< Mark 6 >
1 And he went out from thence, and cometh into his own country; and his disciples follow him.
Ya bar su ya zo garinsu, almajiransa su ka biyo shi.
2 And when the sabbath was come, he began to teach in the synagogue. And most people when they heard him were astonished, saying, Whence hath this man these things? And what is the wisdom which is given him? And how is it that such miracles are wrought by his hands?
Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa?
3 Is not this the carpenter, the son of Mary, and brother of James, and Joses, and Judah, and Simon? And are not his sisters here with us? And they took offence at him.
Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu.
4 And Jesus said to them, A prophet is not without honor except in his own country, and among his own kindred, and in his own house.
Yesu ya ce, “Annabi ba ya rasa daraja sai a gidansa da garinsa da cikin danginsa.”
5 And he could not do any miracle there, except that he laid his hand upon a few sick persons, and cured them.
Bai iya yin wani aikin al'ajibi a wurin ba sai dai mutane kadan marasa lafiya ya dorawa hannu ya warkar da su.
6 And he wondered at their want of faith. And he went about the surrounding villages teaching.
Rashin bangaskiyarsu ya ba shi mamaki. Sai ya tafi cikin kauyuka na kewaye da su ya yi ta koyarwa.
7 And he calleth to him the twelve, and began to send them forth by two and two; and gave them power over the unclean spirits;
Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu,
8 and commanded them that they should take nothing for the way but a staff only; no bread, no bag, no money in their girdle;
ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu,
9 but to be shod with sandals; and, Do not put on two coats.
sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu.
10 And he said to them, Wherever ye enter a house, there abide fill ye leave that place.
Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi.
11 And whatever place shall not receive you, nor hear you, when ye go thence, shake off the dust under your feet as a testimony to them.
Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin.
12 And they went out and preached that men should repent;
Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu.
13 and they cast out many demons, and anointed with oil many sick persons, and healed them.
Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su.
14 And king Herod heard of him (for his name was spread abroad), and he said, John the Baptizer hath risen from the dead, and therefore do these powers work in him. But others said, It is Elijah.
Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa.
15 And others said, It is a prophet, as one of the prophets.
Wadansu kuma suna cewa, “Iliya,” Har yanzu wadansu suna cewa daya “daga cikin annabawa ne na da can.”
16 But Herod hearing of it said, John, whom I beheaded, hath risen again.
Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, “Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi.”
17 For Herod himself had sent forth and seized John, and bound him in prison, on account of Herodias, his brother Philip's wife; for he had married her.
Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya( matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta.
18 For John had said to Herod, It is not lawful for thee to have thy brother's wife.
Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba.
19 And Herodias was enraged against him, and wished to put him to death, but could not.
Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba.
20 For Herod feared John, knowing that he was a righteous and holy man, and was regardful of him; and on hearing him, was in much anxiety, and listened to him gladly.
Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi.
21 And a convenient day having come, when Herod on his birthday made a supper for his nobles and chief captains and the principal men of Galilee,
Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili.
22 and the daughter of Herodias came in and danced, she pleased Herod and those at table with him; and the king said to the damsel, Ask of me whatever thou wilt, and I will give it thee.
Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, “ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi”.
23 And he swore to her, Whatever thou shalt ask of me, I will give thee, to the half of my kingdom.
Ya rantse mata da cewa”Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne”
24 And she went out and said to her mother, What shall I ask? And she said, The head of John the Baptizer.
Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, “me zan ce ya bani?” Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma.
25 And she came in immediately with haste to the king, and asked, saying, I desire that thou wilt give me immediately on a platter the head of John the Baptist.
Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, “Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire.”
26 And the king was exceedingly sorry; but on account of his oaths, and of those at table with him, he would not refuse her.
Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a.
27 And the king immediately sent one of his guards, and ordered his head to be brought. And he went and beheaded him in the prison,
Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku.
28 and brought his head on a platter, and gave it to the damsel; and the damsel gave it to her mother.
Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta.
29 And his disciples, when they heard of it, came and took up his body, and laid it in a tomb.
Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari.
30 And the apostles gather together to Jesus, and told him all which they had done and taught.
Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar.
31 And he saith to them, Come ye by yourselves apart into a desert place, and rest a while. For there were many coming and going; and they had no leisure, even to eat.
Sai ya ce da su “ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan,” domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci
32 And they went away into a desert place in the boat apart.
Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai.
33 And many saw them departing, and knew them, and ran together on foot thither from all the cities, and arrived before them.
Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo.
34 And when he came forth, he saw a great multitude, and was moved with compassion for them, because they were as sheep not having a shepherd; and he began to teach them many things.
Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa.
35 And late in the day his disciples came to him, and said, This is a desert place, and it is now late;
Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, “wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi.
36 send them away, that they may go into the surrounding fields and villages, and buy themselves something to eat.
Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci.
37 But he answering said to them, Give ye them to eat. And they say to him, Shall we go and buy two hundred denaries' worth of bread, and give them to eat?
Amma sai ya ba su amsa ya ce,”Ku ku basu abinci su ci mana”. Sai suka ce da shi, “ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?”
38 He saith to them, How many loaves have ye? Go and see. And when they knew, they say, Five, and two fishes.
Sai ya ce dasu, “Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani.” Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu.”
39 And he ordered them to make all lie down in companies upon the green grass.
Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa.
40 And they lay down in ranks, by hundreds, and by fifties.
Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin.
41 And taking the five loaves and the two fishes, he looked up to heaven and blessed, and broke the loaves, and gave them to the disciples to set before them; and the two fishes he divided among them all.
Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka.
42 And they all ate, and were filled.
Dukansu suka ci suka koshi.
43 And they took up twelve baskets full of the fragments, and of the fishes.
Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin.
44 And they who ate of the loaves were five thousand men.
Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar.
45 And he immediately constrained his disciples to get into the boat, and to go before to the other side to Bethsaida, while he sent the multitude away.
Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen.
46 And when he had taken leave of them, he went away into the mountain to pray.
Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a.
47 And when evening came, the boat was in the midst of the lake; and he was alone on the land.
Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai.
48 And when he saw them toiling hard in rowing, for the wind was against them, about the fourth watch of the night he cometh to them, walking upon the lake. And he would have passed by them;
Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su.
49 but they, seeing him walking upon the lake, thought it was a spectre, and cried out.
Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu,
50 For they all saw him, and were terrified. But he immediately spoke with them, and saith to them, Be of good cheer; it is I, be not afraid.
gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, “Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!''
51 And he went up to them into the boat, and the wind ceased. And they were exceedingly astonished, beyond measure.
Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai.
52 For they did not consider the matter of the loaves; but their heart was hardened.
Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare.
53 And crossing over, they came to land, to Gennesaret; and anchored there.
Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka.
54 And when they had come out of the boat, the people immediately knowing who he was,
Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne.
55 ran through all that region, and began to carry about on beds those that were sick to the place where they heard he was.
Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa.
56 And wherever he entered into villages or cities or the open country, they laid the sick in the market-places, and besought him that they might touch if it were but the fringe of his garment; and as many as touched him were made well.
Ko ina ya shiga birni da kauye, ko a cikin kasar sukan kawo marasa lafiya a kasuwanni suna rokonsa su taba ko da habar rigarsa, dukan wadanda suka taba kuwa suka warke.