< Ezekiel 24 >

1 Again, in the ninth year, in the tenth month, in the tenth day of the month, the word of the LORD came to me, saying,
A shekara ta tara, a wata na goma, a rana ta goma, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 "Son of man, write the name of the day, even of this same day: the king of Babylon drew close to Jerusalem this same day.
“Ɗan mutum, ka rubuta wannan rana, wannan rana, domin sarkin Babilon ya yi ƙawanya wa Urushalima a wannan rana.
3 Utter a parable to the rebellious house, and tell them, 'Thus says the LORD, "Set on the caldron, set it on, and also pour water into it:
Ka faɗa wa wannan gidan’yan tawaye wani misali ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Ka sa tukunyar dahuwa; ka sa ta a kan wuta ka kuma zuba ruwa a cikinta.
4 gather its pieces into it, even every good piece, the thigh, and the shoulder; fill it with the choice bones.
Ka sa gunduwoyin nama a cikinta dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa. Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau;
5 Take the choice of the flock, and also a pile of wood for the bones under the caldron; make it boil well; yes, let its bones be boiled in its midst."'
ka kama mafi kyau daga cikin garken. Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan; ka sa ta tafasa ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta.
6 "Therefore thus says the LORD: 'Woe to the bloody city, to the caldron whose rust is in it, and whose rust is not gone out of it. Take out of it piece after piece; No lot is fallen on it.
“‘Gama wannan shi ne abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Kaito birnin nan mai zubar da jini, ga tukunya wadda take da tsatsa, wadda tsatsarta ba za tă fita ba! Ka fitar da shi gunduwa-gunduwa ba tare da jefa ƙuri’a a kansu ba.
7 For her blood is in the midst of her; she set it on the bare rock; she didn't pour it on the ground, to cover it with dust.
“‘Gama zubar da jini yana a tsakiyarta, ta zubar da shi a dutsen da yake a fili; ba tă zubar da shi a ƙasa ba, inda ƙura za tă rufe shi.
8 That it may cause wrath to come up to take vengeance, I have set her blood on the bare rock, that it should not be covered.'
Don a zuga hasala a kuma yi sakayya na sa jininta a dutsen da ba a rufe ba, saboda kada a rufe.
9 "Therefore thus says the LORD: 'Woe to the bloody city. I also will make the pile great.
“‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Kaito birnin nan mai zubar da jini! Ni ma zan jibge itace da yawa.
10 Pile on the wood, make the fire hot, boil the meat well, and mix in the spices, and let the bones be burned up.
Ka tula gumagumai ka kuma ƙuna wuta. Ka dafa naman da kyau, kana haɗawa da yaji; ka kuma bar ƙasusuwan su ƙone.
11 Then set it empty on its coals, that it may be hot, and its bronze may burn, and that its filthiness may be molten in it, that its rust may be consumed.
Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur domin dattinta ya narke tsatsarta kuma ta ƙone.
12 She has wearied herself with toil; yet her great rust doesn't go forth out of her; her rust doesn't go forth by fire.
Ta gajiyar da dukan ƙoƙari; ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba, kai, ko a wuta ma.
13 In your filthiness is lewdness: because I have cleansed you and you weren't cleansed, you shall not be cleansed from your filthiness any more, until I have caused my wrath toward you to rest.
“‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.
14 I, the LORD, have spoken it: it shall happen, and I will do it: I will not go back, neither will I spare, neither will I repent; according to your ways and according to your deeds I will judge you,' says the LORD."
“‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
15 Also the word of the LORD came to me, saying,
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
16 "Son of man, look, I will take away from you the desire of your eyes with a stroke: yet you shall neither mourn nor weep, neither shall your tears run down.
“Ɗan mutum, da farat ɗaya ina gab da ɗauke abin da idanunka suke jin daɗin gani. Duk da haka kada ka yi makoki ko ka yi kuka ko ka zub da hawaye.
17 Sigh, but not aloud, make no mourning for the dead; bind your headdress on you, and put your shoes on your feet, and do not cover your lips, and do not eat men's bread."
Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”
18 So I spoke to the people in the morning; and at even my wife died; and I did in the morning as I was commanded.
Da gari ya waye, sai na yi magana da mutane, da yamma kuwa matata ta rasu. Kashegari na yi yadda aka umarce ni.
19 The people said to me, "Won't you tell us what these things are to us, that you do so?"
Sai mutane suka tambaye ni suka ce, “Ba za ka faɗa mana abin da waɗannan abubuwa suke nufi a gare mu ba?”
20 Then I said to them, "The word of the LORD came to me, saying,
Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa
21 'Speak to the house of Israel, "Thus says the LORD: Look, I will profane my sanctuary, the pride of your power, the desire of your eyes, and that which your soul pities; and your sons and your daughters whom you have left behind shall fall by the sword.
faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku.’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi.
22 You shall do as I have done: you shall not cover your lips, nor eat the bread of men.
Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba.
23 Your turbans shall be on your heads, and your shoes on your feet: you shall not mourn nor weep; but you shall pine away in your iniquities, and moan one toward another.
Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi.
24 Thus Ezekiel shall be a sign to you; according to all that he has done, you will do. When this comes, then you will know that I am the LORD."'"
Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’
25 "You, son of man, shall it not be in the day when I take from them their strength, the joy of their glory, the desire of their eyes, and that whereupon they set their heart, their sons and their daughters,
“Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka’ya’yansu maza da mata,
26 that in that day he who escapes shall come to you, to cause you to hear it with your ears?
a ranan nan wanda ya tsere zai zo don yă ba ka labari.
27 In that day your mouth will be opened to him who has escaped, and you shall speak, and be no more mute: so you will be a sign to them; and they shall know that I am the LORD."
A lokacin bakinka zai buɗe, za ka yi magana da shi ba kuwa za ka ƙara yin shiru ba. Ta haka za ka zama alama gare su, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.”

< Ezekiel 24 >