< 1 Corinthians 7 >

1 Now concerning the things about which you wrote: it is good for a man not to touch a woman.
To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum yă zauna ba aure.
2 But, because of sexual immoralities, let each man have his own wife, and let each woman have her own husband.
Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.
3 Let the husband fulfill his marital duty to his wife, and likewise also the wife to her husband.
Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta.
4 The wife does not have authority over her own body, but the husband. Likewise also the husband does not have authority over his own body, but the wife.
Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma.
5 Do not deprive one another, unless it is by consent for a season, that you may give yourselves to prayer, and may be together again, that Satan does not tempt you because of your lack of self-control.
Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.
6 But this I say by way of concession, not of commandment.
Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba.
7 Yet I wish that all people were like me. However each one has his own gift from God, one of this kind, and another of that kind.
Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.
8 But I say to the unmarried and to widows, it is good for them if they remain even as I am.
To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake.
9 But if they do not have self-control, let them marry. For it's better to marry than to burn.
Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.
10 But to the married I command—not I, but the Lord—that the wife not leave her husband
Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta.
11 (but if she departs, let her remain unmarried, or else be reconciled to her husband), and that the husband not leave his wife.
In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa.
12 But to the rest I—not the Lord—say, if any brother has an unbelieving wife, and she is content to live with him, let him not leave her.
Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta.
13 The woman who has an unbelieving husband, and he is content to live with her, let her not leave her husband.
In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yă zauna tare da ita, kada tă kashe auren.
14 For the unbelieving husband is sanctified in the wife, and the unbelieving wife is sanctified by the brother. Otherwise your children would be unclean, but now they are holy.
Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba’ya’yanku ba za su zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.
15 Yet if the unbeliever departs, let there be separation. The brother or the sister is not under bondage in such cases, but God has called you to peace.
Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.
16 For how do you know, wife, whether you will save your husband? Or how do you know, husband, whether you will save your wife?
Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?
17 Only, as the Lord has assigned to each one, as God has called each, so let him walk. So I command in all the churches.
Duk da haka, sai kowa yă kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan.
18 Was anyone called having been circumcised? Let him not become uncircumcised. Has anyone been called in uncircumcision? Let him not be circumcised.
In an riga an yi wa mutum kaciya sa’ad da aka kira shi, to, kada yă zama marar kaciya. In an kira mutum sa’ad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya.
19 Circumcision is nothing, and uncircumcision is nothing, but the keeping of the commandments of God.
Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu.
20 Let each person stay in that calling in which he was called.
Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi.
21 Were you called being a slave? Do not let that bother you, but if you get an opportunity to become free, use it.
Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama.
22 For he who was called in the Lord being a slave is the Lord's free person. Likewise he who was called being free is Christ's slave.
Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi,’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi.
23 You were bought with a price. Do not become slaves of people.
Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane.
24 Brothers, let each one, in whatever condition he was called, stay in that condition with God.
’Yan’uwa, a duk matsayin da mutum yake sa’ad da aka kira shi, sai yă kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.
25 Now concerning virgins, I have no commandment from the Lord, but I give my judgment as one who has obtained mercy from the Lord to be trustworthy.
To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji.
26 I think that it is good therefore, because of the distress that is on us, that it is good for a person to remain as he is.
Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke.
27 Are you bound to a wife? Do not seek to be freed. Are you free from a wife? Do not seek a wife.
In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure.
28 But if you marry, you have not sinned. If a virgin marries, she has not sinned. Yet such will have oppression in the flesh, and I want to spare you.
Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba tă yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.
29 But I say this, brothers: the time is short, that from now on, those who have wives should be as though they had none;
’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su;
30 and those who weep, as though they did not weep; and those who rejoice, as though they did not rejoice; and those who buy, as though they did not possess;
waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne;
31 and those who use the world, as not using it to the fullest. For the form of this world is passing away.
masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.
32 But I desire to have you to be free from cares. He who is unmarried is concerned for the things of the Lord, how he may please the Lord;
Zan so ku’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji.
33 but he who is married is concerned about the things of the world, how he may please his wife,
Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa
34 and is divided. And the woman that is unmarried, or a virgin, is concerned about the things of the Lord, so that she may be holy both in body and in spirit. But the one that is married is concerned about the things of the world, how she may please her husband.
hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta.
35 This I say for your own profit; not that I may ensnare you, but for that which is appropriate, and that you may attend to the Lord without distraction.
Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.
36 But if anyone thinks that he is behaving inappropriately toward his virgin, if she is past the flower of her age, and if need so requires, let him do what he desires. He does not sin. Let them marry.
In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure.
37 But he who stands steadfast in his heart, having no necessity, but has power over his own heart, to keep his own virgin, does well.
Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba, wannan mutum ma ya yi abin da ya dace.
38 So then both he who gives his own virgin in marriage does well, and he who does not give her in marriage does better.
Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.
39 A wife is bound to her husband as long as he lives; but if the husband is dead, she is free to be married to whomever she desires, only in the Lord.
Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da’yanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji.
40 But she is happier if she stays as she is, in my judgment, and I think that I also have God's Spirit.
A nawa ra’ayi, za tă fi jin daɗi in ta zauna haka, a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.

< 1 Corinthians 7 >