< 1 Corinthians 11 >

1 Be imitators of me, even as I also am of Christ.
Ku yi koyi da ni, kamar yadda nake koyi da Almasihu.
2 Now I praise you, that you remember me in all things, and hold firm the traditions, even as I delivered them to you.
Yanzu ina yaba maku ne, don kuna tunawa da ni cikin abu duka. Ina kuma yaba maku wajen bin al'adun da na ba ku daidai yadda na ba ku.
3 But I would have you know that the head of every man is Christ, and the head of the woman is the man, and the head of Christ is God.
Amma fa ina son ku fahimta da cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace mutumin ne, shugaban Almasihu Allah ne.
4 Every man praying or prophesying, having his head covered, dishonors his head.
Kuma duk mutumin da ya yi addu'a ko annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa.
5 But every woman praying or prophesying with her head unveiled dishonors her head. For it is one and the same thing as if she were shaved.
Amma duk macen da ta yi addu'a ko annabci kanta a bude, ta wulakanta shugabanta. Gama yayi dai dai da idan tayi aski.
6 For if a woman is not covered, let her also be shorn. But if it is shameful for a woman to be shorn or shaved, let her be covered.
Gama idan mace ba zata rufe kanta ba, to ta yanke gashinta ya zama gajere. Idan abin kunya ne mace ta yanke gashinta ko ta aske kanta, bari ta rufe kanta.
7 For a man indeed ought not to have his head covered, because he is the image and glory of God, but the woman is the glory of the man.
Bai kamata na miji ya rufe kansa ba, tun da yake shi siffa ne da daukakar Allah. Amma mace daukakar namiji ce.
8 For man is not from woman, but woman from man;
Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba. A maimako, matar daga jikin namiji take.
9 for neither was man created for the woman, but woman for the man.
Ba a kuma halicci namiji don mace ba. A maimako, an halicci mace don namiji.
10 For this cause the woman ought to have authority on her head, because of the angels.
Shi ya sa mace za ta kasance da alamar iko a kanta, saboda mala'iku.
11 Nevertheless, neither is the woman independent of the man, nor the man independent of the woman, in the Lord.
Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.
12 For as woman came from man, so a man also comes through a woman; but all things are from God.
Kamar yadda mace take daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.
13 Judge for yourselves. Is it appropriate that a woman pray to God unveiled?
Ku hukunta da kanku: Daidai ne mace ta yi addu'a ga Allah kanta a bude?
14 Doesn't even nature itself teach you that if a man has long hair, it is a dishonor to him?
Ashe, ko dabi'a bata nuna maku cewa abin kunya ne namiji, ya kasance da dogon gashi ba?
15 But if a woman has long hair, it is a glory to her, for her hair is given to her for a covering.
Ba dabi'a ta koya maku cewa idan mace tana da dogon gashi, daukakar ta ne ba? Gama domin rufewa aka yi mata baiwar gashin.
16 But if anyone seems to be contentious, we have no such custom, neither do God's churches.
To idan wani yana da niyyaryin gardama game da wannan, mu dai bamu da wata al'adar, ikilisiyoyin Allah kuma haka.
17 But in giving you this command, I do not praise you, that you come together not for the better but for the worse.
Amma game da umarnin dake biye, ban yaba maku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin gaskiya ce.
18 For first of all, when you come together in the church, I hear that divisions exist among you, and I partly believe it.
Farko dai sa'adda kuke, taron ikklisiya, na ji har akwai rarrabuwa tsakaninku, har na fara amincewa da maganar.
19 For there also must be factions among you, that those who are approved may be revealed among you.
Dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane wadanda suke amintattu a cikinku.
20 When therefore you assemble yourselves together, it is not the Lord's supper that you eat.
Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
21 For in your eating each one takes his own supper first. One is hungry, and another is drunk.
Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci, har ya bugu.
22 What, do you not have houses to eat and to drink in? Or do you despise God's church, and put them to shame who do not have? What should I tell you? Should I praise you? In this I do not praise you.
Baku da gidajen da zaku ci ku sha, kuna raina ikkilisiyar Allah, kuna kuma wulakanta wa wadanda basu da komai? To, me zan ce maku? Yaba maku zan yi? Ba zan yaba maku ba akan wannan.
23 For I received from the Lord that which also I delivered to you, that the Lord Jesus on the night in which he was betrayed took bread.
Amma abin da na karba a gun Ubangiji shi nake baku cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya dauki gurasa.
24 When he had given thanks, he broke it, and said, "This is my body, which is for you. Do this in memory of me."
Bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi domin tunawa da ni.”
25 In the same way he also took the cup, after the meal, saying, "This cup is the new covenant in my blood. Do this, as often as you drink, in memory of me."
Ta wannan hanya kuma, sai ya dauki kokon, ya ce, “kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni.”
26 For as often as you eat this bread and drink this cup, you proclaim the Lord's death until he comes.
Duk sa'adda kuke cin gurasar nan, kuna kuma sha cikin kokon nan, kuna bayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.
27 Therefore whoever eats this bread or drinks the Lord's cup in a manner unworthy will be guilty of the body and the blood of the Lord.
Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a cikin kokon nan, na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa.
28 But let a person examine himself, and so let him eat of the bread, and drink of the cup.
Sai kowa ya fara auna kansa, kafin ya ci gurasar, ya kuma sha a cikin kokon nan.
29 For he who eats and drinks eats and drinks judgment to himself, if he does not discern the body.
In kowa ya ci, ya sha ba tare da rarrabewa da jikin Ubangiji ba, lalle ya jawowa kansa hukunci, ta wurin ci da sha da ya yi.
30 For this cause many among you are weak and sickly, and not a few sleep.
Shi ya sa da yawa a cikin ku suke raunana, kuma suna fama da rashin lafiya, har ma wasun ku da dama suka yi barci.
31 For if we discerned ourselves, we would not be judged.
Amma, in mun auna kanmu, ba a za a hukunta mu ba.
32 But when we are judged, we are punished by the Lord, that we may not be condemned with the world.
In kuwa Ubangiji ne ya ke hukunta mu, To, muna horuwa ke nan, don kada a kayar damu tare da duniya.
33 Therefore, my brothers, when you come together to eat, wait one for another.
Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna.
34 But if anyone is hungry, let him eat at home, lest your coming together be for judgment. The rest I will set in order whenever I come.
Idan kuwa wani yana jin yunwa, ya ci a gida, kada ya zama taronku ya jawo maku hukunci. Batun sauran abubuwan da kuka rubuta kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.

< 1 Corinthians 11 >