< James 5 >

1 Come now, you rich, weep and cry aloud for your miseries that are coming on you.
Ku zo yanzu, ku da kuke masu arziki, ku yi ta kuka da kururuwa domin bakin ciki iri-iri da ke zuwa gare ku.
2 Your riches are corrupted and your garments are moth-eaten.
Arzikin ku ya rube, tufafinku kuma duk cin asu ne.
3 Your gold and your silver are corroded, and their corrosion will be for a testimony against you, and will eat your flesh like fire. You have laid up your treasure in the last days.
Zinariya da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsar su kuwa zai zama shaida a kanku. Zai cinye naman ku kamar wuta. Kun yi ajiyar dukiyarku domin ranakun karshe.
4 Look, the wages of the laborers who mowed your fields, which you have kept back by fraud, cry out, and the cries of those who reaped have entered into the ears of the Lord of hosts.
Duba, hakin ma'aikata yana kuka - hakin da kuka hana wa wadanda suka girbe maku gonaki. Kuma kukan masu girbin ya tafi ya kai ga kunnuwan Ubangiji mai Runduna.
5 You have lived delicately on the earth, and taken your pleasure. You have nourished your hearts in a day of slaughter.
Kun yi zama cikin annashuwa a duniya kuma kun tsunduma kanku. Kun sa zukatan ku sun yi kiba domin ranar yanka.
6 You have condemned, you have murdered the righteous one. He does not resist you.
Kun hukunta kuma kun kashe adalin mutum. Bai kuwa yi tsayayya da ku ba.
7 Be patient therefore, brothers, until the coming of the Lord. Look, the farmer waits for the precious fruit of the earth, being patient over it, until it receives the early and late rain.
Saboda haka ku yi hakuri, 'yan'uwa, har sai zuwan Ubangiji. Duba, yadda manomi ya kan jira kaka mai amfani daga gona. Da hakuri yake jiran ta har sai ta karbi ruwa na fari da na karshe.
8 You also be patient. Establish your hearts, for the coming of the Lord is near.
Ku, ma, ku yi hakuri. Ku karfafa zukatan ku, domin zuwan Ubangiji ya yi kusa.
9 Do not grumble, brothers, against one another, so that you won't be judged. Look, the judge stands at the door.
Kada ku yi gunaguni, 'Yan'uwana, game da juna, don kada a hukunta ku. Duba, mai shari'a na tsaye a bakin kofa.
10 Take, brothers, for an example of suffering and of patience, the prophets who spoke in the name of the Lord.
Dauki misali, 'yan'uwa, daga shan wuya da hakurin annabawa, wadanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji.
11 Look, we call them blessed who endured. You have heard of the patience of Job, and have seen the Lord in the outcome, and how the Lord is full of compassion and mercy.
Duba, mukan kira wadanda suka jimre masu albarka. Kun dai ji irin jimiri da Ayuba ya yi, kun kuma san nufin Ubangiji, yadda yake mai yawan tausayi da jinkai.
12 But above all things, my brothers, do not swear, neither by heaven, nor by the earth, nor by any other oath; but let your "yes" be "yes," and your "no," "no;" so that you do not fall under judgment.
Fiye da komai duka, 'yan'uwana, kada ku yi rantsuwa, ko da sama, ko da kasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. A maimakon haka bari “I” ya zama “I”, in kuwa kun ce “A'a”, ya zama “A'a”, don kada ku fada a cikin hukunci.
13 Is anyone among you suffering? He should pray. Is anyone cheerful? He should sing praises.
Akwai wanda ke fama a tsakanin ku? Sai ya yi addu'a, akwai wanda yake murna? Sai ya raira wakar yabo.
14 Is anyone among you sick? He should call for the elders of the church, and they should pray over him, anointing him with oil in the name of the Lord.
Akwai mara lafiya a tsakanin ku? Sai ya kira dattawan ikilisiya, sai su yi masa addu'a. Suna shafa masa mai a cikin sunan Ubangiji.
15 And the prayer of faith will save the one who is sick, and the Lord will raise him up. If he has committed sins, he will be forgiven.
Addu'ar bangaskiya zai warkar da mara lafiyan, Ubangiji zai tashe shi. Idan ma ya yi zunubi, Allah zai gafarta masa.
16 Therefore confess your sins to one another, and pray for one another, that you may be healed. The prayer of a righteous person is powerfully effective.
Soboda haka, ku furta zunuban ku ga juna, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da karfin aiki kwarai da gaske.
17 Elijah was a human being with a nature like ours, and he prayed earnestly that it might not rain, and it did not rain on the land for three years and six months.
Iliya dan Adam ne kamar mu. Amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, ba kuma yi ruwa a kasar ba har shekara uku da wata shida.
18 He prayed again, and the sky gave rain, and the earth brought forth its fruit.
Sai Iliya ya sake yin addu'a. Sammai suka ba da ruwa, kasa kuma ta ba da amfanin ta.
19 My brothers, if any among you wanders from the truth, and someone turns him back,
Ya ku 'yan'uwana, idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi,
20 let him know that he who turns a sinner from the error of his way will save his soul from death, and will cover a multitude of sins.
wannan mutum ya sani cewa, duk wanda ya dawo da mai zunubi a hanya daga baudewar sa, zai cece shi daga mutuwa, kuma zai rufe dunbin zunubai.

< James 5 >