< Acts 7 >

1 Then the high priest asked, ‘Is this true?’
Sai babban firist ya ce, ''Wadannan al'amura gaskiya ne?''
2 Stephen replied, ‘Brothers and fathers, hear what I have to say. God, who manifests himself in the glory, appeared to our ancestor Abraham when he was in Mesopotamia, and before he settled in Haran, and said to him –
Sai Istifanus ya amsa ya ce, ''Ya 'yan'uwa da ubanni, ku saurare ni, Allah Madaukaki ya bayyana ga ubanmu Ibrahim tun yana can kasar Mesofotamiya, kafin ma ya zauna a kasar Haran;
3 “Leave your country and your people, and come into the country that I will show you.”
ya ce masa, 'Ka bar kasarka da danginka, ka tafi kasar da zan nuna maka.'
4 And so Abraham left the country of the Chaldaeans and settled in Haran; and from there, after his father’s death, God caused him to migrate into this country, in which you are now living.
Sa'annan ya bar kasar Kaldiyawa ya zo ya zauna a Haran; daga can, bayan rasuwar mahaifinsa, sai Allah ya kira shi zuwa wannan kasa da kuke ciki.
5 God did not at that time give him any part of it, not even a foot of ground. But he promised to give him possession of it and his descendants after him, though at that time he had no child.
Amma Allah bai ba shi kasar gado ba tukuna, ko da misalin tafin sawunsa. Amma ya alkawarta - ko da yake bai riga ya haifi da ba tukuna - wanda zai ba shi kasar gado, shi da zuriyarsa, a bayansa.
6 God’s words were these – “Abraham’s descendants will live in a foreign country, where they will be enslaved and ill-treated for four hundred years.
Allah ya yi magana da shi kamar haka, cewa zuriyarsa za su yi bakonci a wata kasa wadda ba tasu ba, mutanen wannan kasar kuwa za su gwada masu bakar azaba su kuma bautar da su har shekaru dari hudu.
7 But I myself will judge the nation, to which they will be enslaved,” God said, “and after that they will leave the country and worship me in this place.”
'Kuma zan hukunta wannan al'umma da ta bautar da su,' Allah ya ce, 'Bayan haka za su fito daga wannan kasa su bauta mini a wannan wuri.'
8 Then God made with Abraham the covenant of circumcision; and under it Abraham became the father of Isaac, and circumcised him when he was eight days old; and Isaac became the father of Jacob; and Jacob of the Twelve Patriarchs.
Allah ya ba Ibrahim alkawarin kaciya, sai Ibrahim ya haifi Ishaku ya yi masa kaciya a rana ta takwas; Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi ubanni Isra'ila su goma sha biyu.
9 The Patriarchs, out of jealousy, sold Joseph into slavery in Egypt; but God was with him,
Wadannan 'yan'uwa suka yi kyashin danuwansu Yusifu suka sayar da shi bauta zuwa Masar. Amma Allah na tare da shi.
10 and delivered him out of all his troubles, and enabled him to win favour and show wisdom before Pharaoh, king of Egypt, who appointed him Governor of Egypt and of his whole household.
Ya kuwa cece shi daga dukan sharin da yan uwansa suka kulla masa, Allah kuwa ya ba shi tagomashi da hikima a gaban Fir'auna, sarkin Masar. Fir'auna kuwa ya mai da shi mai mulki a dukan kasar Masar da kuma dukan mallakarsa.
11 Then a famine spread over the whole of Egypt and Canaan, causing great distress, and our ancestors could find no food.
Sai aka yi babbar yunwa a dukan kasar Masar da ta Kan'ana, iyayenmu suka sha wuya saboda rashin abinci.
12 Hearing, however, that there was corn in Egypt, Jacob sent our ancestors there on their first visit.
Amma lokacin da Yakubu ya ji akwai hatsi a kasar Masar, sai ya aiki ubannimu a karo na farko.
13 In the course of their second visit, Joseph revealed himself to his brothers, and his family became known to Pharaoh.
Da suka je a karo na biyu, sai Yusifu ya bayyana kansa ga yanuwansa; a wannan lokaci ne Fir'auna ya gane da yanuwan Yusufu.
14 Then Joseph sent an urgent invitation to his father Jacob and to his relatives, seventy-five persons in all;
Yusufu ya aiki yanuwansa su kawo Yakubu ubansu da dukan mallakarsu da iyalansu zuwa Masar, Dukansu mutane saba'in da biyar ne.
15 and so Jacob went down into Egypt. There he died, and our ancestors also,
Yakubu ya tafi ya zauna a Masar; shi da zuriyarsa har mutuwar su.
16 and their bodies were removed to Shechem, and laid in the tomb which Abraham had bought for a sum of money from the sons of Hamor in Shechem.
Aka dauke su zuwa Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya da kudin azurfa daga hannun yayan Hamor a Shekem.
17 As the time drew near for the fulfilment of the promise which God had made to Abraham, the people increased largely in numbers in Egypt,
Yayin da alkawarin Allah ya kusato wanda Allah ya fada wa Ibrahim, mutanen suka karu suka hayayyafa kwarai a Masar,
18 until a new king, who knew nothing of Joseph, came to the throne.
Sai a ka yi wani sarki a Masar wanda bai san Yusifu ba,
19 This king acted deceitfully towards our people and ill-treated our ancestors, making them abandon their own infants, so that they should not be reared.
Wannan sarki ya yaudari kakkaninmu ya yi masu mugunta kwarai da gaske, har ma ya kai ga suna barin jariransu cikin hasari don su ceci rayukansu.
20 It was just at this time that Moses was born. He was an exceedingly beautiful child, and for three months was brought up in his own father’s house;
A wannan lokaci ne aka haifi Musa, kuma kyakkyawan yaro ne sai aka yi renon sa tsawon wata uku a gidan mahaifinsa a asirce.
21 and, when he was abandoned, the daughter of Pharaoh found him and brought him up as her own son.
Yayin da aka jefar da shi, sai diyar Fir'auna ta dauke shi ta rene shi kamar danta.
22 So Moses was educated in all the learning of the Egyptians, and proved his ability both by his words and actions.
Aka ilimantar da Musa da dukan ilimi irin na Masar; kuma ya shahara cikin fasahar magana da kuma ayyukansa.
23 When he was in his fortieth year, he resolved to visit his fellow Israelites;
Amma lokacin da yakai shekara arba'in, sai ya yi niyyar ya ziyarci 'yan'uwansa, Isra'ilawa.
24 and, seeing an Israelite ill-treated, he defended him, and avenged the man, who was being wronged, by striking down the Egyptian.
Sai ya ga wani na cin zalin Ba Isra'ile, Musa kuwa ya taimaki wanda ake kwara ta wurin murkushe Bamasaren:
25 He thought his own people would understand that God was using him to save them; but they failed to do so.
zaton Musa 'yan'uwansa za su fahimci taimakon Allah ne ya zo masu amma ina! Basu gane ba.
26 The next day he again appeared on the scene, when some of them were fighting, and tried to make peace between them. “Men,” he said, “you are brothers; how is it that you are ill-treating one another?”
Washegari ya ga wasu Isra'ilawa na fada da junansu; ya yi kokari ya raba su; sai ya ce masu, 'Malamai, ku 'yan'uwan juna ne; don me kuke fada da junanku?'
27 But the man who was ill-treating his fellow workman pushed Moses aside saying – “Who made you a ruler and judge over us?
Amma shi wanda ake kwarar makwabcinsa ya ture Musa a gefe guda, ya ce, 'Wa ya nada ka shugaba ko alkali akanmu?
28 Do you mean to make away with me as you did yesterday with that Egyptian?”
Kana so ka kashe ni ne, kamar yadda ka kashe Bamasaren nan jiya?'
29 At these words Moses took to flight, and became an exile in Midian; and there he had two sons born to him.
Da jin haka sai Musa ya gudu, zuwa kasar Midinawa, a matsayin dan gudun hijira. Anan ya haifi ''ya'ya biyu maza.
30 Forty years had passed when there appeared to him, in the desert of Mount Sinai, an angel in a flame of fire in a bush.
Bayan da shekaru arba'in suka wuce, sai mala'ika ya bayyana gare shi a jeji, kusa da dutsen Sinai, a cikin harshen wuta a cikin jeji.
31 When Moses saw it, he was astonished at the vision; but on his going nearer to look at it more closely, the voice of the Lord was heard to say –
Sa'adda Musa ya ga wutar, mamaki ya kama shi; sai ya maso kusa don ya kara dubawa, sai ya ji muryar Ubangiji na cewa,
32 “I am the God of your ancestors, the God of Abraham, Isaac, and Jacob.” Moses trembled, and did not dare to look.
'Nine Allah na ubanninka, Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu.' Musa ya razana har ma bai sake daga kai ya duba ba.
33 Then the Lord said to him – “Take your sandals off your feet, for the spot where you are standing is holy ground.
Ubangiji ya ce masa, 'Tube takalminka, domin in da kake tsaye wuri mai tsarki ne.
34 I have seen the oppression of my people who are in Egypt, and heard their groans, and I have come down to deliver them. Come now and I will send you into Egypt.”
Ba shakka na ga wahalar da mutane na ke sha a Masar, kuma na ji nishinsu, don haka na zo in cece su, yanzu fa sai ka zo, in aike ka zuwa Masar.'
35 This same Moses, whom they had disowned with the words – “Who made you a ruler and a judge?” was the man whom God sent to be both a ruler and a deliverer, under the guidance of the angel that had appeared to him in the bush.
Wannan fa shine Musan da suka ki, harma da cewa, 'Wanene ya nada ka alkali ko shugaba a kanmu?' Shine kuma wanda Allah ya aiko masu a matsayin shugaba da kuma mai ceto. Allah ya aiko shi ta hannun mala'ikan da ya gani a daji.
36 He it was who led them out, after he had shown wonders and signs in Egypt, in the Red Sea, and in the desert during forty years.
Bayan alamu da al'ajibai iri-iri a Masar da kuma Baharmaliya, Musa ya fito da su daga Masar da kuma cikin jeji, a lokacin da suka yi tafiya shekara arbain.
37 This was the Moses who said to the people of Israel – “God will raise up for you, from among yourselves, a prophet, as he raised up me.”
Wannan shine Musan da ya cewa Isra'ilawa, 'Ubangiji zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin Yan'uwan ku.'
38 He, too, it was who was present at the assembly in the desert, with the angel who talked to him on Mount Sinai, and with our ancestors, and who received living truths to impart to you.
Wannan shine mutumin da ke tare da mutane a jeji. Karkashin jagorancin mala'ikan da ya yi magana da shi a dutsen Sinai. Wannan ne mutumin da ke tare da ubannen mu, wannan shi ne mutumin da ya ba mu maganar Allah mai rai.
39 Yet our ancestors refused him obedience; more than that, they rejected him, and in their hearts turned back to Egypt,
Wannan shine mutumin da ubannenmu suka ki su yi masa biyayya; su ka fitar da shi daga cikinsu, suka kudurta a zuciyarsu za su koma masar.
40 while they said to Aaron – “Make us Gods who will lead the way for us, since, as for this Moses who has brought us out of Egypt, we do not know what has become of him.”
A lokacin ne suka cewa Haruna, 'ya yi masu allolin da za su jagorance su zuwa masar. Domin kuwa ga zancen Musan nan da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.'
41 That was the time when they made the calf and offered sacrifice to their idol, and held festivities in honour of their own handiwork!
Sai suka kera dan maraki suka kawo wa gunkin hadaya, suka yi murna da abin da hannayensu suka kera.
42 So God turned from them and left them to the worship of the Starry Host, as is written in the book of the prophets – “Did you offer victims and sacrifices to me, house of Israel, all those forty years in the desert?
Allah ya bashe su su bauta wa tauraran sama, kamar yadda yake a rubuce cikin littattafafan annabawa, 'Kun mika mani hadayu na yankakkun dabbobi a jeji ne a shekaru arba'in din nan ya ku Isra'ilawa?'
43 You took with you the tent where Moloch is worshipped and the star of the god Rephan – the images which you had made to worship. Therefore I will exile you beyond Babylon.”
Kun yarda da haikalin Molek da kuma tauraron allahn nan Rafem, da kuma siffofin nan da kuka kera don ku yi masu sujada; don haka zan kai ku bauta har gaba da Babila.'
44 Our ancestors had the tent where they worshipped God in the desert, constructed, just as he who spoke to Moses had directed him to make it, after the model which he had seen.
Kakkaninmu suna da alfarwa ta sujada domin shaida a cikin jeji, kamar yadda Allah ya umarta yayin da ya yi magana da Musa, cewa ya yi shi bisa ga salon da aka nuna mashi.
45 This tent, which was handed down to them, was brought into this country by our ancestors who accompanied Joshua (at the conquest of the nations that God drove out before their advance), and remained here until the time of David.
Wannan shine Alfarwar da kakkaninmu suka zo da shi, a lokacin Joshuwa. Wannan ya faru ne yayin da suka mallaki wannan kasa ta al'ummai da Allah ya kora a gaban kakkaninmu. Haka abin yake har ya zuwa zamanin Dauda,
46 David found favour with God, and prayed that he might provide the God of Jacob with a place to reside.
wanda ya sami tagomashi a wurin Allah; don ya gina masujada domin Allah na Yakubu.
47 But it was Solomon who built a house for God.
Amma Sulaimanu ne ya gina Gidan Allah.
48 Yet it is not in buildings made by hands that the Most High dwells. As the prophet says –
Sai dai Madaukaki ba yakan zauna a gidan da hannaye suka gina ba, kamar yadda annabin ya ce,
49 “The heavens are a throne for me, and the earth a stool for my feet. What manner of house will you build me, asks the Lord, or what place is there where I may rest?
'Sama kursiyina ce, duniya kuwa wurin ajjiye sawayena ne. To wane irin gida za ku gina mani? inji Ubangiji: ko kuwa ina ne wurin da zan huta?
50 Was it not my hand that made all these things?”
Ko ba hannayena ne suka yi dukan wadannan ba?'
51 Stubborn people, heathen in heart and ears, you are for ever resisting the Holy Spirit; your ancestors did it, and you are doing it still.
Ku mutane masu taurin kai masu zuciya mara kaciya da kunnuwa marasa ji, kullum kuna gaba da Ruhu Mai Tsarki, kuna aikata abin da kakkaninku suka aikata.
52 Which of the prophets escaped persecution at their hands? They killed those who foretold the coming of the righteous one; of whom you, in your turn, have now become the betrayers and murderers –
Wane annabi ne kakkaninku ba su tsanantawa ba? Sun kashe annabawan da suka rigayi zuwan Mai Adalcin nan, kuma kun zama wadanda suka kasance masu bashe shi da masu kashe shi,
53 you who received the Law as transmitted by angels and yet failed to keep it.’
kune mutanen da kuka karbi shari'a wadda mala'iku suka bayar, amma ba ku kiyaye ta ba”.
54 As they listened to this, the Council grew frantic with rage, and gnashed their teeth at Stephen.
Yayin da majalisar suka ji wannan, sai ransu ya baci kwarai, har suna cizon hakoransu don gaba da Istifanus.
55 He, filled as he was with the Holy Spirit, fixed his eyes intently on the heavens, and saw the glory of God and Jesus standing at God’s right hand.
Amma shi, cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya daga idonsa sama, ya ga daukakar Allah; ya kuma hango Yesu na tsaye a hannun daman Allah.
56 ‘Look,’ he exclaimed, ‘I see heaven open and the Son of Man standing at God’s right hand!’
Istifanus ya ce, “Duba, ina ganin sama ta bude, ga Dan Mutum na tsaye a hannun dama na Allah.”
57 At this, with a loud shout, they stopped their ears and all rushed on him, forced him outside the city,
Amma yan majalisar suka daga murya da karfi, suka yi ihu, suka kuma toshe kunnuwansu, gaba dayansu suka afka masa;
58 and began to stone him, the witnesses laying their clothes at the feet of a young man named Saul.
suka fitar da shi bayan gari, suka jejjefe shi da duwatsu, don shaida sai suka tube manyan rigunansu suka ajiye a gaban wani matashi da ake ce da shi Shawulu.
59 And they stoned Stephen, while he cried to the Lord, ‘Lord Jesus! Receive my spirit!’
Lokacin da suke kan jifan Istifanus, ya dinga kira yana cewa, ''Ya Ubangiji Yesu, ka karbi ruhu na.”
60 Falling on his knees, he called out loudly, ‘Lord! Do not charge them with this sin;’ and with these words he fell asleep.
Ya durkusa ya daga murya da karfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka rike wannan zunubi a kansu.” Yayin da ya fadi wannan, sai ya yi barci.

< Acts 7 >