< 1 Timothy 3 >
1 This is a faithful saying: If someone aspires to the office of bishop, he desires a good work.
Wannan magana tabattaciya ce: Idan wani na da marmari ya zama shugaban Ikilisiya, ya na marmarin aiki mai kyau.
2 The overseer, therefore, must be beyond criticism, the husband of one wife, temperate, self-controlled, respectable, hospitable, good at teaching;
Don haka, wajibi ne shugaban Ikilisiya ya zama mara abin zargi. Ya zama mai mace daya. Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baki. Wajibi ne ya iya koyarwa.
3 not a drunkard, not violent, but gentle, not quarrelsome, not a lover of money;
Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya. A maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama. Ba mai son kudi ba.
4 one who rules his own house well, having children in subjection with all reverence;
Wajibi ne ya iya lura da gidansa da kyau, 'ya'yansa su zama masu yi masa biyayya da dukkan bangirma.
5 (but if someone does not know how to manage his own house, how will he take care of the church of God?)
Gama idan mutum bai iya sarrafa gidansa ba, ta yaya zai iya lura da Ikkilisiyar Allah?
6 not a new convert, lest being puffed up he fall into the same condemnation as the devil.
Bai kamata ya zama sabon tuba ba, domin kada ya kumbura da girman kai, kada ya fadi cikin irin hukunci da aka yi wa Ibilis.
7 Moreover he must have good testimony from those who are outside, to avoid falling into disgrace and the trap of the devil.
Wajibi ne kuma ya kasance mai kyakyawar shaida a cikin wadanda ba masubi ba, domin kada ya fadi cikin kunya da kuma tarkon Ibilis.
8 Deacons, in the same way, must be reverent, not double-tongued, not devoted to a lot of wine, not greedy for money;
Hakanan kuma Dikinoni su kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba. Bai kamata su zama mashayan giya ko masu hadama ba.
9 holding the mystery of the faith in a pure conscience.
Su zama masu rikon bayyananniyar gaskiyar bangaskiya da lamiri mai tsabta.
10 Let them also first be tested; then let them serve as deacons, if they are blamesless.
Daidai ne kuma a fara tabbatar da su, daga nan su fara hidima domin basu da abin zargi.
11 Their wives in the same way must be reverent, not slanderers, temperate, faithful in all things.
Hakanan ma mata su zama masu mutunci. Bai kamata su zama magulmanta ba, amma masu kamewa da aminci cikin komai.
12 Let deacons be husbands of one wife, ruling their children and their own houses well.
Tilas Dikinoni su zama masu mata daya daya. Su iya kulawa da 'ya'yansu da gidajensu.
13 For those who have served well as deacons gain for themselves a good standing, and great boldness in the faith which is in Christ Jesus.
Gama wadanda suka yi hidima da kyau sun sami tsayawa mai kyau da gabagadi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu.
14 These things I write to you, hoping to come to you shortly;
Ina rubuta maka wadannan abubuwa, da sa zuciya zan zo wurin ka ba da jimawa ba.
15 but if I wait long, that you may know how people ought to behave themselves in the house of God, which is the church of the living God, the pillar and ground of the truth.
Amma idan na yi jinkiri, ina rubuta maka ne domin ka san yadda za ka gudanar da al'amuranka a cikin gidan Allah, wato Ikklisiyar Allah rayyayiya, ginshiki da kuma mai tallafar gaskiya.
16 Without controversy, the mystery of godliness is great: He was revealed in the flesh, justified by the Spirit, seen by angels, preached among the nations, believed on in the world, and received up in glory.
Babu musu an bayyana cewa ibadarmu ta gaskiya da girma take: “Ya bayyana kansa cikin jiki, Ruhu ya baratar da shi, mala'iku suka gan shi, aka yi shelarsa a cikin al'ummai, aka gaskanta shi a duniya, sa'an nan aka dauke shi sama cikin daukaka.