< Acts 25 >
1 Festus, therefore, having come upon the province, after three days, went up unto Jerusalem from Caesarea;
Da Festas ya shiga lardin, kuma bayan kwana uku, ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.
2 and the High-priest and chiefs of the Jews laid information before him against Paul, and began to beseech him
Sai babban firist da manyan Yahudawa suka kawo wa Festas sara a kan Bulus.
3 asking for themselves as a favour against him, that he would send for him unto Jerusalem, —making, an ambush, to kill him on the way.
Suka roki tagomashi wurin Festas ya kira Bulus zuwa Urushalima domin su kashe shi a hanya.
4 Festus, therefore, answered, that Paul should be kept in Caesarea, and that, he himself, was about, shortly, to be going out [thither].
Amma Festas ya amsa masu cewa, Bulus dan sarka ne a Kaisariya, kuma ba da dadewa ba shi da kansa zai koma can.
5 They, therefore, among you (saith he) who are in power, let them go down with me; and, if there is in the man, anything amiss, let them accuse him.
“Saboda haka duk wadanda za su iya, su biyo mu. Idan akwai wani laifi game da mutumin, sai ku zarge shi.”
6 And, spending among them, not more than eight or ten days, he went down unto Caesarea; and, on the morrow, taking his place upon the judgment-seat, ordered Paul to be brought.
Bayan kwana takwas ko goma, sai ya gangara zuwa Kaisariya. Washegari ya zauna bisa kursiyin shari'a ya bada umarni a kawo Bulus a gabansa.
7 And, when he presented himself, the Jews who, from Jerusalem, had come down, stood round about him, many and grievous charges, bringing against [him], which they were not able to prove, —
Da Bulus ya iso, Yahudawa daga Urushalima suka tsaya kusa, suka yi ta kawo kararraki, amma basu iya tabbatar da su ba.
8 Paul saying in defence—Neither against the law of the Jews, nor against the temple, nor against Caesar, have I in anything sinned.
Bulus ya kare kansa ya ce, “Ban yi wa kowa laifi ba, ko Yahudawa, ko haikali, ko kuma Kaisar.”
9 But, Festus, wishing, with the Jews, to gain, favour, answered Paul, and said—Art thou willing, unto Jerusalem, to go up, and, there, concerning these things, be judged before me?
Amma Festas yana neman farin jini wajen Yahudawa, sabo da haka ya tambayi Bulus ya ce, “Kana so ka je Urushalima in shari'anta ka a can game da wadannan abubuwa?”
10 But Paul said—Standing before the judgment-seat of Caesar, am I, where, I, ought to be judged. Unto the Jews, have I done no wrong, as, even thou, right well, art discovering.
Bulus ya ce, “Ina tsaye a Ddakalin Shari'ar Kaisar inda dole a shari'anta ni. Ban yi wa Yahudawa laifi ba, kamar yadda ka sani sosai.
11 If then, on the one hand, I am doing wrong, and, anything worthy of death, have committed, I excuse not myself from dying; but, on the other hand, if there is, nothing, in the things whereof these are accusing me, no man, hath power to give, me, unto them as a favour: —Unto Caesar, I appeal!
Idan lallai na yi laifi kuma na yi abin da ya chanchanci mutuwa, ban ki ba in mutu. Amma idan zarginsu karya ne, kada kowa ya bashe ni gare su. Ina daukaka kara zuwa ga Kaisar.”
12 Then Festus, having conversed with the council, answered—Unto Caesar, hast thou appealed? Unto Caesar, shalt thou go.
Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, “Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar.”
13 And, some days having gone by, Agrippa the king and Bernice came down to Caesarea, to salute Festus.
Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas.
14 And, as they were spending more days there, Festus, repeated, unto the king, the things relating to Paul, saying—A certain man, hath been left behind by Felix, as a prisoner;
Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, “Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku.
15 concerning whom, when I happened to be in Jerusalem, the High-priests and the Elders of the Jews laid information, claiming against him a condemnation:
Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi.
16 unto whom made answer—That it is not a custom with Romans, to grant as a favour any man, before the accused, face to face, should have his accusers, and, opportunity of defence, should receive, concerning the charge.
Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin.
17 When, therefore, they had come together here, no delay whatever, making, on the next day, taking my place upon the judgment-seat, I ordered the man to be brought:
Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin.
18 Concerning whom, taking their stand, his accusers, no accusation at all, were bringing, of the evil things which, I, had been suspecting;
Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta.
19 but, certain questions concerning their own demon-worship, had they against him, and concerning one Jesus, who had died, whom Paul was affirming to be alive.
Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai.
20 And, I, being at a loss as to the inquiry into these things, was asking—whether he might be minded to go unto Jerusalem, and, there, be judged concerning these things.
Na rasa yadda zan bincike wannan al'amarin, sai na tambaye shi ko zai je Urushalima a shari'anta shi kan wadannan abubuwa.
21 But, Paul, having appealed to be kept for the decision of the Emperor, I ordered him to be kept, until I could send him up unto Caesar.
Amma da Bulus ya nemi a lura da shi, Kaisar ya shari'anta shi, sai na ba da umarni a ajiye shi har sai na aika shi wurin Kaisar.”
22 And, Agrippa, [said] unto Festus—I could wish, myself also, to hear, the man. To-morrow, (saith he) thou shalt hear him.
Agaribas yace wa Festas. “Zan so ni ma in saurari mutumin nan.” “Gobe za ka ji shi,” in ji Fostus.
23 On the morrow, therefore, when Agrippa had come, and Bernice, with great display, and they had entered into the audience-chamber, with the captains of thousands and men of distinction of the city, —and Festus had given orders, Paul was brought.
Washegari Agaribas da Barniki suka zo tare da kasaitaccen taro suka shiga dakin taro tare da hafsoshi da shugabanin gari. Da Festas ya ba da umarni, aka fito da Bulus wurinsu.
24 And Festus saith—King Agrippa! and all ye men, here present with us: Ye observe this person, concerning whom, one and all the throng of the Jews, have interceded with me, both in Jerusalem and here, crying aloud that he ought not to be living any longer.
Festas ya ce, “Sarki Agaribas da dukanku da kuke tare da mu a nan, kun ga mutumin nan, dukan Yahudawa sun gana da ni a Urushalima da nan kuma. Suna mani ihu cewa, bai chanchanta a bar shi da rai ba.
25 But, I, gathered, that, nothing worthy of death, had he committed; and, this man himself, having appealed unto the Emperor, I decided to send him: —
Na gane bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ba; amma saboda ya daukaka kara zuwa Kaisar, na yanke shawara in aika shi.
26 Concerning whom, anything certain to write unto my lord, I have not; wherefore, I have brought him forth before you, —and especially before thee, King Agrippa! in order that, after examination had, I might have something I could write;
Amma ba ni da wani dalili na musamman da zan rubuta wasika ga Kaisar. Saboda wannan dalili na kawo shi gabanku, masamman kai ya sarki Agaribas. Domin in sami karin abin da zan rubuta game da shi.
27 For, unreasonable, unto me, it seemeth, when sending a prisoner, not also, the accusations against him, to signify.
Gama a ganina wauta ce in aika dan sarka ba tare da na rubuta laifi a kansa ba.”