< James 2 >
1 My brothers, practice your faith in our Lord Jesus Christ, the Lord of glory, without showing partiality.
Ya ku 'yan'uwana, muddin kuna rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijin daukaka, kada ku nuna bambanci ga wadansu mutane.
2 Suppose a man in fine clothing comes into your assembly wearing a gold ring, and a poor man in filthy clothing also comes in.
Idan wani mutum ya halarci taron ku da zobban zinariya da tufafi masu kyau, wani matalauci kuma ya shigo da tufafi marasa tsabta.
3 If you pay attention to the man who is wearing fine clothing and say to him, “Yoʋ sit here in a good place,” but you say to the poor man, “Yoʋ stand there, or sit here under my footstool,”
Sa'adda kuka kula da mai tufafi masu kyau nan, har kuka ce masa, “Idan ka yarda ka zauna a nan wuri mai kyau,'' mataulacin nan kuwa kuka ce masa, “Kai ka tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan kasa a gaba na,”
4 have you not made distinctions among yourselves and become judges with evil thoughts?
Ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mungayen tunani kenan ba?
5 Listen, my beloved brothers, has not God chosen the poor of the world to be rich in faith and heirs of the kingdom that he has promised to those who love him?
Ku saurara, ya 'yan'uwana kaunatattu, ashe, Allah bai zabi matalautan duniyar nan su zama mawadata cikin bangaskiya ba, su kuma zama magada a cikin mulkin nan da ya yi wa masu kaunar sa alkawari ba?
6 But you have dishonored the poor man. Is it not the rich who oppress you? Are they not the ones who drag you into court?
Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa maku ba? Ba su ne kuwa suke jan ku zuwa gaban shari'a ba?
7 Do they not blaspheme the good name by which you are called?
Ba kuma sune ke sabon sunan nan mai girma da ake kiran ku da shi ba?
8 If you really fulfill the royal law according to the Scripture, “Yoʋ shall love yoʋr neighbor as yoʋrself,” you do well.
Duk da haka, idan kuka cika muhimmiyar shari'ar da nassi ya ce, “Ka kaunaci makwabcin ka kamar kanka,” to, madalla.
9 But if you show partiality, you commit sin and are convicted by the law as transgressors.
Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi kenan, shari'a ta same ku da laifin keta umarni.
10 For whoever keeps the entire law but stumbles in one point has become guilty of it all.
Duk wanda yake kiyaye dukan shari'a, amma ya yi tuntube a hanya daya kadai, ya sabi shari'a gaba daya ke nan.
11 For he who said, “Yoʋ shall not commit adultery,” also said, “Yoʋ shall not murder.” Now if yoʋ do not commit adultery but do commit murder, yoʋ have become a transgressor of the law.
Domin wanda ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisan kai.” Idan ba ka yi zina ba amma ka yi kisan kai, ai, ka zama mai taka shari'a kenan.
12 Speak and act as those who will be judged by the law of liberty.
Saboda haka, ku yi magana ku kuma yi aiki kamar wadanda za a hukunta ta wurin 'yantacciyar shari'a.
13 For judgment is without mercy to anyone who has not shown mercy; mercy triumphs over judgment.
Gama hukunci yana zuwa ba tare da jinkai ba ga wadanda ba su nuna jinkai. Jinkai ya yi nasara a kan hukunci.
14 What is the benefit, my brothers, if someone says he has faith but does not have works? Can that faith save him?
Ina amfanin haka, 'yan'uwana, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka? Wannan bangaskiyar ba za ta cece shi ba, ko za ta iya?
15 If a brother or sister is poorly clothed and lacks daily food,
Misali, idan wani dan'uwa ko 'yar'uwa ba su da tufa mai kyau ko suna rashin abincin yini.
16 and one of you says to them, “Go in peace, be warmed and filled,” without giving them anything to address their physical needs, what is the benefit?
Misali, idan waninku kuma ya ce masu, “Ku tafi cikin salama, ku kasance da dumi ku koshi.” Idan baku ba su abubuwan da jiki ke bukata ba, ina amfanin wannnan?
17 In the same way faith by itself, if it does not have works, is dead.
Haka ma, bangaskiya ita kadai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, matacciya ce.
18 But someone will say, “Yoʋ have faith, and I have works.” Show me yoʋr faith by yoʋr works, and I, by my works, will show yoʋ my faith.
To, wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa ina da ayyuka.” Nuna mani bangaskiyar ka ba tare da ayyuka ba, ni kuma in nuna maka bangaskiya ta ta wurin ayyuka na.
19 Yoʋ believe that God is one; yoʋ do well. Even the demons believe—and shudder!
Ka gaskanta cewa Allah daya ne; ka yi daidai. Amma ko aljannu ma sun gaskata, kuma suna rawar jiki.
20 Do yoʋ want to be shown, O foolish man, that faith without works is dead?
Kana so ka sani, kai marar azanci, cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce?
21 Was not our father Abraham justified by works when he offered his son Isaac on the altar?
Ba an baratar da Ibrahim mahaifinmu ta wurin ayyuka ba, sa'adda ya mika Ishaku dansa a bisa bagadi?
22 Do yoʋ see how faith was active along with his works, and by works his faith was brought to completion?
Ka gani, ashe, bangaskiyar sa ta yi aiki da ayyukan sa, kuma da cewa ta wurin ayyuka bangaskiyar sa ta ginu sosai.
23 And the Scripture was fulfilled that says, “Abraham believed God, and it was counted to him as righteousness,” and he was called a friend of God.
Nassi kuma ya cika da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lisafta masa ita a matsayin adalci.” Aka kuma kira shi abokin Allah.
24 You see then that a person is justified by works, and not by faith alone.
Kun ga, ta wurin ayyuka ne mutum yake samu baratarwa ba ta wurin bangaskiya kadai ba.
25 In the same way, was not Rahab the prostitute also justified by works when she received the messengers and sent them out by another way?
Ta wannan hanyar kuma, ba Rahab karuwar nan ta samu baratarwa ta wurin ayyuka, da ta marabci masu leken asirin nan ta fitar da su ta wata hanya dabam ba?
26 For just as the body without the spirit is dead, so faith without works is also dead.
Kamar yadda jiki idan ba tare da ruhu ba matacce ne, haka kuma, bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.