< James 1 >

1 James, a servant of God and of the Lord Jesus Christ, to the twelve tribes which are scattered abroad, greeting.
Yakubu, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da suke warwatse: ina gaishe ku.
2 Count it all joy, my brethren, when ye fall into various temptations;
Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi.
3 knowing that the trying of your faith worketh endurance.
Ku sani cewa gwajin banskiyar ku ta kan haifi jimiri.
4 But let endurance have a perfect work, that ye may be perfect and entire, wanting in nothing.
Bari jimiri ya cika aikin sa, domin ku kai ga cikakken girma kuma ku kammalu, domin kada ku rasa komai.
5 But if any one of you is wanting in wisdom, let him ask of God, who giveth to all liberally, and upbraideth not; and it will be given him.
Amma idan waninku yana bukatar hikima, sai ya roki Allah, wanda yake bayarwa a yalwace, ba tare da gori ba ga duk wanda ya roke shi, zai kuwa ba shi.
6 But let him ask in faith, nothing doubting; for he that doubteth is like a wave of the sea driven by the wind and tossed.
Amma fa sai ya roka da banskiya ba tare da shakka ba, don mai shakka kamar rakumin ruwan teku yake, wanda iska take korarwa tana tunkudawa.
7 For let not that man think that he shall receive anything from the Lord,
Tilas ne wannan mutum kada ya yi tunanin zai karbi wani abu a wurin Ubangiji.
8 a double-minded man as he is, unstable in all his ways.
Irin wannan mutumin mai zuciya biyu ne, mara tsai da hankali a dukan hanyoyin sa.
9 Let the brother of low degree glory in that he is exalted;
Bari dan'uwa matalauci ya yi takama da matsayin sa babba,
10 but the rich, in that he is made low; because as the flower of the grass he will pass away.
amma mutum mai arziki kuma a kaskantaccen matsayin sa, gama zai shude kamar furen ciyawa na jeji.
11 For the sun rose with its burning heat, and withered the grass, and its flower fell off, and the beauty of its appearance perished; so also will the rich man fade away in his ways.
Domin rana na bullowa da zafi mai konarwa kuma ya busar da ciyawa. Furen ya fadi, kuma kyaun sa ya lalace. Haka ma, mai arziki zai bushe yana cikin tsakiyar tafiyarsa.
12 Blessed is the man that endureth temptation; for when he is approved, he will receive the crown of life, which He promised to them that love him.
Albarka ta tabbata ga mutum mai jurewa da gwaji. Domin in ya jure gwajin, zai sami rawanin rai, wanda aka yi alkawarin sa ga wadanda ke kaunar Allah.
13 Let no one when he is tempted, say, I am tempted by God; for God cannot be tempted with evil, and he tempteth no one.
Kada wani ya ce idan aka gwada shi, ''Wannan gwaji daga wurin Allah ne,'' domin ba a gwada Allah da mugunta, shi kan sa kuwa ba ya gwada kowa.
14 But each one is tempted when by his own lust he is led away and enticed;
Amma kowanne mutum yakan sami gwaji daga muguwar sha'awar sa, wadda take janye shi kuma ta rinjaye shi.
15 then lust, having conceived, bringeth forth sin, and sin, when completed, bringeth forth death.
Bayan da muguwar sha'awar ta dauki ciki, sai ta haifi zunubi. Kuma bayan da zunubi ya yi girma, yakan haifi mutuwa.
16 Do not err, my beloved brethren.
Kada fa ku yaudaru, 'yan'uwana kaunatattu.
17 Every good gift and every perfect gift is from above, coming down from the Father of the lights, with whom is no change, nor shadow from turning.
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar baiwa daga sama take. Ta sauko ne daga wurin Uban haskoki. Wanda babu sauyawa ko wata alamar sakewa kamar yadda inuwa ke yi.
18 Of his own will he begot us with the word of truth, that we should be a kind of first-fruits of his creatures.
Allah ya zabi ya haife mu ta wurin maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunar fari na dukan halittar sa.
19 Wherefore, my beloved brethren, let every man be swift to hear, slow to speak, slow to wrath.
Kun san wannan, 'yan'uwana kaunatattu: bari kowanne mutum ya yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi.
20 For the wrath of man worketh not the righteousness of God.
Domin fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah.
21 Wherefore put off all filthiness, and excess of wickedness, and receive with meekness the implanted word, which is able to save your souls.
Saboda haka, sai ku yar da kowanne irin aikin kazanta da yalwar mugunta. A cikin tawali'u ku karbi dassashiyar maganar, wadda ke iya ceton rayukan ku.
22 But be doers of the word, and not hearers only, deceiving yourselves.
Ku zama masu aikata maganar, kada ku zama masu jin ta kawai, kuna yaudarar kanku.
23 For if any one is a hearer of the word, and not a doer, he is like a man beholding his natural face in a glass;
Domin duk wanda ya ke mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi.
24 for he beholds himself, and goes away, and immediately forgets what manner of man he was.
Yakan dubi kansa sai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya manta da kamannin sa.
25 But he who looks into the perfect law of liberty, and remains there, being not a forgetful hearer, but a doer of the work, this man will be blessed in his deed.
Amma duk mai duba shari'ar da bin ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace biyayya da ita, ba zai zama kamar wanda zai ji ya manta ba, wannan mutum zai zama da albarka a cikin abin da yake yi.
26 If any one thinks that he is religious, and bridles not his tongue, but deceives his own heart, this man's religion is vain.
Idan wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, yana yaudarar zuciyarsa ne, addinin mutumin nan na banza ne.
27 Pure religion and undefiled before God, the Father, is this, to visit the fatherless and widows in their affliction, and to keep one's self unspotted from the world.
Addini sahihi kuma marar aibi a gaban Allahnmu da Ubanmu, shine a kula da gwauraye da marayu a cikin kuntatar su, kuma mutum ya kebe kansa ya zama marar aibi daga duniya.

< James 1 >