< Proverbs 27 >
1 Boast not thyself of tomorrow; for thou knowest not what a day may bring forth.
Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.
2 Let another man praise thee, and not thine own mouth; a stranger, and not thine own lips.
Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba.
3 A stone is heavy, and the sand weighty; but a fool’s vexation is heavier than them both.
Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.
4 Wrath is cruel, and anger is outrageous; but who is able to stand before jealousy?
Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?
5 Better is open rebuke than love that is hidden.
Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye.
6 Faithful are the wounds of a friend: but the kisses of an enemy are profuse.
Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
7 The full soul loatheth an honeycomb: but to the hungry soul every bitter thing is sweet.
Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.
8 As a bird that wandereth from her nest, so is a man that wandereth from his place.
Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa haka yake da mutumin da ya bar gidansa.
9 Ointment and perfume rejoice the heart: so doth the sweetness of a man’s friend [that cometh] of hearty counsel.
Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
10 Thine own friend, and thy father’s friend, forsake not; and go not to thy brother’s house in the day of thy calamity: better is a neighbour that is near than a brother far off.
Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
11 My son, be wise, and make my heart glad, that I may answer him that reproacheth me.
Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.
12 A prudent man seeth the evil, [and] hideth himself: [but] the simple pass on, [and] suffer for it.
Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce, marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
13 Take his garment that is surety for a stranger; and hold him in pledge [that is surety] for a strange woman.
A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
14 He that blesseth his friend with a loud voice, rising early in the morning, it shall be counted a curse to him.
In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana.
15 A continual dropping in a very rainy day and a contentious woman are alike:
Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;
16 He that would restrain her restraineth the wind, and his right hand encountereth oil.
hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka.
17 Iron sharpeneth iron; so a man sharpeneth the countenance of his friend.
Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.
18 Whoso keepeth the fig tree shall eat the fruit thereof; and he that waiteth on his master shall be honoured.
Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.
19 As in water face [answereth] to face, so the heart of man to man.
Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.
20 Sheol and Abaddon are never satisfied; and the eyes of man are never satisfied. (Sheol )
Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani. (Sheol )
21 The fining pot is for silver, and the furnace for gold, and a man is [tried] by his praise.
Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.
22 Though thou shouldest bray a fool in a mortar with a pestle among bruised corn, yet will not his foolishness depart from him.
Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.
23 Be thou diligent to know the state of thy flocks, [and] look well to thy herds:
Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;
24 For riches are not for ever; and doth the crown endure unto all generations?
domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.
25 The hay is carried, and the tender grass sheweth itself, and the herbs of the mountains are gathered in.
Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,
26 The lambs are for thy clothing, and the goats are the price of the field:
gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.
27 And [there will be] goats’ milk enough for thy food, for the food of thy household; and maintenance for thy maidens.
Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.