< Acts 7 >

1 And the high-priest said, Are then these things so?
Sai babban firist ya tambaye shi ya ce, “Waɗannan zargen gaskiya ne?”
2 And he said, Brethren and fathers, hearken. The God of glory appeared to our father Abraham, when he was in Mesopotamia, before he dwelt in Haran,
Game da wannan ya amsa ya ce, “’Yan’uwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran.
3 and said to him, “Go forth from thy country and thy kindred, and come into the land which I will show thee.”
Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’
4 Then came he out of the land of the Chaldaeans, and dwelt in Haran; and from thence, after his father was dead, he caused him to remove into this land wherein ye now dwell;
“Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aika da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama.
5 and he gave him no inheritance in it, no, not so much as to set his foot on; and he promised to give it to him for a possession, and to his posterity after him, when as yet he had no child.
Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro.
6 And God spoke in this manner: “That his posterity should sojourn in a foreign land, and that they would bring them into bondage, and ill-treat them four hundred years;
Allah ya yi magana da shi ta haka, ‘Shekara ɗari huɗu, zuriyarka za tă yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci.
7 and the nation to which they shall be in bondage will I judge,” said God; “and after that they shall come forth, and shall worship me in this place.”
Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘Kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’
8 And he gave him the covenant of circumcision; and so he begat Isaac, and circumcised him on the eighth day; and Isaac begat Jacob, and Jacob the twelve patriarchs.
Sa’an nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.
9 And the patriarchs, moved with envy, sold Joseph into Egypt; and God was with him,
“Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi
10 and delivered him out of all his afflictions, and gave him favor and wisdom in the sight of Pharaoh king of Egypt; and he made him governor over Egypt, and all his house.
ya kuma cece shi daga dukan wahalolinsa. Ya ba wa Yusuf hikima ya kuma sa ya sami farin jini a wurin Fir’auna, sarkin Masar; saboda haka ya mai da shi mai mulki a kan Masar da kuma dukan fadarsa.
11 Now there came a famine over all the land of Egypt and Canaan, and great distress; and our fathers found no Sustenance.
“Sai yunwa ta auko wa dukan Masar da Kan’ana, ta kawo wahala mai tsanani, kakanninmu ba su iya samun abinci ba.
12 But Jacob, hearing that there was grain in Egypt, sent out our fathers first.
Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa akwai hatsi a Masar, sai ya aiki kakanninmu ziyararsu ta farko.
13 And at the second time Joseph was recognized by his brothers, and the kindred of Joseph became known to Pharaoh.
A ziyararsu ta biyu, Yusuf ya faɗa wa’yan’uwansa wane ne shi, Fir’auna kuwa ya sami sani game da iyalin Yusuf.
14 Then Joseph sent and called his father Jacob to him, and all his kindred, seventy five souls.
Bayan wannan, Yusuf ya aika a zo da mahaifinsa Yaƙub da dukan iyalinsa, gaba ɗaya dai mutum saba’in da biyar ne.
15 And Jacob went down [[into Egypt]], and died, he and our fathers.
Sai Yaƙub ya gangara zuwa Masar, inda shi da kuma kakanninmu suka mutu.
16 And they were removed to Shechem, and laid in the tomb that Abraham bought for a sum of money of the sons of Hamor, the father of Shechem.
Aka dawo da gawawwakinsu Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya daga wurin’ya’yan Hamor da waɗansu kuɗi a Shekem.
17 But as the time of the promise drew near, which God solemnly made to Abraham, the people grew and multiplied in Egypt,
“Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, sai yawan mutanenmu da suke a Masar ya ƙaru ƙwarai.
18 until another king arose, who knew not Joseph.
Sa’an nan wani sarki, wanda bai san kome game da Yusuf ba, ya zama mai mulkin Masar.
19 The same dealt subtly with our race, and ill-treated our fathers, so that they should cast out their infants, that they might not be preserved alive.
Ya kuwa wulaƙanta mutanenmu sosai, ya kuma gwada wa kakanni-kakanninmu azaba ta wurin tilasta su su zubar da sababbin jariransu, don su mutu.
20 In which time Moses was born, and was exceedingly fair; who was nourished in his father's house three months.
“A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa.
21 And when he was cast out, Pharaoh's daughter took him up, and nourished him for herself as a son.
Sa’ad da aka ajiye shi a waje, diyar Fir’auna ta ɗauke shi ta kuma rene shi kamar ɗanta.
22 And Moses was instructed in all the wisdom of the Egyptians, and was mighty in his worlds and deeds.
Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.
23 And when he was forty years old, it came into his heart to visit his brethren, the sons of Israel.
“Da Musa ya cika shekara arba’in da haihuwa, sai ya yanke shawara yă ziyarci’yan’uwansa Isra’ilawa.
24 And seeing one of them suffer wrong, he defended him, and avenged him that was oppressed by smiting the Egyptian.
Ya ga ɗayansu yana shan wulaƙanci a hannun wani mutumin Masar, sai ya je ya kāre shi, ya rama masa ta wurin kashe mutumin Masar ɗin.
25 For he supposed his brethren would understand that God through his hand would give them salvation; but they understood not.
Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don yă cece su, amma ba su gane ba.
26 And the next day he showed himself to them as they were contending, and urged them to peace, saying, Ye are brethren; why do ye wrong one another?
Kashegari, Musa ya sadu da Isra’ilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku’yan’uwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’
27 But he who was wronging his neighbor thrust him away, saying, “Who made thee a ruler and a judge over us?
“Amma mutumin da yake wulaƙanta ɗayan, ya tura Musa a gefe ya ce, ‘Wa ya mai da kai mai mulki, da alƙali a kanmu?
28 Dost thou mean to kill me, as thou didst kill the Egyptian yesterday?”
Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’
29 And Moses fled at this saying, and became a sojourner in the land of Midian, where he begat two sons.
Sa’ad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi’ya’ya biyu maza.
30 And when forty years were completed, there appeared to him in the wilderness of Mount Sinai an angel in the flaming fire of a bush.
“Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.
31 And Moses seeing it wondered at the sight; and as he drew near to behold it, the voice of the Lord came [[to him]],
Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,
32 saying, “I am the God of thy fathers, the God of Abraham and Isaac and Jacob.” And Moses trembled and durst not behold.
‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.
33 And the Lord said to him, “Loose the sandals from thy feet; for the place where thou standest is holy ground.
“Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne.
34 I have surely seen the oppression of my people in Egypt, and I have heard their groaning, and am come down to deliver them; and now, come, I will send thee into Egypt.”
Tabbatacce na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in’yantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’
35 This Moses, whom they denied, saying, “Who made thee a ruler and a judge?” this very man did God send both as a ruler and a redeemer with the hand of the angel who appeared to him in the bush.
“Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin mala’ikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yă zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu.
36 This very man brought them out, working wonders and signs in the land of Egypt, and in the Red Sea, and in the wilderness forty years.
Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arba’in.
37 This is the Moses who said to the sons of Israel, “A prophet will God raise up to you from among your brethren, as he raised up me.”
“Wannan Musa ne ya ce Isra’ilawa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’
38 This is he that was in the assembly in the wilderness with the anger who spake to him on Mount Sinai, and with our fathers; who received the living oracles to give to us;
Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da mala’ikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don yă miƙa mana.
39 to whom our fathers would not be obedient, but thrust him from them, and in their hearts turned back into Egypt,
“Amma kakanninmu suka ƙi yin masa biyayya. A maimakon haka, sai suka ƙi shi a cikin zuciyarsu kuwa suka koma Masar.
40 saying to Aaron, “Make us gods who shall go before us; for as for this Moses, who brought us out of the land of Egypt, we know not what is become of him.”
Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba!’
41 And they made a calf in those days, and offered sacrifice to the idol, and rejoiced in the works of their own hands.
A lokacin ne suka ƙera gunki mai siffar ɗan maraƙi. Suka kawo masa hadayu suka kuma yi bikin girmama abin da suka ƙera da hannuwansu.
42 But God turned away, and gave them up to worship the host of heaven; as it is written in the book of the Prophets, “Did ye offer to me slain beasts and sacrifices for forty years in the wilderness, O house of Israel?
Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa, “‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?
43 And ye took up the tabernacle of Moloch, and the star of the god Rephan, the figures which ye made to worship them; and I will carry you away beyond Babylon.”
Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.
44 Our fathers had the tabernacle of the testimony in the wilderness, as he that spoke to Moses commanded that he should make it according to the pattern that he had seen;
“Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.
45 which also our fathers received and brought in with Joshua, at their taking possession of the gentiles whom God drove out from before our fathers, until the days of David;
Bayan sun gāji tabanakul nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga al’umman da Allah ya kora a idanunsu. Tabanakul ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda,
46 who found favor before God, and asked that he might find a habitation for the God of Jacob.
wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yă yi wa Allah na Yaƙub wurin zama.
47 But Solomon built him a house.
Amma Solomon ne ya gina masa gida.
48 Yet the Most High dwelleth not in [[temples]] made with hands; as saith the prophet,
“Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa,
49 “Heaven is my throne, and the earth is my footstool. What house will ye build for me? saith the Lord; or what is the place of my rest?
“‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji.
50 Did not my hands make all these things?”
Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’
51 Stiffnecked, and uncircumcised in heart and ears! ye do always resist the Holy Spirit; as your fathers did, so do ye.
“Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki!
52 Which of the prophets did not your fathers persecute? And they slew those who foretold the coming of the righteous one, of whom ye have now become the betrayers and murderers;
An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi
53 ye who received the Law as ordained through angels, and did not keep it.
ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”
54 But when they heard these things, their hearts were filled with rage, and they gnashed their teeth at him.
Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu.
55 But, being full of the Holy Spirit, he looked up earnestly into heaven, and saw the glory of God, and Jesus standing on the right hand of God,
Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.
56 and said, Lo, I behold the heavens opened, and the Son of man standing on the right hand of God.
Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”
57 And they cried out with a loud voice, and stopped their ears, and rushed upon him with one accord;
Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya.
58 and having cast him out of the city, they stoned him. And the witnesses laid down their garments at the feet of a young man named Saul;
Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.
59 and they stoned Stephen, making supplication, and saying, Lord Jesus, receive my spirit.
Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”
60 And kneeling down he cried with a loud voice, Lord, lay not this sin to their charge. And saying this, he fell asleep.
Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.

< Acts 7 >