yi kwana bakwai suna Bikin Burodi Marar Yisti, suna cike da farin ciki, gama Ubangiji ya cika su da farin ciki don ya sa sarkin Assuriya ya canja tunaninsa, ya taimake su cikin aikin gidan Allah, Allah na Isra’ila.