< 2 Corinthians 4 >

1 Therefore, since we have this ministry through God's mercy, we do not lose heart.
Don haka, domin muna da wannan hidima, da kuma yadda muka karbi jinkai, ba mu karaya ba.
2 Rather, we have renounced shameful hidden deeds; we do not act deceitfully or distort the word of God, but by openly proclaiming the truth we commend ourselves to everyone's conscience in the sight of God.
Maimakon haka, sai muka rabu da dukan hanyoyin da ke na kunya, kuma na boye. Ba mu rayuwar makirci, kuma bamu yiwa maganar Allah rikon sakaci. Ta wurin gabatar da gaskiya, muna mika kanmu ga lamirin kowa a gaban Allah.
3 But even if our gospel is veiled, it is veiled among those who are perishing.
Amma, idan bishararmu a rufe take, tana rufe ne ga wadanda ke hallaka.
4 The god of this age has blinded the minds of unbelievers like them, so that the light of the gospel of the glory of Christ, who is the image of God, might not dawn upon them. (aiōn g165)
A al'amarinsu, allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya. A sakamakon haka, ba su iya ganin hasken bisharar daukakar Almasihu ba, wanda shine surar Allah. (aiōn g165)
5 For what we preach is not ourselves, but Christ Jesus as Lord, and ourselves as your servants for Jesus' sake.
Gama ba mu yin shelar kanmu, amma Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
6 For God, who commanded light to shine out of darkness, has shone in our hearts to give us the light of the knowledge of the glory of God in the face of Jesus Christ.
Gama Allah shine wanda ya ce, “Haske zai haskaka daga cikin duhu.” Ya haskaka cikin zukatanmu don ya bada hasken sanin daukakar Allah a gaban Yesu Almasihu.
7 But we have this treasure in jars of clay, to show that this extraordinary power is from God and not from us.
Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba.
8 We are afflicted in every way, but not crushed; perplexed, but not in despair;
Muna shan tsanani ta kowace hanya, ba a ci mu dungum ba. Mun rikice amma ba mu karaya ba, an tsananta mana amma ba a watsar da mu ba.
9 persecuted, but not forsaken; struck down, but not destroyed;
Ana tsananta mana amma ba a yashe mu ba. Aka doddoke mu amma ba mu lalace ba.
10 always carrying about in our bodies the death of the Lord Jesus, so that the life of Jesus may also be revealed in our bodies.
Mu dai a kullayaumin muna dauke da mutuwar Yesu a jikkunanmu, saboda a bayyana rayuwar Yesu a jikkunanmu kuma.
11 For we who live are always being delivered up to death for Jesus' sake, so that the life of Jesus may also be revealed in our mortal flesh.
Mu da muke a raye kuwa a kulluyaumin ana mika mu ga mutuwa saboda Yesu, domin rayuwar Yesu ta zama a bayyane a jikunanmu na mutuntaka.
12 So then, death is at work in us, but life is at work in you.
Saboda haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, amma rai na aiki a cikinku.
13 It is written, “I believed, therefore I spoke.” With that same spirit of faith we also believe, therefore we also speak.
Amma dai muna da wannan Ruhu na bangaskiya kammar yadda aka rubuta: “Na gaskata, saboda haka na furta.” Mu ma mun gaskata, haka kuwa muke fada.
14 For we know that he who raised the Lord Jesus will also raise us through Jesus and bring us with you into his presence.
Mun sani cewa wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu za ya sake tada mu tare da Yesu. Mun san cewa zai gabatar da mu tare da ku a gabansa.
15 All of this is for your benefit, so that grace, as it extends to more and more people, may cause thanksgiving to abound to the glory of God.
Dukan abubuwa sabili da ku suke domin, yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, bada godiya ta karu ga daukakar Allah.
16 Therefore we do not lose heart. Even though on the outside we are wasting away, on the inside we are being renewed day by day.
Don haka ba mu karaya ba. Kodashike daga waje muna lalacewa, daga ciki ana sabunta mu kulluyaumin.
17 For our light and momentary affliction is bringing about for us an eternal weight of glory far beyond all measure, (aiōnios g166)
Domin wannan 'yar wahala ta dan lokaci tana shirya mu zuwa ga nauyin madauwamiyar daukaka wadda ta wuce gaban aunawa. (aiōnios g166)
18 as we look not to what is seen, but to what is unseen. For what is seen is temporary, but what is unseen is eternal. (aiōnios g166)
Domin ba muna kallon abubuwan da ake gani bane, amma abubuwan da ba a gani. Abubuwan da muke iya gani ba masu dawwama ba ne, amma abubuwan da ba a gani madawwama ne. (aiōnios g166)

< 2 Corinthians 4 >