< Acts 9 >
1 Meanwhile Saul, still breathing murderous threats against the disciples of the Lord, went to the High Priest,
Amma Shawulu, ya cigaba da maganganun tsoratarwa har ma da na kisa ga almajiran Ubangiji, ya tafi wurin babban firist
2 and asked him to give him letters to the Jewish congregations at Damascus, authorising him, if he found there any supporters of the Cause, whether men or women, to have them put in chains and brought to Jerusalem.
kuma ya roke shi wasiku zuwaga majami'un da ke Dimashku, domin idan ya sami wani da ke na wannan hanya, maza ko mata, ya kawo su Urushalima a daure.
3 While on his journey, as he was nearing Damascus, suddenly a light from the heavens flashed around him.
Yayin da yana tafiya, ya kasance da ya iso kusa da Dimashku, nan da nan sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi;
4 He fell to the ground and heard a voice saying to him — “Saul, Saul, why are you persecuting me?”
Sai ya fadi a kasa kuma yaji wata murya na ce da shi, ''Shawulu, Shawulu, me yasa kake tsananta mani?''
5 “Who are you, Lord?” he asked. “I am Jesus, whom you are persecuting,” the voice answered;
Shawulu ya amsa, ''Wanene kai, Ubangiji?'' Ubangiji ya ce, ''Nine Yesu wanda kake tsanantawa;
6 “Yet stand up and go into the city, and you will be told what you must do.”
amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi.
7 The men traveling with Saul were meanwhile standing speechless; they heard the sound of the voice, but saw no one.
Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba.
8 When Saul got up from the ground, though his eyes were open, he could see nothing. So his men led him by the hand, and brought him into Damascus;
Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku.
9 and for three days he was unable to see, and took nothing either to eat or to drink.
Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha.
10 Now there was at Damascus a disciple named Ananias, to whom, in a vision, the Lord said: “Ananias.” “Yes, Lord,” he answered.
Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, ''Hananiya.'' Sai ya ce, ''Duba, gani nan Ubangiji.''
11 “Go at once,” said the Lord, “to the ‘Straight Street’, and ask at Judas’s house for a man named Saul, from Tarsus. He is at this moment praying,
Ubangiji ya ce masa, ''Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a;
12 and he has seen, in a vision, a man named Ananias coming in and placing his hands on him, so that he may recover his sight.”
kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude.''
13 “Lord,” exclaimed Ananias, “I have heard from many people about this man — how much harm he has done at Jerusalem to your People there.
Amma Hananiya ya amsa, ''Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima.
14 And, here, too, he holds authority from the Chief Priests to put in chains all those who invoke your Name.”
An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka.''
15 But the Lord said to him: “Go, for this man is my chosen instrument to uphold my Name before the Gentiles and their kings, and the people of Israel.
Amma Ubangiji ya ce masa, ''Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila;
16 I will myself show him all that he has to suffer for my Name.”
Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana.''
17 So Ananias went, entered the house, and, placing his hands on Saul, said: “Saul, my Brother, I have been sent by the Lord — by Jesus, who appeared to you on your way here — so that you may recover your sight and be filled with the Holy Spirit.”
Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, ''Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki.''
18 Instantly it seemed as if a film fell from Saul’s eyes, and his sight was restored. Then he got up and was baptized,
Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma;
19 and, after he had taken food, he felt his strength return. Saul stayed for some days with the disciples who were at Damascus,
kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa.
20 and at once began in the Synagogues to proclaim Jesus as the Son of God.
Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah.
21 All who heard him were amazed. “Is not this,” they asked, “the man who worked havoc in Jerusalem among those that invoke this Name, and who had also come here for the express purpose of having such persons put in chains and taken before the Chief Priests?”
Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce ''Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci.''
22 Saul’s influence, however, kept steadily increasing, and he confounded the Jews who lived in Damascus by the proofs that he gave that Jesus was the Christ.
Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu.
23 After some time the Jews laid a plot to kill Saul,
Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi.
24 but it became known to him. They even watched the gates day and night, to kill him;
Amma shirin su ya zama sananne ga Shawulu. Suna fakkon sa ta wurin tsaron kofar birnin dare da rana domin su kashe shi.
25 but his disciples let him down by night through an opening in the wall, lowering him in a basket.
Amma da tsakar dare almajiransa suka daukeshi a kwando, suka zurara shi ta katanga.
26 On his arrival in Jerusalem, Saul attempted to join the disciples, but they were all afraid of him, as they did not believe that he was really a disciple.
Sa'adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba.
27 Barnabas, however, taking him by the hand, brought him to the Apostles, and told them the whole story of how Saul on his journey had seen the Lord, and how the Lord had talked to him, and how in Damascus he had spoken out fearlessly in the Name of Jesus.
Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku.
28 After that, Saul remained in Jerusalem, in close intercourse with the Apostles; and he spoke fearlessly in the Name of the Lord,
Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu
29 talking and arguing with the Jews of foreign birth, who, however, made attempts to kill him.
kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi.
30 But, when the Brethren found this out, they took him down to Caesarea, and sent him on his way to Tarsus.
Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus.
31 And so it came about that the Church, throughout Judea, Galilee, and Samaria, enjoyed peace and became firmly established; and, ordering its life by reverence for the Lord and the help of the Holy Spirit, it increased in numbers.
Sa'annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta'aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane.
32 Peter, while traveling from place to place throughout the country, went down to visit the People of Christ living at Lydda.
Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda.
33 There he found a man named Aeneas, who had been bed-ridden for eight years with paralysis.
A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado.
34 “Aeneas,” Peter said to him, “Jesus Christ cures you. Get up, and make your bed.” Aeneas got up at once;
Bitrus ya ce masa, ''Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka.'' Nan take sai ya mike.
35 and all the inhabitants of Lydda and of the Plain of Sharon saw him, and came over to the Lord’s side.
Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji.
36 At Jaffa there lived a disciple whose name was Tabitha, which is in Greek ‘Dorcas’ — a Gazelle. Her life was spent in doing kind and charitable actions.
Yanzu kuwa a Yafa akwai wata almajira, mai suna Tabita, ma'ana ''Dokas.'' Wannan matar kuwa tana chike da ayyukan nagarta da halin tausayi da take yi ga mabukata.
37 Just at that time she was taken ill, and died; and they had washed her body and laid it out in an upstairs room.
Ya kai ga cewa a kwanakin can ta yi rashin lafiya har ta mutu; da suka wanke gawar ta suka kwantar da ita a bene.
38 Jaffa was near Lydda, and the disciples, having heard that Peter was at Lydda, sent two men with the request that he would come on to them without delay.
Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, ''Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba.''
39 Peter returned with them at once. On his arrival, he was taken upstairs, and all the widows came round him in tears, showing the coats and other clothing which Dorcas had made while she was among them.
Bitrus ya tashi ya tafi da su, da isowar sa, suka kai shi benen. Sai dukan gwamrayen suka tsaya kusa da shi suna kuka, sai suka dauko riguna da sutura da Dokas ta dinka lokacin da take tare da su.
40 But Peter sent everybody out of the room, and knelt down and prayed. Then, turning to the body, he said: “Tabitha! stand up.” She opened her eyes, and, seeing Peter, sat up.
Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu'a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, ''Tabita, tashi.'' Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna,
41 Giving her his hand, Peter raised her up, and, calling in the widows and others of Christ’s People, presented her to them alive.
Bitrus kuwa ya mika hannunsa ya tashe ta; sa'annan ya kira masu bi da gwamrayen, ya mika ta a raye garesu.
42 This became known all through Jaffa, and numbers of People came to believe in the Lord.
Wannan al'amari ya zama sananne cikin dukan Yafa, kuma mutane da yawa suka bada gaskiya ga Ubangiji.
43 And Peter stayed some days at Jaffa with a tanner named Simon.
Ya kasance, cewa, Bitrus ya zauna kwanaki da dama a Yafa tare da wani mutum mai suna Saminu, majemi.