< Isaiah 54 >
1 "Sing, barren, you who did not bear; break forth into singing, and cry aloud, you who did not travail with child: for more are the children of the desolate than of her that has a husband," says the LORD.
“Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji.
2 "Enlarge the place of your tent, and let them stretch forth the curtains of your habitations; do not spare: lengthen your cords, and strengthen your stakes.
“Ki fadada wurin tentinki, ki miƙe labulen tentinki da fāɗi, kada ki janye; ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta.
3 For you shall spread out on the right hand and on the left; and your descendants shall possess the nations, and make the desolate cities to be inhabited.
Gama za ki fadada zuwa dama da hagu; zuriyarki za su kori al’ummai su kuma zauna a kufan biranensu.
4 "Do not be afraid, for you will not be put to shame, nor will you be humiliated, for you will not be disgraced. For you will forget the shame of your youth, and the disgrace of your widowhood you will remember no more.
“Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba. Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba.
5 For your husband is your Creator; the LORD of hosts is his name: and the Holy One of Israel is your Redeemer; the God of the whole earth shall he be called.
Gama Mahaliccinki shi ne mijinki, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki; ana ce da shi Allahn dukan duniya.
6 For the LORD has called you as a wife forsaken and grieved in spirit, even a wife of youth, when she is cast off," says your God.
Ubangiji zai kira sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta, macen da ta yi aure a ƙuruciya, sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.
7 "For a small moment have I forsaken you; but with great mercies will I gather you.
“Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.
8 In overflowing wrath I hid my face from you for a moment; but with everlasting loving kindness will I have mercy on you," says the LORD your Redeemer.
Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki.
9 "For this is like the waters of Noah to me; for as I have sworn that the waters of Noah shall no more go over the earth, so have I sworn that I will not be angry with you, nor rebuke you.
“A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu, sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba. Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba, ba zan ƙara tsawata miki kuma ba.
10 For the mountains may depart, and the hills be removed; but my loving kindness shall not depart from you, neither shall my covenant of peace be removed," says the LORD who has mercy on you.
Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.
11 "You afflicted, tossed with storms, and not comforted, look, I will set your stones in beautiful colors, and lay your foundations with sapphires.
“Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba, zan gina ke da duwatsu turkuwoyis, zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya.
12 I will make your pinnacles of rubies, and your gates of sparkling jewels, and all your walls of precious stones.
Zan gina hasumiyarki da jan yakutu, ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske, dukan katangarki kuma da duwatsu masu daraja.
13 And all your children shall be taught by God; and great shall be the peace of your children.
Ubangiji zai koya wa dukan’ya’yanki maza, da girma kuma salamar’ya’yanki zai zama.
14 In righteousness you shall be established: you shall be far from oppression, for you shall not be afraid; and from terror, for it shall not come near you.
Da adalci za a kafa ke. Zalunci zai yi nesa da ke; ba za ki kasance da wani abin da za ki ji tsoro ba. Za a kawar da duk wani abin banrazana; ba zai yi kusa da ke ba.
15 Look, they may gather together, but not by me: whoever shall gather together against you shall fall because of you.
In wani ya far miki, ba daga wurina ba ne; duk wanda ya far miki zai miƙa wuya gare ki.
16 "Look, I have created the smith who blows the fire of coals, and brings forth a weapon for his work; and I have created the waster to destroy.
“Duba, ni ne wanda na halicci maƙeri wanda yake zuga garwashi ya zama harshen wuta ya kuma ƙera makamin da ya dace da aikinsa. Ni ne kuma na halicci mai hallakarwa ya yi ɓarna;
17 No weapon that is formed against you will prosper; and you will condemn every tongue that rises against you in judgment. This is the heritage of the servants of the LORD, and their righteousness which is of me," says the LORD.
ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji.