< Revelation 15 >

1 Then I saw another great and marvelous sign in heaven: seven angels with the seven final plagues, because with them the wrath of God is completed.
Sai na ga wata alama cikin sama, babba mai ban mamaki: Akwai mala'iku bakwai rike da annobai bakwai, wadanda sune annobai na karshe domin da su ne fushin Allah zai cika.
2 I also saw something like a sea of glass mixed with fire, and those who had overcome the image, the beast himself, and the number of his name were standing by the sea of glass, holding the harps of God.
Na ga wani abin da da ya bayyana mai kama da tekun gilashi mai haske garwaye da wuta. Tsaye a gefen tekun sune wadanda suka ci nasara a kan dabban da siffarsa, da kuma lambar da ke wakiltar sunansa. Suna rike da molayen da Allah ya ba su.
3 They sang the song of Moses, the servant of God, and the song of the Lamb: “Great and marvelous are yoʋr works, O Lord God, the Almighty! Righteous and true are yoʋr ways, O King of the nations!
Suna rera wakar Musa, bawan Allah, da wakar Dan Rago: ''Ayyukan ka manya ne da ban mamaki, Ubangiji Allah, Mai iko duka. Adalci da gaskiya hanyoyinka ne, Sarkin al'ummai.
4 Who could not fear yoʋ, O Lord, and glorify yoʋr name? For yoʋ alone are holy. All will come and worship before yoʋ, for yoʋr righteous acts have been revealed.”
Wanene ba zai ji tsoron ka ba, Ubangiji, ya kuma daukaka sunanka? Domin kai kadai ne mai tsarki. Dukan al'ummai za su zo su yi sujada a gabanka domin an bayyana ayyukan ka na adalci.”
5 After this I looked, and the sanctuary of the tent of witness in heaven was opened,
Bayan wadannan abubuwa na duba, kuma aka bude haikalin alfarwar shaida a cikin sama.
6 and out came the seven angels with the seven plagues. They were clothed in pure bright linen, with golden sashes wrapped around their chests.
Daga wuri mafi tsarki mala'iku bakwai masu rike da annobai bakwai suka zo. Suna sanye da tufafi masu tsabta, da lallausar linin mai haske, suna kuma da damarar zinariya a kirjinsu.
7 Then one of the four living creatures gave the seven angels seven golden bowls full of the wrath of God, who lives forever and ever. (aiōn g165)
Daya daga cikin rayyayun halitu hudu ya ba mala'iku bakwai tasoshin zinariya bakwai cike da fushin Allah wanda yake raye har abada abadin. (aiōn g165)
8 And the temple was filled with the smoke from the glory of God and from his power, and no one could enter the temple until the seven plagues of the seven angels were completed.
Haikalin ya cika da hayaki daga daukakar Allah da kuma ikonsa. Ba wanda ya iya shigarsa har sai da annoban nan bakwai na mala'ikun nan bakwai suka cika.

< Revelation 15 >