< Acts 27 >
1 When it was determined that we should sail for Italy, they delivered Paul and certain other prisoners to a centurion named Julius, of the Augustan band.
Bayan da aka amince zamu tafi Italiya, sun mika Bulus tare da wadansu daurarru a hanun wani jarumi mai suna Yuliyas, daga batalian Agustas.
2 Embarking in a ship from Adramyttium, which was about to sail to places on the coast of Asia, we put to sea; Aristarchus, a Macedonian of Thessalonica, being with us.
Muka shiga Jirgin ruwa daga Adramatiya, wanda ke shirin tashi zuwa kusa da gefen tekun Asiya. Sai muka je teku. Aristakus mutumin Tasalonika a Makidoniya ya tafi tare damu.
3 The next day, we landed at Sidon. Julius treated Paul kindly, and gave him permission to go to his friends and refresh himself.
Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su.
4 Putting to sea from there, we sailed under the lee of Cyprus, because the winds were contrary.
Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu.
5 When we had sailed across the sea which is off Cilicia and Pamphylia, we came to Myra, a city of Lycia.
Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya.
6 There the centurion found a ship of Alexandria sailing for Italy, and he put us on board.
Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa.
7 When we had sailed slowly many days, and had come with difficulty opposite Cnidus, the wind not allowing us further, we sailed under the lee of Crete, opposite Salmone.
Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina.
8 With difficulty sailing along it we came to a certain place called Fair Havens, near the city of Lasea.
Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya.
9 When much time had passed and the voyage was now dangerous, because the Fast had now already gone by, Paul admonished them,
Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su,
10 and said to them, "Sirs, I perceive that the voyage will be with injury and much loss, not only of the cargo and the ship, but also of our lives."
ya ce, “Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu.”
11 But the centurion gave more heed to the master and to the owner of the ship than to those things which were spoken by Paul.
Amma jarumin ya fi mai da hankali ga maganar shugabansa da mai jirgin ruwan, fiye da abubuwan da Bulus ya fadi.
12 Because the haven was not suitable to winter in, the majority advised going to sea from there, if by any means they could reach Phoenix, and winter there, which is a port of Crete, looking northeast and southeast.
Da shike tashar ba za ta yi dadin zama da hunturu ba, mafi yawa sun ba da shawara a bar wurin, in maiyiwuwa ne muga mun kai birnin Finikiya, don mu yi hunturu a can. Finikiya tashar jirgin ruwa ce a Karita, tana fuskantar arewa maso gabas da kudu maso gabas.
13 When the south wind blew softly, supposing that they had obtained their purpose, they weighed anchor and sailed along Crete, close to shore.
Sa'adda iska daga kudu ta huro a hankali, sun tsammaci bukatarsu ta biya. Sai suka janye linzamin jirgin ruwan sukabi ta Karita kusa da gaba.
14 But before long, a stormy wind beat down from shore, which is called Euraquilo.
Amma bayan wani dan lokaci sai iska mai karfi da ake kira Yurokilidon, ta fara bugun mu daga tsibirin.
15 When the ship was caught, and could not face the wind, we gave way to it, and were driven along.
Sa'adda Jirgin ruwan ya kasa fuskantar iskar, sai muka bi inda iskar ta nufa.
16 Running under the lee of a small island called Cauda, we were able, with difficulty, to secure the boat.
Sai muka bi ta inda muka sami kariya kusa da wani dan tsibiri wanda ake kira Kauda; kuma da wahala muka daure karamin jirgin a jikin babban.
17 After they had hoisted it up, they used cables to help reinforce the ship. Fearing that they would run aground on the Syrtis, they lowered the sea anchor, and so were driven along.
Bayanda suka daga shi, sun yi amfani da igiyoyi don su daure jirgin don gudun fadawa kan yashin Sirtis, suka bar jirgin yana ta korarsu.
18 As we labored exceedingly with the storm, the next day they began to throw things overboard.
Mun yi ta fama da hadari ba kadan ba, da gari ya waye ma'aikatan jirgin suka fara zubar da kaya daga jirgin.
19 On the third day, they threw out the ship's tackle with their own hands.
A rana ta uku, ma'aikatan jirgi suka jefar da kaya daga cikin jirgin da hannuwansu.
20 When neither sun nor stars shone on us for many days, and no small storm pressed on us, all hope that we would be saved was now taken away.
Kwanaki dayawa ba mu ga hasken rana da taurari a bisan mu ba. Babban hadari kadai ke dukanmu, duk mun fidda zuciya zamu tsira.
21 When they had been long without food, Paul stood up in the middle of them, and said, "Sirs, you should have listened to me, and not have set sail from Crete, and have gotten this injury and loss.
Sa'adda sun dade basu ci abinci ba, sai Bulus ya tashi a gaban ma'aikatan jirgi yace, “Jama'a, da kun saurare ni, da bamu tashi daga Karita ba, balle mu fuskanci wannan barna da asarar.
22 Now I exhort you to cheer up, for there will be no loss of life among you, but only of the ship.
Yanzu fa ina karfafa ku kuyi karfin hali, domin ba wanda zai rasa ransa a cikinku, sai dai jirgin kadai za a rasa.
23 For there stood by me this night an angel, belonging to the God whose I am and whom I serve,
Domin daren da ya gabata mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, wanda kuma nake bautawa -mala'ikansa ya tsaya kusa dani
24 saying, 'Do not be afraid, Paul. You must stand before Caesar. And look, God has granted you all those who sail with you.'
ya ce, “Kada ka ji tsoro, Bulus, dole ka tsaya gaban Kaisar, duba kuma, Allah cikin jinkansa ya baka dukan wadannan da ke tafiya tare da kai.
25 Therefore, sirs, cheer up. For I believe God, that it will be just as it has been spoken to me.
Domin haka, jama'a, kuyi karfin hali, domin na gaskanta da Allah, kamar yadda aka fada mani haka zai faru.
26 But we must run aground on a certain island."
Amma lallai dole ne a jefa mu kan wani tsibiri”.
27 But when the fourteenth night had come, as we were driven back and forth in the Adriatic Sea, about midnight the sailors surmised that they were drawing near to some land.
Sa'adda dare na goma sha hudu ya yi, ana ta tura mu nan da can a cikin tekun Adriyat, wajen tsakar dare, ma'aikatan jirgin sun tsammaci sun kusanci wata kasa.
28 They took soundings, and found twenty fathoms. After a little while, they took soundings again, and found fifteen fathoms.
Da suka gwada sai suka iske kamu ashirin; bayan dan lokaci kadan, sun sake aunawa sai suka iske kamu sha biyar ne.
29 Fearing that we would run aground on rocky ground, they let go four anchors from the stern, and wished for daylight.
Tsoro ya kama su ko watakila a jefar da mu kan duwatsu, sai suka jefa linzami hudu daga karshen jirgin suka yi addu'a don gari ya waye da sauri.
30 As the sailors were trying to flee out of the ship, and had lowered the boat into the sea, pretending that they would lay out anchors from the bow,
Ma'aikatan jirgin ruwan suna neman hanyar da za su rabu da jirgin kuma sun jefa karamin jirgin a cikin teku. Suka yi kamar zasu jefa wasu linzamai daga gaban jirgin.
31 Paul said to the centurion and to the soldiers, "Unless these stay in the ship, you cannot be saved."
Amma Bulus ya ce ma jarumi da sojojin, “Idan mutanen nan ba zasu tsaya cikin jirgin ba, ba zaku tsira ba”.
32 Then the soldiers cut away the ropes of the boat, and let it fall off.
Sai sojojin suka yanke igiyoyin jirgin suka kuma barshi ya fadi.
33 While the day was coming on, Paul urged them all to take some food, saying, "This day is the fourteenth day that you wait and continue fasting, having taken nothing.
Da gari ya fara wayewa, Bulus ya roke su duka su dan ci abinci, ya ce, “Yau kwana goma sha hudu kenan ba ku ci kome ba.
34 Therefore I urge you to take some food, for this is for your preservation; for not a hair will perish from any of your heads."
Saboda haka na roke ku ku ci abinci, domin wannan saboda lafiyarku ne; kuma ko gashin kanku daya baza ku rasa ba”.
35 When he had said this, and had taken bread, he gave thanks to God in the presence of all, and he broke it, and began to eat.
Da ya fadi haka sai ya dauki gurasa ya yi godiya ga Allah a idanun kowa. Sai ya gutsutsura gurasa ya fara ci.
36 Then they all cheered up, and they also took food.
Sai dukansu suka karfafu suka kuma ci abinci.
37 In all, we were two hundred seventy-six souls on the ship.
Mu mutane 276 (dari biyu da saba'in da shida) ne cikin jirgin.
38 When they had eaten enough, they lightened the ship, throwing out the wheat into the sea.
Da suka ci suka koshi, suka zubar da alkamar cikin teku domin su rage nauyin jirgin.
39 When it was day, they did not recognize the land, but they noticed a certain bay with a beach, and they decided to try to drive the ship onto it.
Da gari ya waye, basu fahimci kasar ba, amma suka hangi wani lungu a gacci, sai suka yi shawara tsakaninsu ko su tuka jirgin zuwa cikin lungun.
40 Casting off the anchors, they left them in the sea, at the same time untying the rudder ropes. Hoisting up the foresail to the wind, they made for the beach.
Sai suka yanke linzaman suka bar su cikin tekun. Cikin lokaci guda suka kwance igiyoyin da ke juya jirgin, suka saki filafilan goshin jirgi suka nufi gabar tekun.
41 But coming to a place where two seas met, they ran the vessel aground. The bow struck and remained immovable, but the stern began to break up by the violence of the waves.
Da suka iso inda ruwa biyu suka hadu, sai jirgin ya tsaya kasa. Gaban jirgin ya kafe a nan, ba damar matsawa, sai kuma kurar jirgin ta fara kakkaryewa saboda haukan rakuman ruwa.
42 The soldiers' counsel was to kill the prisoners, so that none of them would swim out and escape.
Shirin sojojin ne su kashe 'yan kurkukun domin kada su yi iyo su tsere.
43 But the centurion, desiring to save Paul, stopped them from their purpose, and commanded that those who could swim should throw themselves overboard first to go toward the land;
Amma shi hafsan ya so ya ceci Bulus, sai ya tsai da shirin su, ya ba da umarni, duk masu iya iyo su yi tsalle su fada ruwa su kai gacci.
44 and the rest should follow, some on planks, and some on other things from the ship. So it happened that they all escaped safely to the land.
Sa'annan sauran mazajen su biyo baya, wadansu a kan karyayyun katakai, wadansu akan abubuwan da ke a jirgin. Ta haka ne dukanmu muka kai gacci lafiya.