< Genesis 16 >

1 Now Sarai, Abram's wife, bore him no children, but she had an Egyptian servant whose name was Hagar.
To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar,
2 Sarai said to Abram, "Look now, God has prevented me from bearing. Please go in to my servant. It may be that I will obtain children by her." Abram listened to the voice of Sarai.
saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.” Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa.
3 So Sarai, Abram's wife, took Hagar the Egyptian, her servant, after Abram had lived ten years in the land of Canaan, and gave her to Abram her husband to be his wife.
Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa.
4 He slept with Hagar, and she conceived. When she saw that she had conceived, her mistress was despised in her eyes.
Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki. Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta.
5 Sarai said to Abram, "This wrong is your fault. I gave my servant into your bosom, and when she saw that she had conceived, she despised me. God judge between me and you."
Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.”
6 But Abram said to Sarai, "Look, your servant is in your hand. Do to her whatever is good in your sight." Sarai dealt harshly with her, so she fled from her presence.
Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.
7 And the angel of God found her by a spring of water in the desert, by the spring on the way to Shur.
Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur.
8 And he said, "Hagar, servant of Sarai, where did you come from, and where are you going?" And she said, "I am running away from the presence of my mistress Sarai."
Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”
9 The angel of YHWH said to her, "Return to your mistress, and submit yourself to her authority."
Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.”
10 The angel of YHWH said to her, "I will greatly multiply your descendants, so that they will be too numerous to count."
Mala’ikan ya ƙara da cewa, “Zan ƙara zuriyarki har su yi yawan da ba wanda zai iya lasafta su.”
11 Then the angel of God said to her, "Look, you are with child, and will bear a son. You are to name him Ishmael, because God has heard your affliction.
Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata, “Ga shi kina da ciki za ki kuwa haifi ɗa. Za ki ba shi suna Ishmayel, gama Ubangiji ya ga wahalarki.
12 He will be like a wild donkey among men. His hand will be against every man, and every man's hand against him. And he will live away from all of his brothers."
Zai zama mutum mai halin jakin jeji. Hannunsa zai yi gāba da kowa, hannun kowa kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zama gāba ga dukan’yan’uwansa.”
13 And she called his name, the one who spoke to her, "You are El Roi," for she said, "Here I have seen the one who sees me."
Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.”
14 Therefore the well was called Beer Lahai Roi. Look, it is between Kadesh and Bered.
Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered.
15 Hagar bore a son for Abram. Abram called the name of his son, whom Hagar bore, Ishmael.
Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa.
16 Abram was eighty-six years old when Hagar bore Ishmael to Abram.
Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.

< Genesis 16 >